Sashe 42
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
din yafi mace tsafta da kwaskwas...yana gama kimtsa dakin ya karaso inda gwaskan yaje, yayi masa tayin wanka ko ze karajin dadin jikinsa, banza AB'ILAL ya masa a zucia alhasan yace "uban yan izzah..." Yana gama fadar hkn ya fada bathroom yayi wanka, ya fito ya shirya cikin kananan kaya irin na yan hutu, sun amshi jikinsa Ainun. A hk dr kabeer ya shigo dakin hannunshi riqe da wata kyakyawar jaka me dauke da kyn aiyukansa, tinda ya shigo dakin idonshi ke kan AB'ILAL wanda idonsa ke bude, shima ya zuba masa ido kallo daya biyu ya dauke kwayar idonsa a kn dr kabeer din , karasowa yy cikin dakin bakinsa dauke da sallahma a karo na biyu, Alhasan ya amsa. "abokina har yayi baccin ya tashi ne?" Dr kabeer ya tambaya dai-dai yana karasowa bakin bed din da AB'ILAL ke kwance. Alhasan dake tsaye gaban dressing mirror ya gama fesa perfume kenan, ya karaso bakin bed din yana fadin "wlhy dr ko rintsawa beyi ba, yadda ka barshi hkn yake, shiyasa ma na kiraka Ai..." Dr kabeer ya zaro ido fuska dauke da mamaki yace "kana nufin beyi bacci ba? Dukda alluran dana masa?" Dr kabeer ya jefowa Alhasan tambayar, alhasan ya daga masa kai alamar tabbatarwa yace "Gashi nan wlhy ko rintsawa beyi ba..." Dr kabeer ya kara cika da mamaki ya ajiye jakar dake hannunsa a kasan dakin kana ya kara tambaya "ko kadan beyi bacci ba?" Ya karashe mgnr yana me kure AB'ILAL da kallo. Alhasan yace "Wallahi dr be rintsaba, ni kaina nayi mamaki ..." Dr kabeer yace "nima nayi mamaki, duk allurorin dana masa...."alhasan yace "Wallahi kuwa dr..." Dr kabeer yace "Yaci wani abu?" Alhasan yace "yasha tea kadan na bashi maganin dakace a bashi ..."dr yace "okay, bani maganin in gani..." Alhasan ya dauko magungunan ya nuna masa, ya dudduba kana ya karasa ya ajiye ledar mgnin a side drower din, ya karaso ya taba jikin AB'ILAL yana me tambayarsa ya jiki, uban yan izzar shiru ya masa, sam be tanka masa ba. Alhasan yace "Dr anyi masa gwaje gwajen jinin ne?'' Dr kabeer ya dago ya kalli Alhasan yace "Yeah anyi masa, result dinsa be numa komi ba,, BP dinsa dayayi low dinnan ne yasashi a wannan halin, kuma damuwa ce,..." Alhasan yayi shiru kawai yana kallon bakin dr, dr kabeer ya kara dudduba jikin AB'ILAL. zuwa lokacin drib din ya kare, dan hk ya cire masa. Ana cirewa ya miqe zumbur cikin dauria kmr ze fadi yakeji amma baka isa ka fahimci hkn ba sbda yanada matukar dauriya, alhasan ya karaso da niyar ya taimaka masa ya dakatar dashi, kawai ya fada bathroom. dr kabeer ya bishi da ido, kai dagani kasan izzar tasa bata banza bace domin kuwa nera ta zauna, gefe yaja ya zauna a gefen bed din, alhasan ya dawo ya zauna shima kawai yana murmushi, dr kabeer ya fara bashi shawara kan yadda zeyi ya temaki AB'ILAL wato yasan yadda zeyi dashi ya rage dmwar da yake ciki tin kafin azo level din da baze haifar masa da d'a me ido ba. Alhasan yace insha Allah kawai, amma a ranshi cewa yakeyi ai AB'ILAL halinshi se shi, ba wanda ya isa yasashi balle ya hanashi. Suna nan zaune suna tattaunawa a kan rashin lafiar AB'ILAL. Daga toilet AB'ILAL yayi kiran Alhasan, tashi yayi yaje bakin kofar toilet din, daga ciki AB'ILAL yace Alhasan ya bashi jallabiyarshi da boxes guda biyu a cikin kynsa. Alhasan yace okay ya juya ya dauki car key dinsa ya fice a dakin , compound din gidan ya fito, ya nufa motarshi daya fita da ita jiya, ya bude ya dauko kayayyakin AB'ILAL din dake motar, kana ya maida motar ya rufe ya dawo cikin gidan, koda ya dawo a falo ya samu dr kabeer ya zubawa tamfatsetsen tv ido, yasan dalilin barinsa dakin maybe danyaga AB'ILAL na wanka ne shiyasa ya bashi guri ya kimtsa, hakan ba karamin dadih ya masa ba. Alhasan ya idasa shiga bedroom din ya ajiye kayan hannunshi a Waldrop dinsa, ya dawo ya kakkabe Bed din, ya chanza bedsheet yasa wani me kyau, ya nufa toilet ya jefa bedsheet din daya cire a basket din ajiye masu datti. Alhasan yanada ma'aikata guda biyu dame girki dame masa share share duk maza ne, sunyi tafia ne, daman duk after 1year sukanje kauyukansu suyi kwanaki biyu uku hudu se su dawo to a wannan karonma sunyi tafiyar ne yana sa ran dawowarsu gobe. Jallabiya kalar ashe Alhasan ya fitowa da ab'ilal dashi, se boxes guda biyu kmr yadda ya umurceshi, se Dariar zuci alhasan yakeyi tinda AB'ILAL yace ya kawo masa boxes biyu yake dryr a zuciarsa, se a ynzu yake kara tabbatr da abnda ya fada gaskia ne, a cikin mgnrsa daya ne babu. "Abubuwa na cikin wanduna ana adanawa..." Alhasan ya fadi a ransa yau dabadan AB'ILAL beda lafia ba dayasha mgna a gun alhasan.. Karasawa bakin toilet din alhasan yayi ya sanar da AB'ILAL ya ajiye masa kyn a gefen bed, a karshe yace inka gama shiryawa muna falo.." Yana gama fadar hkn y juya ya bar dakin, duk AB'ILAL dake Bathroom din yana wanka, yana jiyosa amma be ce komi ba, a dazuma sbda dolene tasashi mgna a toilet...seda ya kwashe awa daya yana wankan kana ya fito kugunsa daure da bathrobe ya goggege jikinsa sam be bari ba ko alama na hango jarumar burarsa ba, se aikin kakkareta yakeyi, koda zesa boxes dinsa juya baya yayi ya saka abunsa, duka biyun ya dauki zumbuleliyar jallabiyarsa ya zumbula ba tare daya shafa cream ba, ya maida bathrobe din daya cire bathroom din. Ya dawo dakin yanajin wani irin ddh a jikinsa sbda wankan da yy, kashi ashirin na ciwon dake jikinsa ya ragu. Daman already yy alwalar sallarh azahar domin kuwa zuwa lokacin har an fara kiraye kirayen sallarh azahar din ne. A daddafe ya karasa ya dauki perfume din alhasan ya feshe jikinsa dashi seda ya sauke ajiyar zucia ya dauki counter din alhasan dake kan dressing, ya saka slifas duk abinda yakeyi jikinsa babu kwari ya fito falon. A falon AB'ILAL ya samu su Alhasan Da dr kabeer Zaune se hira sukeyi, suna ganinshi suka hau jero masa sannu, a wannan karon sunci saarh ya amsa cikin izza kai kace ma beso ne ya amsa, Ya juya ya fice a falon kawai ya nufa masallaci. Dr kabeer ya kalli alhasan yace "Ina zeje?'" Alhasan daya ankare da counter din dake hannun AB'ILAL yace "nasan be wuce masallaci zeje..." Dr kabeer ya jinjina kai yace "inbanda abnsa ai da a gida yayi sallarh sa, tinda beda lafia..." Alhasan yayi nurmushi yace "tab ai bana tunanin akwai ciwon daze hana AB'ILAL zuwa masallaci yabi sallah a jam'i.." Dr kabeer yayi murmushi hadi da mikewa yana fadin "Allah , cemin zakayi malam ne..." Alhasan yayi yar daria shima hadi da mikewa yace "Aah ustaz ne,," dr yayi murmushi, yace "muyi alwala muma muje masallacin..." Alhasan yace "gashima an kusa tada sallarh..." Yayi mgnr yana nufar badroom dinsa domin yin alwala. Dr kabeer ya shige toilet din falon. Ba jimawa duk suka fito suka nufa masallacin dai-dai ana qoqarin tayar da sallah azahar din...bayan sun idar da sallar a tare suka shigo gidan, AB'ILAL se laziminsa yakeyi, yanaji kansa na masa nauyi har zuwa wannan lokacin. Dr kabeer yace ze saka masa wani drib din, nanfa ya daka tsalle yace shi baza a saka masa ba, ya gaji a barshi ya samu sauki Ma kawai. dr kabeer yace "ina wani sauki, bakayi bacci ba.." A hasale Alhasan yace "bari in kira Alhaji babba, ni bazan iya ba gaskia, inyazo seya daukeka ya kaika asibiti ma kurum.." AB'ILAL dake kwance Kan bed din ya zubawa Alhasan ido, wadanda ke tsaye shida dr kabeer. ab'il ya gallarawa alhasan wata iriyar harara. alhasan ya masa gwalo, kana ya duba dr yace "dr sa masa drib Din plx..." Dr kabeer yace okay, da fargaba ya kai hannu, yana me tunanin ko AB'ILAL ze kara gaddana se kuma yaga ya tsayar da hannunshi, seda aka sake neman sabuwar jijiya sbda na dazu dayaje wanka ya tumbuke shegiya ya wurgar. Nan take dr ya mayar masa da drib din yasa msa wasu allurorin dayazo dasu nasa bacci masu karfi, da wata allura dazata zamar masa mazaunin abincin dabe ciba. Komawa yy ya kwanta byn drib din ya fara shigarsa, har ynzu tunaninta be bar ranshi ba..dr kabeer ya bawa alhasan wasu magungunan dayazo dasu, yace masa in drib din ya kusa karewa ya kirashi, yade zamana yana kusa dashi Alhasan yace okay. Dr kabeer ya masa sallahma ya fice gidan Alhasan se jero masa godia yakeyi. Shima ya fice a dakin ya nufa kiching ya hadowa knsa indomie sa dafaffen kwai, ya dawo dakin yayima ab'ilal tayi, ko kallo ma be isheshi ba, Murmushi yayi ya zauna yaci ya koshi ya kora da drink me sanyi, Ya kwashi plt din daya gama cin indomie din ya nufa kiching AB'ILAL ya bi bayansa da ido, da tunani tunani a ransa, duk na wannan kyajyawar yarinyar ne. Ba jimawa alhasan ya dawo dakin, zuwa lokacin AB'ILAL ya fara lumshe ido sbda allurorin da aka masa a wannan karon manya manyan ne, alhasan ya dawo ya zauna gefen bed din, ya zuba masa ido, a hnkli bacci me nauyi yayi surar iska dashi. Alhasan ya zubawa kyakyawar fuskarsa ido a zuciarsa yace "AB'ILAL cases......." Ya saki wani shu'umin murmushi short one, ya raba gefensa ya kwanta domin bacci ne a idonsa har na innalillahi sbda jiyannan be rintsaba.