Sashe 66
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin motar hilwah tayi shiru yayin da knta ke kasa, tana wasa da yatsun hannunta duk jikinta yayi sanyi, yayinda rumfar kunya ta baibayeta, ta rasa ina ne makomarta. Hajiya maryam na driving din amma hnklinta na kn hilwah jefi jefi seta juyo ta kalleta, amma bata ce mata uffan ba...a hk har suka isa asibitin 44, hajiya Maryam tayi packing a packing space din asibitin ba tare data ce ma hilwah komi ba ta fita a motar. Ba tace da hilwah ta fito ba ta bude murfin motar ta fito tana karewa asibitin kallo, ta sama taga an rubuta 44 hospital, hkn ya bata tabbacin asibiti ne sukazo, to me zasuyi a asibitin?'' Hilwah ta tambayi knta kwayar idonta na kn Amihh wadda tini tayi gaba, ba bata lokaci hilwah ta bita a baya, suka saka kai cikin asibitin, duk inda suka gifta se mikowa hajiya maryam gaisuwa akeyi, kama daga kan doctors da nurses, da ma'aikata masu share share da de sauransu. amsawa kawai hajiya maryam keyi cikin dakiya, a haka har suka isa dakin dibar jini, Hajiya maryam ta nunawa hilwah kujera tace ta zauna ba bata lokaci ta zauna tanata rarraba ido. Hajiya Maryam ta dauko abin dibar jini da madauri, ta karaso inda hilwah take. hilwah ta bita da ido, hannunta na dama ta kamo ta fito dashi daga cikin hijjabin dake jukinta, ta daura mata wata igiya, a dai-dai inda ake dibar jini, wato, nan da nan babbar jijiya ta jini ta bayyana, ba tare da Hajiya maryam tasha whla ba.. hilwah ta zaro ido zucia a matukar Tsorace, ganin hajiya maryam na kokarin dibar mata jini, nan fa ido ya raina fata, hajiya maryam ta kawo sirinjin dibar jinin tana kokarin diba Hilwah ta a kaudar da hannunta tana fadin "zafih zanji..." "Sorry..." Itace kalmar data fito daga bakin Amihh. Dole hilwah ta tsaya amihh ta diba jinin amma harda kuka tayi ta share da gefen hijjabinta amihh ta bita da ido , kana ta fice a dakin dibar jinin ta nufa lab, babu kowa sbda akwai labs dayawa a asibitin. Wannan special ne. gun binciken jinin wato blood test's. Da knta ta shiga binciken jinin hilwah data diba ta mafa HIV test da sauran gwaje gwaje na jini, duk wata cuta ta duniya seda Amihh ta gwada a jinin hilwah duk result daya yake badawa shine babu kowanne ciwo a jikinta, har kara maimaita test's din Amihh tayi dan kara tabbatarwa ya kara nuna amsar daya bada a farko seda Amihh ta sauke ajiyar zucia ta duba group din jininta da sauransu nanma taji ddh, ta fito daga dakim gwajin tana murmushi ta dawo inda ta bar hilwah nan ta sameta, ta zubo mata ido tin sako kafarta cikin gurin, hajiya maryam dinma ido ta bita dashi. "Taso mu tafi..." Cewar hajiya maryam. Ba tare da Hilwah tace komi ba ta taso ta biyo Amihh dake tafe ita tana biyarta a baya suka fito daga asibitin suka shiga motar Amihh taja sukabar asibitin. Direct gida Amihh ta nufa dasu zuciar hilwah bata bar tunanin shin me Amihh tayi da jinin data diba a jikinta ba, har suka isa gidan. Amihh tayi packing a gun packing din gidan ta fito zucia zallar farin ciki kawai, hilwah ma ta bude ta fito jikinta a sanyaye. Babu kowa a harabar gidan se me gadi kawai, daman haka ma'aikan suke dasunga Amihh batanan zasu tafi yawonsu, harda dan ustaz ma, inya dawo aka tambayesa yaje ina ne se yace yaje daukar darasi ne a gun babban malami, hajiya Maryam ta gaza gane wanene wannan babban malamin na dan Ustaz. Amihh ta tsaya ta zubawa hilwah ido, kasa tayi da knta ji tayi wata iriyar kunyarta me tsanani ta ziyarceta. "Mu shiga ciki..." Cewar hajiya maryam , ba bata lokaci hilwah tayi gaba, ita kuma hajiya maryam tana biye da ita a baya, kallon surar jikinta kawai takeyi musammanma duwawukanta da suka gaza boyuwa a cikin hijjabin dake jikinta, se aikin jujjuyawa kawai sukeyi kmr zasu faso hijjabin su fito fili, akwau na zama kam!.'' Amihh ta fadi a ranta. Salwah na zaune a falon ta rafka uban tagumi Hannu biyu Biyu tana ta aikin tunanin hilwah gashi gobe takeso ma ta koma gidan Hajiya karama sbda next week zasu fara lecture. Kwatsam taji kamshin Hilwah da'iman ya cika falon, a razane ta dago kwayar idonta tin daga kasa ta fara kallon hilwah har zuwa fuskarta, kmr an tsikareta ta tashi a guje taje ta rungumo hilwah wadda keta murmushi sbda ganin Salwah din, hajiya maryam kam karasowa tayi falon ta zauna kan 3ct ta daura kafa daya kn daya, tana tunani. tabbas tana tsananin son sanin wacece hilwah, sbda wata manufa dake manne a kasan zuciarta, ta barwa ALLAH da knta sani.... "I miss you me rabin sunah..." Cewar salwah daketa murnar ganin hilwah, har zuwa ynzu tana jikinta. "I miss you too me rabin suna..." Cewar hilwah. Dukkaninsu duk sukayima junansu murmushi me fidda sauti, a kasan zuciyoyinsu suna son junansu tamkar yadda jini da jini ke kaunar junansu. Salwah ta kamo hannun hilwah suka isa kan kujerar 2ct suka zauna, hajiya Maryam ta zubo musu ido, yynda hannun salwah ke cikin na hilwah. "Bamu guri..." Hajiya maryam ta fadi hkn , kwayar idonta na kn salwah. "Toh Amihh.." Cewar salwah itama kwayar idonta na kn mahaifiyar tata data umarceta. Sakin hannun hilwah tayi ta mike ta fice a falon. Hajiya maryam ta dawo da kwayar idonta kan hilwah wadda tayi kasa da knta. Ajiyar zucia hajiya maryam ta sauke tana me rintse idanuwanta, dasuke mata zafi sbda rashin bacci a kwanaki biyun da batayi na, sbda aikin tunanin hilwah. Bude idanuwanta tayi a kn hilwah "Me kikeyi a gidan karuwai?" Hajiya maryam ta jefowa hilwah tambayar hilwah tajita tamkar saukar araduh a tsakiyar zuciarta seda ta girgiza ta gigice ta dago kwayar idonta ta zubawa Hajiya maryam suka hada ido se kuma tayi saurin janye nata kwayar idon, tayi kasa da knta, ba tare da tayi mgna ba. Hajiya maryam ta juyo da jikinta sosai ta fuskanci hilwah ta kara jefo mata tambayar data mata a farko "me kikeyi a gidan karuwai..." hilwah ta karayin shiru a wannan karonma, nan da nan ta farajin kwallah na taruwa a idanuwanta. Hajiya maryam ta jinjina kai kawai tana me nazarin hilwah. "Dan ALLAH ki gayamin wacece ke plx? Ina son insan su waye iyayenki plx? Ina mamanki? Ina babanki ?'' Hajiya maryam ta jerowa hilwah wadannan tambayoyin, kwallar da hilwah take adanawa suka hau sintirin zubowa daga kwayar idonta, suna aikin sintiri a kn jajayen kumatunanta..ganin kwallah a kan kumatunan nata ba karamin haifarwa da Hajiya maryam tsananin tashin hnkli yy ba, nan da nan taji tausan hilwah da kaunarta sun kara samun matsugunni a zuciarta, nan take zuciarta ta bata amsar tmbyrta ga hilwah ko iyayen hilwah dinne suka mutu, nan da na. tausanta ya kara rufeta ta sawa ranta kila shine silar fitowarta bariki..., tasowa tayi daga kn kujerar da take zaune ta iso inda hilwah take tanata faman kwallah hadda shashsheka , jawota jikinta tayi ta rungume ta shiga aikin rarrashinta tana buga mata bayanta, hatta da yayan data haifa da cikinta in suna kuka bata rarrashinsu amma ynzu ita ce ke rarrashin hilwah hadda kalamai masu dadih. "Sorry plx Ainie, kiyi hkri, bnsan cewa tambayoyina zasu saki kuka ba, am sorry plx inajin kukanki a can kasan zuciata, kiyi shiru dan Allah, insha ALLAH bazan kara tambayarki komi ba..." Sune kalaman dake fita daga bakin hajiya maryam da muryar rarrashi, se faman bubbugawa hilwah Baya takeyi,,,da kyar ta samu tayi shiru ta dena kukan. Dago fuskarta tayi daga jikinta idanuwanta sunyi ja jawur kmr gauta, fuskarta fara sol ta koma pink light seta kara wani irin mugun kyau. "Zaki zauna dani a nan gidan?'' Hajiya maryam ta jefowa hilwah tambayar, shiru tayi ta kara kasa da knta. "Ki zauna dani knji , na daukeki tamkar yata ta cikina, kisa a ranki zan miki gatan da duk uwa kewa yarta, kin zama yatah daga yau hilwah, shi d'a na kowa ne, , dan Allah ki daukeni a matsayin uwarda ta haifeki."hajiya maryam ta karasa mgnr murya cike da kaunar hilwah. Shiru kawai hilwah tayi hajiya maryam ta kara rungumota jikinta, kusan na 30mnt se aikin rokonta takeyi kan dan ALLAH ta zauna da ita, ita de tana sonta, ba karamin jin ddhn kalaman Hajiya maryam hilwah tayi ba, data ke jikinta ji takeyi tamkar tana jikin uwarda ta haifeta ne, jikin Amihh na fidda wani irin ddh kmr yadda jikin uwa ke fidda wannam dadin a duk lokacin data rungumi yarta ko danta. Ajiyar zucia kawai Hilwah keta saukewa...hajiya marya ta dagota daga jikinta ta mike tsaye ta jawo hannun hilwah suka nufa wata hanya ta bude kofa suka shiga wani irin dankareren falo ne me dan karan kyau, yaji kujeru royal na dubai sun hadu ita haduwa, se kamshi da sanyin AC kawai ke tashi a falon. Direct hajiya maryam ta nufa wani bed room da hannun hilwah a cikin nata har suka isa bedroom din, ta bude handle suka shigo, seda hilwah tace wow! A kasan zuciarta sbda tsabar fitina da jarabar kyau da bedroom din yayi, komi nashi kama daga kan kayan furniture's zuwa kan komi dake dakin labulayya light purple ne and dark purple amma light din yafi yawa , sannan light din yayi kamar white white haka Seka Kalla da kyau zakasan cewa light purple ne. Hilwah se aikin kallon dakin takeyi ya hadu wlhy harya gaji da haduwa komi tsarin dakin yayi mata. Ba tare da Amihh tace mata komi ba, suka fice a dakin, suka nufa wani dakin shi kuma komi nashi light peach ne and dark peach. "Wow!" Hilwah ta fadi a fili sbda taga colors din datafi kauna a duk dunia peach light and dark peach, duniar ALLAH tanason colors dinnan, farin ciki ne ya mamaye zuciarta, ta shiga bin dakin da kallo, Amihh ta juyo ta zuba mata ido, ta fuskanci dakin ya mata kuma ya sata a farin ciki, itama seta tsinci knta a farin cikin, suka hau zagaye tamfatsetsen dakin da fadar girmansa ze ita cinye gaf book dinnan nawa