Sashe 39
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bangaren AB'ILAL kam yana isa falon hotel din ya yada zango kasan carpet. Se sauke numfarfashi kawai yakeyi yanajin zuciarsa na masa quna hadi da rad'adi da zafin da besan dalilinsaba, a zahirin gaskia de yaji a ranshi ya tsaneta tinda yake a rayuwarshi be taba tsanar wata mace ba kmr yadda yaji a ranshi ya tsani Wannan yarinyar, se kara hasko surarta yakeyi da yanayin kayan dake jikinta, nan da nan tsanarta ke kara ninkuwa a zuciyarshi. Wayarshi daya shigo da ita ya lalubo ya budeta a tsiyace ya cire sim din dake ciki yasa a aljihunsa ya mike ya nufa bedroom wayar na hannunshi riqon wulaknci, direct bathroom ya nufa ya bude gidan toilet ya wurga wayar a ciki yayi flushing dinta ta wuce, zuciarshi cike da tsanar wayar saboda taba ta da hilwah tayi da hannunta. Se jan uban tsuki kawai yakeyi ya dawo ya kwanta a carpet din dakin, ya dafe knshi da hannayenshi duka biyu, kwata-kwata yau beda sa'arh ko yace be tashi da sa'arh ba, a gidan Alhaji murtala ya hadu da tantiriyar karuwa har taba masa hannu tayi, again yanzu ma ya hadu da wadda ma taci uwar zee karuwanci a hotel wadda da gani base an fada maka ba kanada tabbacin karuwa ce wadda duk namijin dayaga danar tsoma alqalaminsa a tawadarta ze tsoma harma ya samu ya dangwalo tawada, ba tare da bata lokaci ba. AB'ILAL be taba tsanar mace kmr yadda ya tsani hilwah ba, kwata-kwata baya fatanma ya kara ganinta a rayuwarshi, ga mace har mace amman sede ba macen arziki bace, karuwa ce. Gaskia AB'ILAL ya fara tunanin anya Auwal hubb ba baki ta masa ba yaketa haduwa da irin wadannan kaddarorin marasa kyau a zuwansa kano. Idanuwansa na lumshe ya fara addu'ur'in neman tsari daga matsifun duniya irin su hilwah, ajiyar zucia kawai yake saukewa yna me kyasto hilwah a ranshi,. Duk yabi ya tsaneta, hkma ya tsani hotel din kyamarsa ma yakeyi. Miqewa yayi ya shiga hada kayanshi dake dakin yana jan uban tsuki yace "Wallahi bazan kara kwana a matattarar zunubin nan ba.." Ya hada komi nashi tas ya dawo dasu falo ya dauki wayarshi kirar Samsung ya lalubo lambar Alhasan ya danna masa kira, bugu daya biyu Alhasan ya daga. "Kai da Allah ni ka dawo ka dauke ni!'' AB'ILAL yayi mgnr a hasale kai kace Alhasan ne ya masa lefi. Alhasan da tuni ya iso gidanshi harma ya kwanta AB'ILAL ya kirashi , fuska dauke da mamakin jin muryar AB'ILAL a hasale mutumin dasuka rabu ba jimawa lami lafiya. Alhasan yace "in dawo in daukeka kmrya?" Ai nan fa ya kara harzuqa AB'ILAL ya daka masa wata uwar tsawa kmr ubansa. "Ka dawo ka dauke ni nace, daga hotel din nan, kawai ni yau zan koma kano...ka maidani kanon kawai!'' Alhasan ya zaro ido jin ab'ilal na mgnr yazo ya maidashi kano a tsohon daren nan, ana neman kusan 11:30pm ne, nan Alhasan ya fara tunanin ko de AB'ILAL shaye shaye ya fara ne. Ya bude baki da niyar zeyi mgna ya tsinkayi muryar AB'ILAL ta cikin wayar yana cewa ''nan da 5mnt kazo ka daukeni daga hotel dinnan!'' Yana gama fadar hkn ya katse wayar, ya zirata a aljihu se huci kawai yakeyi ya gaza zama ya hau zagayen falon, yanada tabbacin a wannan halin dayake ciki baxe iya driving ba, da tini ya fice a gidan ya dauki hanyar kano yaje gun Auwal hubb dinsa ya durkusa ya nemeta gafara ko kila inta yafe masa ya rabu da irin wadannan mutsibun duniyar. Yana nan tsaye yana zirya a falon a haka har Alhasan yayi knocking kofar falon after 10mnt dasukayi waya dashi, shine ya debo mota ya zo, karasawa yayi ya bude masa kofar falon rai a matukar bace, Alhasan ya shigo sanye da kayan bacci danshi har yayi ma shirin kwancia AB'ILAL ya kirashi. Tsayawa Alhasan yayi ya shiga karewa AB'ILAL kallo, kallo daya biyu uku ya masa yaga canjin yanayi a tattare dashi ba kmr yadda ya barshi ba dazu. Da ya debo matsifa ne yaso ya sauke masa Amma ganin yanayinsa ya tabbatar masa da ba lafia ba, idanuwanshi ne suka sauka a kan kayanshi da komi nashi daya ajiye a kasan carpet din falon. AB'ILAL yaja dogon tsuki idonshi na kan Alhasan wanda keta faman karewa falon kallo, bayan ya gama kare masa kallo. "Se ynzu kaga dmar zuwa,...kuma ka tsaya kana karemin kallo, again ka dawo kallon falo, tinda gidanku ba falo Ai...da Allah guy in bazaka dauke ni bane ka gayamin in samu mota a kan titi in roqesu su temaka min..." A matukar harzuqe AB'ILAL yake mgnr zuciarshi kmr zata fashe dan saboda tsabar takaici bisa takaici. Shiru alhasan yayi ba tare dayace masa uffan ba dan yasan inyayi mgna zasu iya hawa sama ta bakwai su fado sbda ya kula a hasale yake, dan haka ya kwantar da murya. "Muje ..." Ba tare da ab'ilal ya dauki komi ba bace wayoyinsa dake jikinsa ya fice a dakin, alhasan ya nufa bedroom din ko zega wani abu nashi important be gani ba, dan hk ya dawo falon ya kwashe kayan dake yashe kasan falon, ya fice a dakin ya kulleshi da key yabi linter ya sauko kasa, ya bawa masu hotel din key dinsu suka masa mgnr sauran kudinsa dake hannunsu yace bkm su barshi sukayi ta masa godiya be bi ta knsu ba ya fice, hannayenshi niqe niqe da kaya, ya iso bakin motarshi nan ya samu ab'ilal se jero uban kwafa yakeyi ya jingina bynshi da motar se kwafa kawaui yakeyi,Alhasan na Karasowa ya rufeshi da balbalin bala'i idanuwanshi a rufe kmr makaho. "Wani irin wulaknci ne wannan, ka ajiyeni inata jiranka! Look in baza ka dauke ni a motarka bane kawai ka gayamin!" Alhasan ya kalleshi kawai ba tare daya ce komiba ya bude motar Ab'ilal ya shige mazaunin baya , Alhasan ya girgiza kai kawai ya zagaya ya bude dayan murfin kofar bayan ya ajiye kayan dake hannunshi ya mayar da murfin ya rufe, kana ya shiga dreva seat ya tada motar suka bar hotel din yana fadin. "To motarka fa da muka bari a nan?" Ya jefowa AB'ILAL tambayar. Ab'ilal dake kwance a baya , yanajin zuciarsa na masa kunci kai kace mutum ya kashe, zuciyarshi duk ta cunkushe da kunci, dukda yaji me Alhasan yace Amma yayi banza dashi kai kace da dutse ake mgna, se sanyin AC motar kawai ke ratsashi. Alhasan yaci gaba da driving dinsa kawai danya kula ba lafiya, "ynzu ynzu se Allah," ya fadi hkn a zuciarshi. Har suka isa gidan Alhasan AB'ILAL bece komi ba, se aikin kwafa kawai yakeyi, suna shiga gidan Alhasan yayi packing a packing space din gidan. AB'ILAL ya fito yana karewa gidan kallo, Alhasan ya fito hannunshi riqe da car key se wayarshi kirar Samsung shima. "Ina ne nan ka kawo ne?" Ab'ilal ya tambaya cikin gadara da isa da tsabar bura uba dake cinsa a rai. Murya cike da mamaki Alhasan yace " gidana mana..." Wani irin dan iskan kallo AB'ILAL ya bishi dashi yace "wani irin iskan ci ne, wannan ...ni cewa nyi ka kawo ni gidanka, ka kaini kano nifa bazan kara kwana a kd ba kawai ka kaini kano..." Alhasan ya zubawa AB'ILAL ido harya dauki maganarsa ya dire a hasale, girgiza kai kawai alhasan yayi ya duba agogon wayarshi yaga 11:45pm, cikin sanyin murya yace ''malam yanzu fa 12:am muke nema taya zamu dauki hanyar kano, in kayi la'akari da yanayin kasarmu yadda ta kom...." AB'ILAL ya kara harzuqa a hasale ya katse Alhasan "ina ruwana da wata kasa! Malam in bazaka kaini ba kawai kace kai baza ka kaini ba, bani car key dinka..." AB'ILAL ya karasa mgnr hadi da mikowa alhasan hannu shi a dole seya bashi key din motarshi dake hannunshi. Hade rai Alhasan yayi ganin haukar na AB'ILAL na gaske ne, ya gaji da lallabashi. "Bazan baka ba, kai mahaukacin ina ne dazaka dauki hanyar kano yanzu da tsakiyar daren nan,..." Alhasan yy mgnr shima a hasale. Ab'ilal ya kara hasala ya daga kafada cikin izza da mulki da kasaita yce ''ina ruwana da dare, in zaka bani key ka bani kawai ni kano zan tafi, bazan kara kwana a wannan garin naku ba na manya manyan karuwai da yan DANDI..." Karshen mgnr tashi ta bawa Alhasan dmr gano tabbas wani abu akawa AB'ILAL din daya harzuqashi har haka, maybe wata macece ta kawo masa kanta..." Zuciar Alhasan tayi wannan tunanin. Nan de ya shiga lallaba AB'ILAL wanda ya dage kan dole shi seya bar garin zuwa garin kaduna a wannan tsohon daren me furfura. Da kyar AB'ILAL yabi alhasan zuwa cikin gidan nasa madaidaici me madaidaicin kyau da Tsaruwa, a bedroom suka yada zango AB'ILAL ya haye kan bed din zuciarsa babu dadih, jinsa yakeyi tamkar bashi ba, daya lumshe idanuwansa surar hilwah ce kawai ke masa yawo a idanuwansa, dan hk bema son lumshe idanuwan nasa, . Zaunawa gefen bed din Alhasan yayi zucia fal damuwa ya zubawa AB'ILAL ido wanda idonshi ke kallon saman dakin, se ajiyar zucia kawai yake saukewa. "Frnd wai meke faruwa ne dakai plx?'' Alhasan ya jefowa AB'ILAL tambayar cikin sanyin muryarsa me cike da damuwa.
"Fans kuyita hkri dani plx...."
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi 💃💃💃.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni 😀😀.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jiku💃💃💃💃💃💃
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*YAR DANDI CEH*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
(SHE'S A WORLDLY PERSON)
SAADATU BINTU ABDULLAHIâœðŸ?
*Writer of KYAUTAR ALLAH* ga masu bukatar books din marubuciar su tuntubi lmbr nan 08136349646.
"Fans kuyita hkri dani plx...."
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi 💃💃💃.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni 😀😀.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jiku💃💃💃💃💃💃
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*YAR DANDI CEH*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
(SHE'S A WORLDLY PERSON)
SAADATU BINTU ABDULLAHIâœðŸ?
*Writer of KYAUTAR ALLAH* ga masu bukatar books din marubuciar su tuntubi lmbr nan 08136349646.