← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 225

Sashe 63

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

4:30pm tafe take a cikin motarta kirar zamani, da knta take Driving , tasowarta Aiki kenan, tana hnyar komawa gida, driving din takeyi amma zuciarta cike take da tunanin hilwah, haka jiya ta kwana ta tashi sede bacci barawo, zallar tunanin hilwah kawai takeyi. Haka kawai ta tsinci knta da juya akalar motarta zuwa gidan dandi, bata dakatar da kntaba taci gaba dabin hanyoyin dazasu kaita gidan dandin, batajin zata iya jure halin da take ciki wato na tunanin hilwah. Cikin isar ubangiji ta isa da motarta har kofar gidan dandi packing tayi a kofar get din gidan ta zubawa gidan ido tanaji a jinin jikinta tamkar yarta ce ta cikinta take cikin gidan. "Shin zaki iya barinta a cikin gidan?'' Zuciarta ta jefo Mata tambayar nan, rintse idanuwanta tayi tana me jin zafin halin da Hilwah take ciki, harga Allah hajiya maryam ke kaunar hilwah. "Ke ta ceci rayuwarki...meyasa ke bazaki ceto tata rayuwar ba daga fadawa halaqa..." Zuciarta ke tuhumarta. Ajiyar zucia ta sauke, hadi da bude murfin motar ta fito, zuciarta cike da full confidence ta nufa get din gidan dandin ta shiga zuciarta ko alamar fargaba babu, daman already ita din jarumar macece, bawai matsoracia bace. Tsayawa tayi bayan ta shigo cikin gidan, ta hau karewa dakunan gidan kallo, tabbas ko babu tantama gidan na karuwai ne, rintse idanuwanta ta karayi tana me rashin jin dadin kasancewar hilwah a gidan, amma fa ita ko a yaya take tana kaunarta har abadan kaunar da batasan dalilintaba. Mata da maza marasa tarbiya se aikin zirya suke tayi a harabar gidan, hajiya maryam ta bisu da ido, tana mejin zafin yadda aka maida zina ba komi ba a kasar hausa, kuma ga yayan hausawar. Wasu daga cikin karuwan gidan har kwarkwasa sukeyi ganin hajiya maryam su ga tunaninsu ko yar lesbians ce tazo ta dauki daya ta biyata ta kwana da ita. Hajiya maryan ta girgiza kai tana kallonsu zucia fal tausansu, wata iriyar siririyar kwalla ce ta shiga aikin zirya a saman kuncinta,... Tausayin su takeji sosai ga ranta, wasu kaddara ce ta kawosu gidan wasu kuma son zucia ne, wasu kuma basu da rabo ne a dunia da lahira, ka mutu kana zina kuwa ai ka zama tababbe dukda de ba a cire ran rahama ga musulmi amma kai kanka kasan bakayi aikin alheri ba a dunia aiko baza kaga alherinba a kiyama, abinda ka aikata shi zakaje ka taddo, hk koyarwar musulunci ta sanar damu (faman ya'amal miskalaa zarratin khairan yarah. Waman ya'amal misqalaa zarratin sharran yarah). Hannunta ta kai ta share hawayen dasuka hau zirya a kan kuncinta ba tare data ankare ba nan take ta shiga kokarin dakatar da hawayen nata daga zubowa. Rarraba ido ta shigayi tana tunanin ta ina zataga hilwah, gashi gida ba dan kadan ba, dakuna ko sunfi a kirga. Takawa ta shigayi a cikin gidan yayinda karuwan keta zuwa inda take suna kwarkwasa , hajiya maryam se aikin girgiza kai kawai takeyi taci gaba da tafiyarta a cikin gidan, ko Allah zesa taga hilwah. Har ta gama zagaye gidan bataga hilwah ba, ta shiga lungu da saqo Bata gantaba, wata karuwa ce tazo tana ta mata kwarkwasa a gabanta tana jijjiga mata jikinta hajiya maryam ta dago ta kalleta ita fa har ynzu mamaki takeyi na yadda yaya matah suka zama marasa kunya, ansan mace da kunya amma banda matan yanzu. "Ammmm...plx tambaya nakeyi...." Cewar hajiya maryam da tayi mgnr kwayar idonta na kan balki me idon gold. Far-far da kwayar ido balki tayi ta kara jujjuyawa hajiya maryam jikinta, ba lefi tana da diri. Cikin kwarkwasa da zallar iya karuwanci bilki tace "ALLAH yasa nasani..." Hajiya maryam ta jinjina kai zucia fal takaici kana tace "Hilwah nake nema plx, ko kin santa?" Duk wata fara'arh dake kn fuskar balki seda ta gushi dmn ta tsani hilwah iyakar tsana sbda duk customers dinsu maza sun gujesu a kn hilwah ita kuma bata ma kulasu, kawai jaraba ce irin ta dana miji. Cikin kissa da kisisina balki me idon gold tace "haba hajiya ki bar mgnr hilwah komi kkeso zanyi miki, dubafa ki gani nima nan macece iyakar mace..." Ta kashewa Hajiya maryam ido, hadi da jujjuyawa. Murya cike da roko hajiya maryam tace "Plx in knsan inda take ki kaini...." Ta karashe mgnr hadi da marairaicewa. Ran balki ya kara baci, ganin matar ta dage ita hilwah takeso ta gani. Aiko duk yadda hajiya maryam taso balki ta kaita inda hilwah take taki, dole ta hakura ta karasa ta tambaya wasu suma sukaki nuna mata inda hilwarh take, har 6:1am tana gidan, tanata zagaye tana tambayar mutanen gidan hilwah amma aka gaza kaita inda take, su a tunaninsu ko hajiya Maryam yar lesbians, zata dauketa ne taje a rage zafi, daga gani kuma Sunsan akwai arziki ba karya, su kuma bakin ciki garesu sosai, musammanma a kn hilwah sun tsaneta basa sonta sam a gidan. Haka hajiya maryam ta gaji ta fice a gidan ta nufa gidanta jiki babu laka. Washe garima ko aiki batajeba ta kara dawowa gidan, ta kara tambaya a kaita inda hilwah take amma bata dace ba yau dinma aka ki kaitan, haka ta koma gida jiki a sanyaye. Hkn be hanata taki dawowaba washe gari, wato rana ta uku, da safe around 8:am a waje tayi packing motarta ta shigo cikin gidan sanye da hijjabi milk dogo har kasa, ba karamin kyau hijjabin yayi mata ba...dai-dai kankana na shirin fita ya siyo wi-wi ya tashi da safe ze busa yaga babu. Idanuwanshi suka sauka a kn hajiya maryam wada ke tsaye dai-dai ai kofar fita daga get din gidan ta tsaya tanata bin gidan da kallo, shima ta bishi da ido. "Lafiya kuwa hajiya?'' Kankana ya tambayi hajiya maryam da zallar muryarsa ta D, ya karaso daf da ita. Nan take hajiya maryam ta gano kankana dan daudu ne. Ta kara kare masa kallo sanye yake da riga iya guiwa ta bacci, sak rigar irin ta mata, waishi a dole ga mace kenan. "Hilwah nake nema plx....yau kimanin 3days kenan ina zirya duk wanda na tambaya baya kaini inda take, plx in kasan inda take ko ba nan bane kamin kwatance se inje...." Hajiya maryam tayi mgnr jiki a sanyaye. Kankana yayi far far da idanuwa ya hau yarfa hannu yana magana "daman waze nuna miki inda hilwah take ai babu, wannan tsinannan gida me cike da bakin ciki, yadda akejin hilwah kmr a kasheta dmn waze sota da k'aruwa...hmmm! Amma wlhy duk wata yar kutmar uba dai-dai nake da ita wabllahillazi! Ni nan rijiyace ko dan ruwa dole a nemeni! Ah toh!'' Ya karashe mgnr yana buga cinyoyinsa da duka hannayensa biyu. Hajiya maryam tayi shiru tana kallon ikon Allah, wai namiji a dole ya koma mace. "Dan Allah in kasan inda take,, ko biya ne se in biyaka ka kaini..." Kankana yayi murmushin gefen baki yana farfar da ido yace "Allah sarki hajiya ba komi, zan kaiki har inda hilwah take, ai in kika ganni tamkar knga hilwah ne! Uwar daki na ce Ai...amma fa gaskia karki kara hadani da jinsin kaza, ni nan macece sunana ma kankana uwar ruwah..." Ya karashe mgnr yana karayin fari da ido. Hajiya maryam ta saki tayi kasake tana kallon ikon ALLAH, namiji take gani a gabanta Amma kuma yace mata shi macece. "Ka kaini plx ynzu...ngode ss..." Cewar hajiya maryam. Kankana yace "Ba komi hajiya...... Amma de kafin in kaiki ina so ki gayamin meke tafe dake gun uwar dakina?" Hajiya maryam tayi shiru kana race "Ba komi..." Kankana yaci gaba da mgna cikin kwarkwasa "hajiya dade kin fadamin kmr zefi Alheri, ni ma nan dan hannu ne... Amma a Gaskia zan fada miki wani Abu, in har da lesbians ko zina kike neman uwar dakina to ki hkra kawai..." Hajiya Maryam dake sauraron Kankanah hadi da nazarin kalamansa, seda ta zaro ido jin an amfaci manya manyan zunuban dunia zina lesbians. "To me yake nufi?'' Tayi tambayar a zuciarta, tanason karin bayani a game da mgnr kankana, amma kuma ba hkn bane a gabanta a halin ynzu. "Ka kaini gunta plx ni mahaifiyarta ce..." Ba tare data ankare ba ta fadi hkn, wato dubul da baka tayi. Kankanah ya zaro ido jin hajjya maryam tace ita ce mahaifiyar hilwah, se ynzu ma ya hango kamanni hilwah da matar , hilwah fara ce sol haka ma matar fara ce sol, dan hk se yaga sun masa kamanni. Kankana fa ya rasa uwar ubansa gashi besan ta yaya ze kubce ba kuma bayaso ya kaita inda hilwah take sbda yasan karshenta daukarta zatayi tabar gidan da ita na har abadan, tinda tace ita ce mahaifiyarta. Rarraba ido kankana ya shigayi kmr angon kare , hajiya maryam taga Alamar bayaso ne ya kaita inda hilwah din take sbda tace ita mahaifiyarta ce, dukda ba mgna yayi ba amma ta fahimci hkn ne a kan fuskarshi, dan haka ta shiga aikin rokonshi. "Plx ka kaini inda take, ina da bukatar ganinta ne, ka duba girman musulunci, Dan darajar ma'aiki S.A.W..." Kankana yaji jikinsa ya masa sanyi jin an ambaci ma'aikin Allah. "Muje...." Cewar kankana amma ba hkn yaso ba. Ya juya ya fara tafiya hajiya maryam ta biyo bayansa hannunta riqe da car key dinta da wayarta, se kara karewa gidan kallo takeyi,har suka iso kofar dakin hilwah kankama ya juyo ga hajiya maryam yace "Hajiya amma fa ynzu bacci takeyi..." Hajiya maryam tace ba damuwa kaini inda taje kawai...zan jira har ta tashi.." Kankana beda choice ya bude kofar dakin ya shiga hajiya maryam ta biyo bayansa kamshin jikin hilwah da tini ta dade da haddaceshi a kwanakinta biyu a gidanta, ya dakar mata hanci, hadi da sanyin AC. dayake daga haske suka fito se yazamana bataganin kowa dake dakin sbda babu yalwar haske se haske dan kadan na bacci. Haska fitilar wayarta ta kunna , nan take hasken wayar ya gauraye dakin, ta shiga haske haske a dakin, yayinda hasken wayar da idanuwanta suka sauka a kan hilwah dake kwance a kasan carpet din dakin tana sanye da rigar bacci me dankaran kyau light purple jikin rigar se walwali yakeyi, bacci kawai takeyi hnkalinta kwance. Hajiya maryam ta bita da ido yayin da gabanta ke cike
Chapter 63 · 0% Book details