← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 225

Sashe 118

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*littafinnan na kudi ne.... 08136349646*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 37***
Tinkarosu yakeyi gadan gadan zucia na kuna, hadi da tafarfasa, se faman hada hanya yakeyi sbda kunar zucia, idanuwansa ma nuna masa sukeyi kmr murmushi hilwah keyima mutumin. A matukar harzuke ya karaso inda suke daf daf da Alhaji ibrhm ya tsaya kwayar idonsa na kn hilwah wadda itama shi din take kallo hnklinta a tashe yayinda kaf jikinta keta faman rawa. "Keeee!! Shiga mota!!'' Itace kalmar data fito daga bakinsa cikin tsawa, firgita hilwah tayi a matukar rude ta bude murfin motar ta shiga gidan baya, jiki na rawa, ji takeyi kmr zuciarta zata fashe. AB'ILAL ya dawo da dubansa kan alhaji ibrahin wanda ya zuba masa ido jin yace hilwah ta shiga mota ya bashi tabbacin ko yayanta ne. "Ina wuni yayanmu..." Alhaji Ibrahim ya rissina ya gaida AB'ILAL cikin girmamawa , AB'ILAL ya zuba masa ido kallon kiyayya yake jifansa dashi a ranshi yanaji kmr ya shakuresa dande kawai ya kai zuciarsa nesa ne, zucia ta kara zuwarma AB'ILAL wuya jin mutumin ya kirasa da yaya, shi ganinsa rainin hnkli ne. "Look ni ba dan iska bane ka gane Kou? Uban meye hadinka da ita dazaka mata mgna! Wannan Ai isknci ne, da rashin sanin daraja!!'' AB'ILAL ya fadi cikin kunar zucia besanma ya fada ba, yayin da kwayar idonsa ke kn alhaji ibrahm. Alhaji ibrahim firgita yayi jin yadda AB'ILAL ke masa mgna cikin tsawa, kmr ze zaburo ya watsa masa mari, kalaman AB'ILAL sunyima Alhajin zafi amma ya daure, sbda son yarinyar yakeyi da gaske. alhaji ibrhm ya kara tsorata ganin kallon da ab'ilal ke jifansa dashi, duk yabi ya tsorace sbda yasan in aka barshi dashi se buzunsa, kirar karfafa garesa irin mazannan yan dambe.. "Bada kai nake mgna ba! Nace menene tsakaninku da ita! Ko an gaya maka nan gidan karuwai ne dazaka tare ta a titi!!'' AB'ILAL ya kara dakawa alhaji ibrahim tsawa murya cikin karad'i da bala'i. alhaji ibrahim jiki na rawa ya fara mgna sbda ganin kmr AB'ILAL na shirin yin ball ne dashi ''Ammm..am sorry ni bada wata manufa na mata mgna ba na ganta ne inaso kuma ni Aure...." Tin kafin ya karasa AB'ILAL ya dakatar dashi yana me jin kmr ya shakuro wuyansa sbda tsabar tsananin jin zafin kalaman nasa wato ma ze Aurenta zeyi...''se aka gaya maka neman miji takeyi! Ko an gaya maka budurwa,ce ita!! Manemin matan mutane!!wannan Ai isknci ne da wulaknci da rashin sanin darajar matar mutane!!'' AB'ILAL ya karashe mgnr murya da kwayar idonsa cike da tsantsar kishi da kiyayyar Alhaji, mgnganun nasa ma besan ta ina suke fito wa ba. Alhaji ibrahim ya kuresa da ido yana me hango kishi a kwayar idonsa, se yanzu ya kula d hkn. "To ko matarsa ce, ko budurwarsa, ya tambayi knsa d knsa. Nan take zuciarsa ta basa sede matarsa. dan hk jikinsa yy sanyi, ya fara mgna da laushin murya. "Am very sorry bnsan cewa matarka bace, wlhy nasha budurwa ce...." AB'ILAL yaja kwafa kawai se faman tiriri yakeyi yana hajijiyar matsifa yaso ace alhajin ya masa wata mgnr bnza wlhy da sede a kwasheshi a sume. Kwafa yaja a karo na biyu ya kalli alhaji ibrhim a wulaknce kana ya juya ya koma motarshi alhaji ya juya shima ya koma motarsa jiki a sanyaye a gaskia ya kamu da sonta a gani na farko, yasan da wuya ya hkra da ita a nan kusa sbda y kamu da tsamanin sonta. AB'ILAL na shiga motar ya figeta da tsiya, aka bude masa get ya fice a guje kmr ze bige masu gadin ya daura motar a kn titi ya hau sharara gudu kai daganin yadda yake tukin zakasan cewa a hasale yake ko kallon inda take beyi ba sbda haushi take basa, be taba sanin iskncinta yakai hk ba se yau, driving yakeyi amma kuma takaici na cinsa inside ..... Kasa da knta tayi har lokacin jikinta na rawa, ganin yadda yake gudu da ita a motar ma seya kara mata tsoro gani takeyi kmr niyar kashesu ma yakeyi, ta kulle murfin idanuwanta tsoro da firgice na cin zuciarta. Har suka isa gidan be juyo ya kalleta ba itama bata kallesa ba sbda duk a tsorace take. Suna isa gidan ko gama packing beyi ba ta bude murfin motar ta fita, ta nufa falon Amihh a guje kai kace biyota akayi, sukayi kicibus da Salwah a tsakiyar falon Amihh, suka zube a kn 3ct salwah data firgita da ganin hilwah a firgice ta shiga tambayarta meya faru hilwah tace mata bakomi kawai, tanata faman haki , salwah ta kara tambayarta meya faru, tace mata ba komi, salwah taki yadda da hkn, ta nace mata da tambaya dole hilwah ta sanar da ita kawai sun kusa yin accident ne a hnyar daaowa, salwah ta mata Allah ya kyauta ita a fari ma tasha ab'ilal ne ya mata wani abu.... Fitowa yayi bayan ya gama packing motar zucia fal takaici har ynzu tiriri zuciarsa keyi, hannunsa riqe da car key dinsa ya nufa side dinsa, a falonsa ya yada zango a kn 3ct yana mejin kmr ze mutu se ynzu yake nadama dayabar mutuminnan dabe kai masa hannu ba ta yadda 44 ma bazasu amsheshi ba, ya zagi mutumin yafi sau dari biyu a zuciarsa. "Meyasa kakejin hkn a kn karuwa?'' Wani bangare na zuciarsa ta masa wannan tambayar, dogon tsuki yaja hadi da rintse kwayar idonsa, ya juya ya kwanta kwanciar gefe akasin da dayake kwance yana me kallon sama. Yasan kirayyar yarinyar ce tasashi jin wannan mugun yanayin a ransa, a lokacin ji yayi kmr ya rufeta da duka dan yafi ganin lefinta a kn mutumin, bacin rai ya hanashi mata mgna, da gudun raini,,juyi yashigayi a kn kujerar kmr zuciarsa zata fito waje ta fashe dan takaici ga yunwa na cin cikinsa amma beji takaicin da yarinyar ta kunsa masa ya hana yaji yunwar dake cikin nasa....ranar hk ya kasamce beci abinci ba seda daddare. Dayazo bacci da bacin ran hilwah ya kwana dadin dadawa kuma ga sha'awar nono, musammanma yau daya kara ganinta se hnklinsa ya kara tashi, bura kuwa bata rankwafa ba har washe gari....

Bayan kwana biyar hilwah ta kara samun jikinta sosai har yar kiba tayi tana nan side din Amihh tana bata kulawa sosai. Yau Amihh tace ta koma side dinta tinda ta samu sauki sosai, sam hilwah bataso hknba hk de ta koma can din zucia ba ddh, sam bata bari sun hadu da Ab'ilal ba, tinda ta kule a daki ko falo bata fitowa, hilwah bata mnta da warning din AB'ILAL. Har ynzu a kasan carpet take kwana shima a tsorace, salwah ke kawo mata abnci har tayi 2 days a side din basu hadu ba, rabonta dashi tin rnr daya kaita asibiti, hk shima rabonshi da ita tin rnr daya kaita asibitin a 2 days dinnan yayi busy sosai kullum seya fita ma'aikatarsa dake nan garin kadunar, gashi sun bude wani sabon company na saida motoci na alfarma dan hk se yy busy sosai. Da safe de kullum kafin ya fita se yaje ya gaida Amihh takan amsa ba yabo ba fallasa, sam batabi ta knsa ba kn bacin ran daya kunsa mata rnr daze kawo hilwah asibitin, tasan ze kuma wani iskncin seta hada taci ubansa a lokacin.. Tinda Hilwah ta dawo side din kullum se tayi aikace aikacen daya zamana nata na gidan, ko rana daya bata taba tsallakewa ba, tin bata saba ba harma ta dan fara sabawa, a bangaren gyara nasa dakin kuwa Se ta faki idonsa in benan kmr lokacin azahar da la'asar hk tasan yana zuwa masallaci, shine take shiga ta gyara masa shape shape ta fito, har wanki take masa, ta gyara masa komi tsaf. sede in gogan ya dawo yaga an gyara masa ko ina sannan ga kamshin jikinta da zuwa ynzu ya riga daya gama kama masa daki, ba krmin jin dadin kamshin nata yakeyiba, hkn ba karamin kara tada masa sha'awah yakeyi ba , daman ya lafiar kura, be bacci har ynzu kullum bura a mike, se da kyar yake bacci shima se zuwa bayan asubahi.

Amihh tayi ciku cikun sa hilwah a mkrntar su salwah, ta zaba mata irin cos din da salwah ke karanta ba tare da tayi shawara da ita ba, sosai hilwah taji dadin cos din da Amihh ta zabar mata na krtun likitanci. Rnr monday hilwah ta fara zuwa makarantarta ita da salwah komi na bukatuwwa Amihh ta mata, tase mata dogayen riguna kusan kaloli arba'in marasa nauyi wadanda zata rinka sakawa zuwa mkrntar, danta kula batason kaya masu nauyi sbda duk kayan da AB'ILAL ya mata bata sa ko daya ba a ciki sbda bata ma iya sasu ba. A sati daya data fara zuwa mkrntar mlmn suka yaba da kokarinta ai tini ta samu shiga a gun malamai da wasu dalibn mkrntar hadda wadanda ta fisu aji sosai, amma sam bata sakewa da maza sbda Amihh ta mata fada kn ta riqe mutumcinta tinda tabada Aure. Duk wainar nan da ake toyawa Sam AB'ILAL besan ma meke faruwa ba, kwanansa goma a garin kaduna, aiki ya taso masa zuwa garin kano ya nemi izinin Amihh tayi masa fatan dawowa lafia yaji dadin hkn , ya nufa garin kanon cikin jin Dadin zucia sbda adduarh mahaifiyyarsa garesa, har ya tafi bega fuskarta ba, yana cike da bukatuwar ganin fuskarta amma sede bacin ranta be bar zuciarsa ba, na rnr daya kaita asibitin.
Chapter 118 · 0% Book details