Sashe 180
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
toilet din jiki babu vitamin A, Amihh ta juya ta fice Zuwa side dinta, ta nufa kiching domin ta hada masa abinci mara nauyi me sauki,,ba bata lokaci ta gama hada masa dafadukan superghetti me Irish wanda ta cikashi da kayayyakin ganye na gina jiki, ta gama ta juye a kulah, ta hada masa farfesun cow leg, ta juyeshi a cikin kular shima,, ta hada masa drink me sauki hadi da gina jiki, ta hada duk kulolin a kn tray, hadi da jug din drink din, ta hada plate da bowl da cup din jug din, data zuba drink din a ciki, ta dauko bottle water me sanyi ta ajiye a tray din, jikinta har yana rawa ta gama ta dauko tray din zuwa side dinsa, a falo sukayi kicibus hanyar fitowa, ta tsaya ta zuba masa ido, sanye yake da jallabia me layi layin kalar dark mint color, and light mint, ta saman jallabiar duk aikine me kyau da tsaruwa, dukda ramat da yayi amma jallabiyar ta amsheshi.. ''fita zakayi?'' Amihh ta jefo masa tambayar. Daga mata kai yayi Alamar Eh, Amihh tace "Ina zakaje?'' Ab'ilal yace "Zanje gunki ne Amihh tin daxu na gama wankan, zanzo ne ki gayamin ina yarinyar take..." Hjya maryam tayi shiru ta zuba masa ido, yaro duk ya susuce. "Muje dining kaci abnci, tukunna...." Ta fadi hkn hadi dayin gaba, ya biyota a baya, ta ajiye tray din a kn dinning table din, AB'ILAL yaja kujerar daya daga kujerun dinning din ya zauna, hadi da zubo mata ido, ya rafka uban tagumi. "Babana cire tagumi ..." Amihh ta fadi hadi da jnye masa hannunsa daga tagumin da yayi, tana tsaye, ya langwabar da knsa gefe, se kara langwobewa yakeyi ko ze samu Amihh ta kara jin knsa, sosai ta gaya masa inda yarinyar take,,amma jikinsa na basa da wuya ta gaya masan. Da knta ta zuba mata superghetti din daketa kamshi a ciki plate, ta tura masa gabansa, hadi da caka masa face a cikin superghettin. ya zubawa superghattin ido , amihh ta zauna kujerar kusa dashi, sam ko yunwa bataji dukda ana nemn 10:am ne lokacin, ka ta saba karyawar wuri amma sam batajin yunwa. "Bismillah kaci mna, se in gaya maka inda take....." Cewar Amihh, ba bata lokaci AB'ILAL ya dauki fake ya faracin superghatti yanaci yana lumsar idanuwa, ji yayi abncin na Amihhn ma ba ddh har wani daci daci yake masa a baki, kawai yana daurewa ne, yanaci tunawa da yayi da tace zata fada masa inda hilwah take, Amma har zuciarsa tashi ma takeyi., yanacin superghatti yanawa Amihh sambatu a kn yarinyar, duk lbrinsa a kn yarinyar ne, "Amihh de nata ido, duk ta daskare a zaune, uban yan taurin kai da rashinji duk yabi yayi Sanyi kmr ma bashi ba. Kadan yadanci superghattn ya barshi hk, shi a ganinsa yaci da yawa sbda ya mance yaushe rabonsa da abnci me amsa sunansa abinci ya shiga cikinsa yama mnce, inba jiya ba dayaci kadan a gidan hjya karama, yau km yaci dayawa. "Ka k'oshi kenan?'' Amihh ta tambaya ganin ya ture plate din gabanshi. Daga mata kai yayi alamar A. "Ka kara plz..." AB'ILAL ya girgiza mata kai alamar Aa'h, ba tare dayayi mgna ba. "Ki gayamin ina take to Amihh tinda naci abncin..." Ya fadi a marairaice, duk yabi ya kagu. Ba tare da amihh tace masa komi ba, ta tashi ta dauki bowl ta zuba masa farfesun, ta tura masa gabansa ya kalli farfesun ya dago ya kalleta, hadi da girgiza mata kai, ta daga masa kai, ba musu ya fara cin farfesun kadan ya danci yasha drink ya tashi a kn dining din ya koma kn kujerar 3ct ya zauna, yanajin zuciarsa na tsananta tashi, Amihh ta biyoshi tana fadin 'Baka ci komi ba sosai..." AB'ILAL daya rike knsa dake tsananin masa ciwo, abncin daya gamaci se taso masa yakeyi sosai, cikin dakiya da dauriya yace "Am ok Amihh, in ba na gnta ba bazan iya cin abnci bama kwata kwata..." Karasowa Amihh tayi ta zauna kusa dashi, takawo hannunta ta taba knsa taji ya dau zafi rau-rau, "'kanka na ciwo ne?'' Ba tare daya bata amsa ba, ya mike cikin hnzari ya nufa toilet din falon, amihh ta biyoshi a baya, ta taddashi a durkushe a kasa Se kwarara aman abubuwan dayaci ma cikinsa yakeyi, Amihh ta zuba masa ido, har ya gama amayar da kaf abubuwan dake cikinsa, nan take jikinsa yayi laushi lubus, Amihh ta bashi ruwa ya kuskure bakinsa, ta zuba masa ruwa a knsa, se yaji sanyi, ta wanke masa face dinsa,, ta rikoshi suka dawo falon ya kwanta a kn kujerar 3ct se sauke numfarfashi yakeyi, cikinsa nata murd'a masa. Sannu kusan uku amihh ta jero masa a lokaci daya. daga mata kai kawai yy, ta juya ta nufa toilet din ta gyara inda ya bata da aman, kana ta dawo ta fice a dakin ta dauko kayayyakin aykinta ta dubashi sosai, a nan ta gane bugun zuciarsa ta yawaita ya wuce yadda akeso, hnklin Amihh ya tashi, tasa masa drib domin ya samu sassauci da karfin jikinsa, tasa masa alluran baccia drib din, ruwan na fara ratsa jijiyoyinsa, ba jimawa kuwa bacci ya kwasheshi, Amhh ta zauna kujerar dake fuskantarsa ta zuba masa ido, duk jikinta yy sanyi... Rnr nan side din nasa Amihh ta wuni, tanata bashi kulawa, har dare, se tambayarta yakeyi ina matarsa take, Amihh se kwantar masa da hnkli takeyi, tin 2:pm, drib din data sa masa ya kare. da daddare byn yayi sallar isha'i yau duk, a gida yayi sallolin sa, amihh ta bashi abnci ta matsa masa yaci, ta masa allurori, ya kwanta a kn bed dinsa, Amihh ta zauna a bedside se kara tambayarta yakeyi a kn ina matarsa, amihh ta masa shiru dan gani takeyi beda lafiar hnkli,, ta zura masa ido, har bacci ya kwasheshi yana sambatun cewa, ina matata! amihh tayi ta masa addu'ur'i tana tofesa dashi harta samu ya tsagaita da sambatun nasa, ta lullubeshi sosai da duvet ta fice a falon, zuwa side dinta, tana tafe tana zancan zuci, tana shiga bedroom dinta, ta jawo wayarta ta kiran lmbr wani dr babbar dr ne me duba lafiar kwakwalwa,, ta kirashi kn yazo ya duba AB'ILAL sbda ita ganinta ma beda lafiya kwakwalwar ne..