Sashe 45
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SAADATU BINTU ABDULLAHIâœðŸ? *Writer of KYAUTAR ALLAH* Sadaukarwa ga Hauwa'u mmn little mrs Asal, Ina tayaki farin cikin Abinda ya samemu na Alheri Allah ya kauda idon makiya yan iskan area.....😂 🅿ï¸?14 Cikin muryar dattako Alhaji murtala ya fara magana. "Dama nayi wani tunani ne, me kyau a gareni dake gaba daya, da duk diyanmu masu albarka .." Yayi jim, hajiya maryam ta zuba masa sexy eyes dinta masu kama dana AB'ILAL sede nashi yafi nata kyau da walwali, sannan nata yasha miya wai danma akwai hutu iya hutu. Alhaji murtala yaci gaba da mgna hadi da kallon agogon dake maqale da hannunsa. "Bari muyi sallah maci gaba da mgna.... " hajia maryam ta jinjina kai dukd ta kagu taji ko menene gashi an fara kiraye kirayen sallarh azahar dole ta hakura. Miqewa hajiya maryam tayi tana fadin "To alhaji ku karasa side dinku, se kuyi alwala...." (Wato side din da yake sauka inyazo) alhaji murtala ya mike hadi da murmushi idonshi na kn hajiya maryam yace "maryamu, maryamu, maryamu manyan mata...ya kamata de kiyi Aure..." Hajiya maryam ta tabe baki ba tare daya ankare ba zuciarta cike da takaici wani lokaci Alhaji murtala haushi yake bata, shi sam be iya controlling bakinshi ba kmr de yadda kaninshi yake mahaifin AB'ILAL shima hk yake, se yyta mata rawar kafa yana mata shiririta, inya cita sau daya kullum seya fadi dadinta dayaji sau dari da hansin, ko ya wuni rnr yana mata zantuttuka a kn saduwar da yayi da ita, a kullum yana ranta shiyasa batajin zata iya auren wani namiji a halin ynzu ta hakura da Aure, ba karamin jin dadin tsohon mijinta takeyiba gani takeyi babu namijin dazata Aura daze kaishi dadih da iya love, kullum tana fatan ya zamto mijinta a gidan Aljannah. Alhaji murtala ya nufa wata kofa dazata kaishi har inda yake sauka, hajiya maryam ta nufa falo inda su muhammad da salwah suke. Da sallahma ta turo kofar falon ta shigo ta gansu zaune a kn 3ct daf daf da juna se aikin Hira sukeyi suna shewa, nan ta umurcesu dasu tashi suje suyi alwala suyi sallarh , sukace toh hadi da mikewa a tare suka fito daga falon Muhammad ya nufa hnyar da mahaifinsa yabi ita kuma salwah ta nufa bedroom dinta hajiya maryam ma ta nufa nata bedroom din, tana shiga ta fada toilet ta dauro alwala ta dawo dakin tayi sallah ta sallame hadi da addu'ur'inta ta mike ta cire hijjabin datayi sallarh dashi ta ajiyeshi a mazauninsa kana ta fice a dakin ta nufa dakin Salwah, da sallahma ta tura kofar bedroom din ta shigo, taga salwah zaune a kan dadduma ta idar da sallah kenan tanata lazimi, karasawa tayi ta zaune gefen bed dinta ta daura kafa daya kan daya, jiki na rawa salwah tayi addu'ur'inta ta shafa kana ta juyo ga mahaifiyar tata kallo daya ta mata taga fuskarnan babu annuri da hnzari ta dauke kwayar idonta a kanta. Hajiya maryam tayi kwafa kana ta fara mgna da muryarta me cike da tsiya "Ke kibi duniya a hnkli knji na gaya miki! Ke da ace ba a tsaye da kanki da an shiga uku! Domin kuwa ke dinnan yarinya da an barki Allah kadai yasan me zaki Aikata a doron kasa,..." Salwah tayi shiru yynda kwayar idonta ke kasa Ta zubawa kan tiles din dakin me kama da madubin duba fuska ido se walwali tiles din yakeyi, a ranta tunani takeyi shin me tawa mahaifiyar tata againt ita de bataga abnda tayi ba na wannan fadan, koda yake Amihh ko babu lefi fada takeyi, shiyasa ba a gane mi akayi mata. Hajiya maryam data dakata da mgna se bin salwah takeyi da ido taci gaba da mgna still muryarta cike da tijara "kinje kin kebance da d'ana miji kun zauna ga kujera daya sbda rashin sanin darajar kai, ko kamun kai ne baki dashi oho, to tin wuri ki natsu, namiji ba abin shishshige mawa bane, koda kuwa uwarku daya ubanku daya tinda ba mijinki bane, kina jina kou? Kika kuskura na kara ganinku a kujera daya se naci mutumcin dangin ubanki, knji na gaya miki, zan nuna miki ainihin wacece ni a ranar..." Tana gama fadar hkn ta mike tsaye hadi da jan kwafa tace "kinga kwana biyu ban duba mutumcinki ba, to yau zan duba in gani, dan ubanki..." Tana gama fadar hkn ta fice a dakin, salwah ta dago kai tabi byn hajiya maryam da ido wasu lokutanma mamaki mahaifiyar tata take bata, sbda wani fadan nata beda dalili wato ba kai ba gindi, ita ba halin ta zaune kusa da Muhammad kenan a matsayinsu na yan uwan juna, ba tin yauba daman hk hajiya maryam ke matsa mata, duk sanda zatazo hutu gunta seta duba mutumcinta wai har ynzu yana nan, ita de salwah abin ma ya fara isarta, ss ayita ganar mata jiki a bnza. Mikewa tayi hadi da sauke ajiyar zucia ta fice a dakin, direct kicking ta nufa. Nan taga hajiya maryam tasa hannu anata shiryawa baki abinci iri daban daban. Da suka gama ma'aikatan da salwah suka kai kalolin abincin da drinks falon da Alhaji murtala yake. Ranar nan sukaci abncin rana a tare da hajiya maryam da Muhammad da salwah se Alhaji Murtala, suna cin abncin suna raha suna daria har suka kammala, salwah da Muhammad suka kwashe dukkanin abnda suka bata suka nufa kicking. Alhaji murtala da hajiya maryam suka koma kan kujerarun falon suka zauna, nan Alhaji Murtala ya shaida mata abinda ke ransa na son ta koma garin kaduna,,,bayan duk ya gama tsarata a tunaninsa ma ta riga ta gama amincewa hajiya maryam daketa binsa da ido har l ya kare fadar abinda ke ransa tayi jim ta sauke ajiyar zucia hadi da gyara siririn glashin dake manne da kwatar idonuwanta. Cikin natsuwa ta fara mgna "amm... Alhaji kaduna kuma? Ni maryam in koma kaduna? Haba Alhaji ka duba mgnr nan taka da kyau, inkoma kaduna inyi mi a can? Bayan nan ga ayyukana inayi, ni bazan ma iya zaman kd ba gaskia,,sam sam na fi jin dadin nan kano, sbda nan na fara zama tin zuwana Nigerian,...Alhaji da ace in koma kd ai kwara ace in koma indian kawai..." Ta karashe maganar babu alamar ma tana ra'ayin kd a rayuwarta. Alhaji murtala yayi jim kawai ya zubawa maryam ido yasanta kaifi dayace intace zatayi to zatayi in tace batayi to tabbas batayi, koda kuwa me za ayi mata bazata taba yinba, dan hk Alhaji murtala ya sauke ajiyar zucia a ranshi yana me maimaita ''babu nasara..." A fili kuma yace "Okay Shikenan kawai...amma ni da naga zumuncinmu zefi karfafa ne, ga yaranmu ma zasufi zumunci sbda muna da kusanci da juna, Amma de maryam kiyi tunani ..." Jinjina kai hajiya maryam tayi kwayar idonta na kn Alhaji babba tace "Okay..." A takaice tayi mgnr, wasu lokatan ita AB'ILAL ya biyo gurin mulki sbda tanada jinin sarauta a jikinta, shi kuma jinin sarauta baya boyuwa ko yaya ne se an nuna isar nan d mulkin nan. Hira suka dan shiga tabawa alhaji babba de se yin iya bakin qoqarinsa yakeyi kan yaga ya shawo knta ta yadda zata koma garin kaduna amma fir hajiya maryam taki dadin kai. Kwana sukayi a garin kano washe gari da sassafe suka hau hanyar zuwa garin kaduna, byn hajiya maryan ta cika Muhammad da abin arziki tace ya kaima uwarsa da sauran iyayen nasa, wato matan babanshi, hajiya maryam mutumce wadda sam abin hannunta be rufe mata ido ba, tanada kyauta ba ruwanta da arzikinka inhar taso zata baka koda kuwa kai ne maliya, dan hk bata la'akari da dangin mijinta masu shine tana kyautata musu hadi da nakasa da ita, shiyasa hatta ma'aikatanta kejin dadinta Ainun matsalarta daya ce akwai tsare gida wato bata da wasa ,amma kuma tasan darajar dan adam ita hk nature dinta yake, akasin AB'ILAL da besan darajar kowa ba shifa ganin kowa yakeyi dan iska ne inka cire hajiya maryam wato uwarsa. Akwai wata rana daya taba kama me gadinsu da matarshi suna kissn juna da daddare tazo tayashi zama a inda yake gadinsa dayake a nan gidan take an basu bangare guda a cikin bangarorin ma'aikata. Kawai AB'ILAL ya dawo daga masallaci yazo ya gansu bakunan juna cikin na juya rnshi yy mugun baci ya rufe idanuwansa cike da kyama, kana ya budesu ya saukesu a kn me gadin nasu, da matar tashi dasuka ankare da zuwansa suka saki bakin juna tini, nan take AB'ILAL ya masa kaca kaca yana ce masa dan iska, ya koresa a gidan yace ya bar gidan shida matarsa a yanzu ynzu , baballe me gadi ya zube kasa ya hau bashi hkri yana kuka yana ce masa matarsa cefa, AB'ILAL kam ko ga jikinsa shide kawai isknci ya gani ba ruwanshi da wani matarshi ce,...kukan da baballe keyi shine har yajawo hnklin hajiya maryam ta jiyo datake falonta sbda kuka riris baballe me gadi keyi, shine datazo taji abinda ke faruwa tace Baballe me gadi baze bar gidanba, tinda ba isknci yakeyiba ko a tsakiyar gidan ya kusance laminde matarsa ce ba matar wani ba, halak malak yaci ba zina yayi ba, AB'ILAL ya cika ya batse ya fice a gurin fuuuu! Ya nufa hnyar side dinsa ta kofar baya, rai a matukar bace Sbda Beda yadda zeyi inhar Amihh ta fadi abu to dashi ake amfani ko anaso ko ba aso. Tin daga rnr AB'ILAL ya dasawa baballe me gadi karan tsana, da duk ma'aikatan gidan maza da mata, shi gani yakeyi kmr duk cin juna sukeyi, shifa ko mace ya gani da namiji suna mgna shikenan shi a gunsa yan iska ne, sam shi irin mutanen nan ne da be kaunar zina kai ko hnyar da zina tabi beson bi, ko sunan zinarma be son fadi da tsarkakken harshensa. A ranar da yammaci hajiya maryam ta shirya ta nufa gidan hajiya juwairiyya kawarta ta amana (like me and mrs Asal) A bedroom din hajiya Juwairriyya suka yada zango Hajiya maryam ta kwashi bukatun da Alhaji murtala yazo mata dashi na ta koma kaduna ta zayyanawa hajiya Juwairriyya, shiru hajiya Juwairriyya tayi hadi da maida numfashi tana nazari, kana ta fara mgna. "Ki koma kd kuma? Hajiya