Sashe 62
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A bangaren gogan naku AB'ILAL Har zuwa ynzu baya ganewa kansa, tunanin yarinyar be bar ruhi da gangar jikinsa ba, a kullum adduarh yakeyi kan ALLAH ya yaye masa ita, Amma ina a kullum kara yawa takeyi a ruhinsa da gangar jikinsa, kmr yadda yake tunaninta hake yake tsanarta a rayuwarsa, yayi nadamar ganinta yafi sau dari biyar da Hansin, da kyar ya samu ya fara zuwa gun Aikinsa, ko a gun Aikin ma beda wata natsuwa seya tasa system dinsa a gabansa yana dubawa se kawai fuskarta ta bayyano masa, se yaji duniyar ALLAH ya tsani aikinma gabaki daya, sede ya taso ya dawo gida nan ma be tsira ba, tunanintan nede ke addabarsa, a ko ina kuma a ko da yaushe. shi fa daza a bashi dama wlhy ze iya kasheta sbda tsanar da yayi mata tayi, yawa, inda ace inta mutu ze samu ta fita a rayuwarsa dayafi kowa son ta mutun kowa ya huta Shi kmshi ma ko ya samu natsuwa a rayuwarsa, zuwa kd ya zamar masa kaddara. Dadin dadawa gashi inya kira Amihh har zuwa ynzu bata Amsa masa call, in ze mata kiran dunia bata amsawa, sede kullum yayita kiran salwah yana tambayarta ya lafiar Amihh, tace masa lafia lau, a nan ne yake dsn rage rad'adin dake ransa. Amma yana tsananin yunwar ganinta gashi sam beso ma ya koma kaduna a rayuwarsa duk garuruwan da kasarma baki daya sun fitar masa a rai,. kiyayyar yarinyarnan tabi ta damu rayuwarsa Duniarma zafi take masa...jefi jefi suna waya da Alhaji babba da Alhasan ma, haka hajiya Juwairriyya ma tana yawan kiransa dan taji lafiyarsa, a yan kwanakin nan ne take sa dreva dinta ke kawo masa abincin rana da abincin dare,..yana samu yaci abincin ba lefi gani yakeyi kmr abincin Auwal hubb dinsa ne, a kwanaki biyun ne da hajiya Juwairriyya ke aiko masa da abincin yana ci yana koshi shine ya dan rage wata dmwar amma fa kiyayyar hilwah bata bar zuciarsa ba, baya kaunar ya sake ganinta a rayuwarsa, saboda kiyayyar da yake mata ta wuce girman da Alqalamina ze iya misaltawa, shi knshi gogan baze iya misalta kiyayyar da yakewa mata ba.
Gabaki daya duniyar Allah Hajiya maryam ta rasa sukuni sbda tunanin hilwah, ko gurin Aiki taje da tunanin hilwah a ranta, ko mi takeyi de tunanin hilwah na ranta, a memakon taji ta tsaneta ko ta kyamaceta sbda gidan data gnta sema taji doubles kaunarta na addabar rayuwarta, ba ita kadaiba hatta da Salwah tana cikin wannan halin, tin rnr da Amihh ta dawo ta tambayeta sunje gidansu hilwah ne!'' Amihh ta mata bnza kawai ta shige bedroom dinta, ita ma da tata damuwar. Yau kimanin kwanaki biyu sun shude amma hilwah bata shud'eba a rayuwar hajiya maryam da salwah, abinda salwah kema bakin ciki da bata amshi koda number din Hilwah ba, gashi tace zata zo after 2days yau kimanin 2 days din bata zo ba, salwah se zuba ido takeyi har dare hilwah bata zoba, haka ma washe gari bata cire raiba ta rinka zuba idon ganin ko hilwah zata zo, shiru babu ita babu alamarta, bama me kmrta. 6:pm Amihh ce zaune a tamfatsetsen falonta wanda yaji kayan alatu, ya hadu harya gaji da haduwa, se sanyin AC kawai ke tashi a falon, yana ratsata, sanye take da riga mara nauyi irin ta shan iskar nan, ta amsheta ainun abinka da fatar hutu. yau ta dawo aiki da wuri tin 2:am ta tashi a aiki, ta dawo gida se hutun kawai takeyi, hutun sam be isa hutu ba a gareta sbda dmwar hilwah data dabaibayeta. Salwah ce ta shigo falon sanye da doguwar rigar material dinkin free gown babu alamar inda rigar ta matseta, rigar ta amsheta Ainun tako ina ta koshi ta cika fam, kanta sanye da hula me kyau yynda sumar gaban gashinta ta bayyana. Karasowa tayi tsakiyar falon kwayar idonta na kn Amihh wadda ke kallon TV a zahiri amma a, bad'ini tunanin hilwah takeyi. "Barka da hutawa..." Cewar salwah ta karaso ta zauna kasan kafafuwan amihh. Ajiyar zucia amihh ta sauke kana ta amsa a dakile. "Yauwah...." Salwah tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta zuciarta cike taf da tambayoyi a kan hilwah tanaso ta tambayi Amihh amma kuma babu fuskar yin hkn. Suna nan zaune shiru har aka fara kiraye kirayen sallarh magrib Dukkaninsu suka mike suka nufa dakunayensu dan gabatar da sallarh magribar. Basu fito ba har akayi isha'i, time din da sukecin amincin dare yayi, suka karaso dining masu aiki se hidima suke musu, a kwanaki biyun ko kicking Amihh bata shiga sede masu aiki ke musu komi. White rice ce da miyar zallar kaza aka akayi seving dinsu dashi, se drinks din strawberry. Cin abincin sukeyi amma dukdaninsu da tunanin dake ransu. Duk yadda Salwah taso ta danne abinda ke ranta Ta gaza, ta fara mgna ba tare data sanma ta fara ba, spoon din dake hannunta se jujjutashi takeyi a cikin abincin tin dazu ta gaza ci. "Ko ya hilwah taje gida bamu sani bama.... Kuma tace zata dawo bata dawo ba after 2 days din, ko ta mnta da mu oho! Ni de tana rainah,..sbda ita har na saba da sallah dare, ALLAH yasa ta zo, ta koyamin kira'arhta ta alqur'ani..." Ta karashe mgnr kmr wata karamar yarinya yar 3yrs, kai kace ma kuka zatayi, kawai bata saba da irin wannan dmwar bane, shiyasa ta gaza dannewa. Tin farkon fara maganganun na Salwah Hajiya maryam ta dakatar da cin amincin da takeyi ta ajiye hannayenta duka biyu a kan dining din , ta zubawa Salwah ido kmr tana kallon TV mgnrta daya ce ta tsaya mata a rai, na cewa hilwah ta koya mata sallarh dare, se maimaitawa take a ranta sallarh dare, taya wanda yake gidan karuwai ana zina dashi zeyi sallarh dare, bayan basu da imanin daza suyi sallah cikakkiya ma balle suyi sallar dare, sbda imaninsu ragagge ne, zinar da sukeyi duk in zasuyita se an cire musu imanin dake ransu, da hk da hk har imani da tsoron Allah ya fice a ransu na har abadan,... gabaki daya kan Hajiya maryam ya kulle, yayinda zucia da gangar jikinta duka dauki wani irin zafi me tafe da rad'adin sanyi. "Are you sure yarinyar nan nayin sallarh dare? Kuma ta iya krtun alqur'ani?" Hajiya maryam ta jefowa salwah tambayar, wadda knta ke kasa. Dago knta tayi ta sauke kwayar idonta irin na mahaifitar tata a knta fuskar Amihh. babu alamar wasa tace "Wallahi Allah Amihh kullum a kan dadduma take kwana, bata bacci harse tayi sallarh asubahi duk ina kallonta, sannan ta iya karatun alqurni sosai wlhy Amihh.. Bata baci fa, ko ta kwanta tayi bacci seta tashi zuwa 12:am, a kwana biyun da tayi a gidannan rnr da bata da lafia ne kawai takai 12:am tana bacci, se kuma ta tashi naga ta shiga toilet ta dauro alwala ta dawo kn dadduma ta Hau jero nafilfili, kinga amihh saboda neman lada ma duk a raka biyu in tayi sallahma seta kara zuwa toilet ta kara dauro Alwala... Rana na biyun kuma bama tayi bacci ba kwata kwata har asubahi tana ibada..." Hajiya maryan ta kure salwah ta ido tana jinjina kalaman nata, tabbas kuwa dajin yadda Salwah take gaya mata tasan hilwah ta saba da bautar ubangiji ko a fuska ka kalleta inde kai musulmi ne sekasan cewa ita din cikakkitar musulma ce, fuskarta na fidda haske da Annurin musulunci hadi da ibadar ubangiji, me bautar ALLAH bilhaqqi da gaskia ko a ina yake baya boyuwa,...amihh ta hau nazari hadi da tunani tunani, mikewa tayi ta bar dining din ba tare data ce komi ba ta nufa bedroom dinta tafiso taje can ita kadai tayi tunaninta salwah tabi bayanta da ido, itama mikewa tayi jiki bb laka ta shiga aikin kwashe kayayyakin dasukaci abincin dashi, Ta kai kiching kana tadawo ta nufa bedroom dinta jiki a sanyaye, kullum se tayi adduarh ta kara ganin hilwah a rayuwarta.... Koda amihh ta shiga bedroom dinta karasawa tayi ta kwanta a kn gadonta, tanajin zuciarta na mata wani kala-kala tunani iri daban daban sunata bijiro mata a kn hilwah....haka tayi ta tunani tunanin hadi da nazari nazari har 12:30am, mikewa tayi ta fada bathroom ta dauro alwala ta fito ta saka hijjabi ta nufa gun da aka kebance dan ibada ta tayar da sallarh nafilah, bata kwanta ba seda tayi sallarh asubahi, kana ta samu ta kwanta tana me jin natsuwa a ranta, son hilwah da kaunarta na karuwah a ranta.....
Ita kanta tana cikin tsananin kewar hajiya maryam da salwah, a kullum suna ranta kmr yadda AB'ILAL ke ranta har rana me kamar ta yau, da kaunarsa take kwana take tashi, yana zuciarta har abadan, wasu lokutan har zuwar mata yakeyi a mafarki... Saboda yawaitar tunaninsu hajiya maryam da salwah da kewarsu dake ranta hkn ya haifar mata da rage yawan shaye shayenta, a 100% ta rage 20%. Tunaninsu ke debe mata kewa, shi kadaima wani lokacin yana sata tayi ta slow ita kadai, musammanma in kyakyawar surar AB'ILAL tazo gareta.