← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 225

Sashe 57

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salwah dake zaune a falon har zuwa ynzu, kmr daga sama taga shigowar mahaifiyarta riqe da mutum a hannunta kmr mataccia, ga jini nata kwarara daga kanta har zuwa ynzu. A razane Salwah ta mike tsaye ta zubawa fuskar mahaifiyar ido nan take ta hango tsananin tashin hnkli hadi da damuwa kwance a kan fuskar tata.."Amihh.. meya .. faru?'' Abinda ya fito daga bakin Salwah kenan murya na rawa. Sam Hajiya maryam bata sanma me salwah ke cewa ba, ta wuce ta, ta nufa bedroom dinta da hilwah a rungume a jikinta wadda ke sume batamasan inda knta yake ba. salwah ta biyo bayanta fuska dauke da ayar tambaya hadi da tausayawa,,,,a kan tamfatsetsen bed dinta hajiya maryam ta ajiye hilwah jikinta nata rawa , ta daburce ta hau safa da marwa a dakin tama rasa ta ina zata fara, taga tashin hnklin daya fi wannan amma wannan ya tsaya mata a zucia, fiye da tunanin me ji da gani. Salwah dake tsaye ta karasa bakin gadon jikinta na rawa ta zubawa fuskar hilwah ido, ita knta seda taji gabanta ya fadi, tsantsar tsagwaron kyaun hilwah dinne ya fadarwa da salwah gaba, bata taba ganin me kyau kmr ita ba. "Amihh ko ta mutu ne?'' Salwah ta fadi hakan fuskarta dauke da zallar farin tashin hnklin ganin kmr hilwah bata motsi. Hajiya maryam kam se faman zagaye dakin takeyi ta rasa ma ya zatayi, duk knta ya kwance. Kmr an tsunguleta ta juya ta fice a dakin jiki na rawa ta nufa wani daki a gidan wanda yake kmr asibiti ne akwai komi da komi a ciki, ita ta zubasu dawowarta kadunar da kwana daya. Ba bata lokaci ta kwaso duk wani abu dazata bukata ta fice a dakin ta dawo dakin da hilwah take salwah na zaune ta gurin knta se faman kuka takeyi tana jijjigata kmr zautacciya haka kawai ta tsinci knta dayin kuka bayan fitar maryam a dakin, kukan da salwah keyi seya kara kid'ima hajiya maryam, ya kasance idanuwanta a bude suke amma kuma sam bata gani dasu Sbda tsabar tsananin kid'imewa, jiki na rawa ta shiga bawa hilwah taikon daya dace, a farko seda ta fara mata allurar dazata farfado da ita daga doguwar sumar da tayi, ta farfad'o amma kuma bata bude idonta ba, numfashinta ya dawo yadda ya kamata, sede batasan inda knta yakeba, hajiya maryam ta mata allurar tsaida jinin daketa aikin zuba a kan nata, duk abinda hajiya maryam kema hilwah zuciarta na maqale da tausanta. Salwah ta koma gefe se sharar kwallah takeyi, duk ta gigice. Duba inda hilwah ta bugu hajiya maryam tayi, nan taga gurin ya fashe sosai har sema an mata dinki gashi kuma gurin akwai gashi, gashin ma ba dan kadanba, dole seda hajiya maryam tasa reza ta aske gashin dake gurin kadan, danta samu damar mata dinkin, seda ta mata allurar kashe zafi kana ta fara mata dinkin, this is the first time data taba jin tausai sosai da sosai da tanawa hilwah dinkin ji takeyi tamkar jikinta take d'inkewa. Bayan ta gama mata dinkin ta kara mata wata allurar a bom-bom ta gyara mara kwanciarta sosai kana ta koma ta zauna kasan carpect din dakin ta zubawa hilwah ido ta rafka uban tagumi hannu biyu biyu, kar kaso ka bincika kasan zuciarta, duk ta daburce gashi ynzu batasan ma ina zata samu number din yan uwan yarinyar ba ta sanar dasu abinda ke faruwa, ta ma rasa ya zatayi.. Salwah data tsagaita da kukanta ta dawo gefen hilwah ta zauna ta zuba mata ido, yayinda farar fuskarta tayi ja jawur sbda tasha wahala, sumar nan tata ta kwanto har zuwa kirjinta, idanuwanta a rufe ajiyar zucia kawai taketa saukewa a kai a kai. Salwah ta dawo da idanuwanta kan mahaifiyarta tana neman karin bayanin meya faru amma tasan bazata samu ba, saboda ta kula ma mahaifiyar tata kmr bata hayyacinta. Suna nan zaune jugum jugum har lokuta suka shude awanni suka tafi, yammaci ta gabato hilwah bata farfad'oba. Mikewa hajiya maryam tayi jiki babu lala ta nufa toilet. ba jimawa ta fito byn ta dauro alwala ta saka hijjabinta nayin sallah ta shimfida dadduma, ta tada sallarh la'asar.... Salwah ma mikewa tayi ta nufa toilet domin dauro alwala , ita duk ta mnta ma batayi sallarba sbda tsabar kidimewa seda taga Amihh na sallah shine ta tuna. Fitowa tayi daga toilet din byn tayi alwalar idanuwanta na kn hilwah ta juya ta fice a dakin ta nufa dakinta danyin Sallar la'asar din, duk tabi ta damu da lamarin hilwah dukda batasan wacece ita ba. Har tayi sallarh ta idar hilwah na ranta, ko hijjabin dake jikinta bata cire ba ta dawo dakin inda ta samu Amihh zaune gefen bed din, zuwa ynzu ta fara firgita da lmrin na har ynzu hilwah bata farfadoba , kuma yaci ace ta farfado bayan awa daya, Amma gashi awanni uku na neman shudewa bata farfadoba. Salwah ta karasa ta zauna a bedside drower ta zubawa hilwah ido,,,dukkaninsu su biyun ita suka zubawa idon... Har lokacin sallarh magrib yazo , suka mike suka gabatar da sallarh magrib din, dukkaninsu hnklinsu na kan hilwah, a cikin sallarh suna aduarh suka rinka mata Allah ya tashi kafadunta. Suna idarwa suka dawo suka kara yin jugum jugum, hajiya maryam se aikin duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta takeyi, karin damuwarta dayace tasan iyayen hilwah suna can suna nemanta ruwah a jallo. A hnkli hilwah ta fara bude kwayar idonta a dai-dai kan fuskar salwah dake zaune a bedside, ji tayi kanta ya dan mata nauyi, nan ta shiga zagaye dakin da kwayar idonta, tana me kokarin tunano abinda ya faru.... Salwah ce ta ankare da farkawar tata kasancewar hajiya maryam ta lula duniar tunani. "Sannu..." Ita ce kalmar data iya fitowa daga bakin salwah, shiru hilwah tayi ba tare data amsaba ta bi salwah da ido. Sannun da Salwah tace ne ya dawo da hajiya maryam duniyar tunanin data afka, ta sauke kwayar idonta a kan Hilwah, ita ma dawo da kwayar idonta tayi kn hajiya maryam din se ynzu ne abnda ya faru ya dawo cikin knta. Nan hajiya maryam ta shiga jerowa hilwah sannu , ji takeyi kmr zata maidata ciki, ita de hilwah se bin hajiya maryam da salwah take da ido, tanajin wani irin sanyi a ranta. "Me ke miki ciwo yanzu?'' Hajiya maryam tayi tambaya hilwah cike da kula kwayar idonta na kanta, tana zaune gefen bed din. "Kaina...." hilwah ta fadi cikin sanyin murya, hajiya maryam ta matso ta kamo hannunta cikin nata kana tace "ze bari,,sannu knji baki ganin jiri?'' Hilwah ta daga mata kai hadi da cewa "Ina gani kadan kadan..." Hajiya maryam ta kara damqe hannunta cikin nata tanajin wani irin sanyi a ranta kasancewar hannunta dake cikin nata. "Sbda jinin da kika zubar ne....sorry knji , ngde da abinda kikayi min Allah ya jibanceki da lamarinki sbda annabi s.a.w..." Duk suma suka amshe da s.a.w. wani irin murmushi hilwah ta sakarwa Hajiya maryam, ita ma ta sakar mata murmushin. Salwah de ta zuba musu ido bata taba ganin annashuwa a kn fuskar Amihh ba tinda take da ita se yau, annashuwar data gani a tattare da itan me fidda annuri ce, tanaso tasan meyasa amihh ke ma hilwah godiya. "Me kikeso kici?'' Hajiya maryam ta tambayi hilwah har zuwa lokacin hannunta na cikin nata duka biyu. Girgiza kai hilwah tayi alamar bazataci komi ba. Hajiya Maryam ta dansha mur tace. "Se kinci fa...." Tayi mgnr hadi da mikewa da niyar ta fice a dakin, hartakai bakin kofar fita ta juyo ta kalli hilwah wadda itama, kwayar idonta ke kan hajiya maryam. "Ya sunanki ?'' Hajiya maryam tayi tambahar. "Hilwah..." ta bawa hajiya maryam amsar tambayarta tana lumsar idanuwa. Maimaita sunan nata hajiya maryam tayi a bayya ne. Salwah kuma ta maimaita a kasan ranta ba karamin dadih sunan ya mataba. Juyawa hajiya maryam tayi ta fice a dakin, salwah ta zubawa hilwah ido se sannu taketa mata, hilwah ta daga mata kai hadi da sakar mata dan guntun murmushi, salwah ta mayar mata da kayataccen murmushin itama kana tace "Sunanki dadih .." Hilwah ta kara sakar ma salwah murmushin gefen baki tace "thank you...ke ya sunanki..." "Sunana Salwah.." Ta bata amsa cike da jin dadin mgnrta harta. Salwah harta fahimci hilwah nada karyayyen harshe mgnrta seka natsu zaka ganeta sosai. "Rabin sunana..." Cewar hilwah, salwah ta kara kureta da ido, yanzu ta kara fahimtar hilwah bata da R da S kwata kwata a bakinta. "ni da ke duk munada rabi rabin suna, ke hilwah ni kuma salwah..." Cewar salwah da farin ciki ya cika mata zuciya hk kawai takejin dadin mgnr hilwah, Dan haka ta hau janta da hira sama sama, wai a hk ma dan tana tausanta ne bata da lafia da lafiarta lau seta dameta da surutu sosai, sbda tanaso tayi ta jin muryarta me dadin nan. A hk hajiya maryam ta dawo dakin ta samesu hannunta dauke da trea.l, se taji dadin yadda tazo ta samesu suna hirar hkn ya bata tabbacin jiki yayi sauki. Krsowa Hajiya maryam tayi ta zauna gefen bed din ta ajiye trea din dake hannunta a kasa ta bude kular dake dauke da superghetti wadda taji kayan lambu da bushashshen kifi da nama da danyan kifin ma duka. ta zuba mata a plt Me kyau, da knta ta dagota ta jingina mata bayanta da fuskar bed din.. ta shiga bata jlp din superghetti din a bakinta, ta amsa zucia cike da farin ciki, seta tuna mahaifiyarta ita ke bata abinci safe rana da daddare a baki, sam batasan cin abinci da kntaba seda ya zamana ta baro gidan iyayenta, shine ta iya kai lomar abinci bakinta. Tsaf hajiya maryam tayi feeling dinta taci sosai ta koshi gashi bata taba cin abinci me dadinshi ba. Ta bata drinks din strawberry Wanda ta hada da hannunta, tasha taji wani irin ddh. Mikewa hajiya maryam tayi ta fice a dakin, ba jimawa ta dawo hannunta riqe da magunguna ta bawa hilwah tasha, ta koma ta kwanta tanajin damar jikin nata. Salwah se aikin sakarwa hilwah murmushi takeyi, itama tana mayar mata da adashen murmushin. "Ina ne gidanku? Se inje in sanar da mahaifiyarki halin da kike
Chapter 57 · 0% Book details