Sashe 49
Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji murtala ya kira AB'ILAL ya sanar dashi hajiya maryam tace zata dawo kd ta hanyar trnsper da akayi mata, nan sukayi mgnr gida AB'ILAL yace ai gida ba damuwa bane sunada gida,...daga hk sukayi sallahma AB'ILAL se murmushi yakeyi karkaso ka bincika kasan zuciarsa data ke fara sol. Ba bata lokaci ya shaidawa alhasan, shima nan ya hau murna da farin ciki, a ranar suka fita sukaje gidan da Amihh zata zauna wanda ke malali GRA gidane dankarere na gani na fa ko gidan shugaban kasa se haka...ranar aka nemo ma'aikatan dazasu karasa aiyukan gidan dmn ba wani aiki bane na azo a gani AB'ILAL da Alhasan suka sakarwa ma'aikatan kudi iya kudi, aiko jiki na rawa suka hau aiki ba kama hannun yaro.... A satin aka hada komi na buqatuwa a gidan aka kira ma'aikatan sanat Turkish suka tsara komi yadda ya dace kama daga side din hajiya maryam da side din AB'ILAL se bangarori guda uku na saukar baki duk aka tsarasu tsaf an zuba dukiya iya dukiya saboda arzikin akwaishi bawai karyarshi akeyiba kudinne akwaisu Alhamdulillahi. Komi da ake bukata an zuba a kicking na bukatuwa stores din gidan duk aka cikesu da abinci iri iri kama daga abincin larabawa dana Indians dana hausawa dana turawa dade sauransu. Gida fa ya hadu iya haduwa tsarin yayi iya tsaruwa domin kuwa yafi gidan hajiya maryam na kano nesa ba kusa ba. A kano kam hajiya maryam se shirye shirye takeyi na dawowarta kd, sosai salwah taji ddh data samu lmrin Amihh zata dawo kd. Yan uwa dake nan kd ma suna cike da murnar dawowarta kd musammanma hajiya karama wato autar su ALHAJI MURTALA wadda salwah ke zaune gunta.... Motoci suka kwashi abubuwan da hajiya maryam zasu bukata wasu na amfaninsu da ma'aikatansu na nan suka fara yin gaba byn sun isa Nan suma suka kara kimtsa komi kowa se santin gidan sukeyi, Hajiya maryam kam taga picture din gidan a waya Alhaji Murtala ne ya turo mata ta WhatsApp ita knta ta yaba da kyaun gidan, sannan ya mata masha Allahu. Washe gari ita da hajiya Juwairriyya da Salwah suka biyo jirgi zuwa garin kaduna sukayima kano bye bye, da sunan duk weekend hajiya maryam zata rinka zuwa kano, sam hajiya maryam bataji dmwa ba kmr yadda tayi tsammani jin zuciarta takeyi wasai sema dumbin farin ciki dake dawainiya da ranta.... Lafia lau suka sauka a jirgin Alhaji murtala da iyalinsa wato bebynsa zee sukazo tarbarsu da motoci na alfarma, AB'ILAL kam be yadda ma yazo ba sbda tsaro. Suka shiga motoci suka nufa malali GRA kowannensu zucia zallar farin ciki , dasuka isa gidan nan suka tadda su hajiya karama da gudu salwah taje ta rungumeta zucia cike da farin ciki hadi da kewarta... Nan fa aka hau farin ciki aka gaggaisa, kana daga bisani suka huta sukaci abincin da hajiya karama ta shirya musu sukaci suka koshi suka gabatar da sallarh azahar da la'asar kana suka shiga aikin zagaye gidan kowa seda yayi santin gidan hadda alhaji babba dske kara ganin gidan ynzu, domin tin kafin a zuba furnitures AB'ILAL ya kawosa ya gani, Hajiya Juwairriyya kam se fadi takeyi gida yayi masha Allah an narka dukiya! Murmushi kawai maryam keyi hk kawai takejin knta a nishadi, se godia takewa alhaji murtala a tunaninta Aikin nasa ne. Matan alhaji murtala duk sunzo da yayanshi nan duk suka wuni se dare suka koma gidajensu wasu kuma nan suka kwana ciki hadda zee da hajiya salamatu mace ta uku ga Alhaji babba, Hajiya karama ma nan Ta kwana. rnr kwana akayi ana hirar zumunci.... Washe gari aka watse gida ya rage daga hajiya Maryam se Juwairriyya se ma'aikatan gidan salwah kam tini tabi hajiya karama zuwa gidanta dmn dukta kagu jinta takeyi kamar a qaya take. Rnr ne aka tara malamai aka kara saukar alqur'ani a gidan, hajiya maryam tasaka aka nemosu , domin batasan cewa AB'ILAL yasa anyi saukr alqur'ani ba a gidan. Tare da hajiya maryam da hajiya Juwairriyya akayi saukar, bayan an gama ta musu sha tara ta arziki suka bar gidan zucia fal jin ddh..... Washe garin ranar Ab'ilal da alhasan sukazo gidan, a falo suka samesu zazzaune suna hutawa ac na ratsasu hajiya maryam kallo daya tama AB'ILAL taga tsantsar ramar da yayi dan haka bata bi ta knsaba Amma so tayi ta koresa. Sugunnawa sukayi a kasa suka gaidasu Hajiya Juwairriyya ce ta iya amsawa hadi da tambayarsu lafiarsu suka amsa da lafia lau..hajiya maryam kam shiru tayi, AB'ILAL ya matso daf da kafafuwanta yayin datake gishin gide a kn kujerar 2ct ita kuma Juwairriyya tana kn 3ct kowacccensu da kyn marmari a gabanta. Ido AB'ILAL ya zubawa mahaifiyar tasa wadda ta hade girar sama da kasa babu alamar annuri a kan fuskarta. "Hajiya Amiih , barka da hutawa?''cewar AB'ILAL hajiya maryam ta masa bnza, nan ya shiga aikin mammatsa mata kafafuwa hajiya Juwairriyya da Alhasan suka zubo musu ido ba karamin burge juwairiyya AB'ILAL keyi ba. Ganin ta masa bnza yasashi ci gaba da mgna. "Allah de yasa kin dawo kd a sa'arh Amiih ki rabu da yaran kawaye...." Karashen mgnr tasa se taso bawa Juwairriyya drya alhasan kam seda ya murmusa hajiya Juwairriyya kuma hadiye dariyarta tayi. Hajiya maryam kam kin tanka masa tayi amma ina be daddaraba yaci gaba da mgna yana mata tausa har zuwa hannayenta "Amihh To wai ya mgnr mgnin karfin mazan nan dazaki nemo min, kafin de kimin Auren daza kiyimin , kinsan kwanaki na gaya miki nifa ba Aurene bnsoba lafia ce bndashi..." Duk ilahirin halittar dake falon seda kunya ta rufesu musammanma hajiya maryam ji tayi kmr kasa ta bude ta shige don tsabar kunya, ta saki baki kawai. AB'ILAL be daddaraba ya bude baki da niyar ze kara mgna A hasale Amiih ta tashi zaune ta taso masa da tsiya "Inka kuma mgna a falon nan kaf shanayen dangin ubanka se na hadasu nashi k'asusuwan bura ubasu kaji na gaya maka....tinda kai baka data ido..mara tarbia kawai..." Shiru AB'ILAL yayi hadi da kame baki kamar karamin yaro. Hajiya Juwairriyya da Alhasan suka zubo musu ido ba karamin burge juwairiyya AB'ILAL keyi ba rashin jinsa na burgeta tin yana yaro taso da tanada diya mace ta hadasu da duk iskncin nan nasa zata jure. "Auwal hubb de an dawo kd to Allah yasa alheri nan de ba ruwanki da kwashe kwashen yaran kawaye ki mannamin..." Be daddaraba seda yaci gaba da magaba. Takaici ya kara rufe zuciar Hajiya maryam ji tayi kmr ta dokesa shi de ya rantse da ALLAH ko zagin ne seta kutuntuma masa ko zeji ddh. "Tashi ka fitarmin a falo dan sitirar dangin ubanka , tashi ka fice min a falona kaji na gaya maka.... In har bazaka natsu ba karka kara shigomin gidana kaji na gaya maka...wannan bakin naka mara tsarki ka saisaitasa kanajina kou?" Qur AB'ILAL ya kureta da ido yadda kikasan badashi take mgna ba a hasale Amihh ta zaburo zata kai masa hannu tana fadin "tashi nace ka fitarmin a falo..." Da hnzari ya tashi ya fice a falon still bakinsa be mutu ba. "To nifa yunwa nkeji Hubb, banci abnciba 2days..." Ya fadi hkn dai-dai yaka bakin kofar fita daga falon. Hajiya Maryam tace "ka mutu dan ubanka!" A hasale tayi mgnr murmushi AB'ILAL yayi yace ''bazan mutu ba sena cika miki burinki nason inyi Aure hadda jikoki zan haifa miki, masu kama da ke Amihh..." Takaici ya kara rufeta kawai tayi kasa da knta tana jinsa ya fice a falon , alhasan ya mike shima ya mara masa baya. Hajiya Juwairriyya ta kwashe da Dariyarta dataketa adanawa hadda riqe ciki tace "kai! Muhammad cases ne to ina mgnin da kika amso masan na lafiyar maza...." Juwairriyya tayi mgnr murya cike da zolaya. Fuska dauke da takaici hajiya maryam ta dago ta kalli Juwairriyya wadda keta faman daria tace "Wallahi Allah bamuyi hk da yaronnan ba, kawai tsabar sharri ne, ni Hajiya ke kin sani ta ina zance zan Amso masa mgnin maza..wlhy yaronnan ya rainani hajiya!'' Hajiya Juwairriyya ta kara tintsirewa da dariya tace "Ba raini bane hajiya maryam shi nature dinsa ne hk..." Takaici ya kara rufe hajiya maryam tace "wai se anyi mgna kice nature nature, kenan haka yake beda kunya...'' Juwairriyya dake dariya tace "ba haka nake nufi ba ni fa hajiya ..." Tabe baki hajiya maryam tayi tace "to ALLAH ya shirya...." Juwairriyya daketa dariya har zuwa lokacin ta amsa da Ameen.
AB'ILAL na fita direct side dinsa ya nufa , alhasan na biye dashi a baya har suka iso cikin kayataccen falon nasa Alhasan be bar Dariaba kasa kasa . falon ya hadu iya haduwa har ma ya gaji da haduwar komi a falon golden and milk ne . A falon suka yada zango a kan tamfatsa tamfatsa din kujerun dake falon Se sanyin AC dake a kunne koda yaushe ke ratsasu kai kace dakasa kafa a falon zaka taka kasan ruwah ne sbda tsabar sanyi. "Mamman na ta'alah Ya kamata muje a dauko motarka dake hotel dinnan fa...'' Cewar Alhasan dake zaune kn 1ct gogan kuma yana zaune kan 2ct yana sauraron me Alhasan ke cewa mikewa yayi tsaye hadi da cewa "tashi muje plx danni gobe zan bar garinnan ..." Alhasan ya tashi a tare suka fice a falon, suka hau motar Alhasan din, suka nufa gidan Alhasan din suka dauki car key din AB'ILAL dake hotel din kana suka hau hanyar zuwa hotel din. Nan fa suka tadda uban holdup ko motsi bayayi .... Duk suna cikinsa har akayi sallarh
magrib ma duk basu fita a holdup dinba wanda suka shigeshi tin 5:30pm takaici da bakim ciki ya cika zuciyoyonsu musammanma AB'ILAL se uban tsuki yakeja kai kace tsaka ya hadiya. Alhasan ya sauke motar tasu a kn titin ya shiga bi ta layi ta yadda zasu isa da wuri. "Da kasan da wannan layin shine ka barmu a wancan tsinannan holdup din..." Cewar AB'ILAL alhasan yayi bnza dashi yana me cigaba da duba area din sbda hnyar bata da kyau sosai wahalar tuki sbda ba kwalta, se kacau kacau yaketa cin karo dashi.
AB'ILAL na fita direct side dinsa ya nufa , alhasan na biye dashi a baya har suka iso cikin kayataccen falon nasa Alhasan be bar Dariaba kasa kasa . falon ya hadu iya haduwa har ma ya gaji da haduwar komi a falon golden and milk ne . A falon suka yada zango a kan tamfatsa tamfatsa din kujerun dake falon Se sanyin AC dake a kunne koda yaushe ke ratsasu kai kace dakasa kafa a falon zaka taka kasan ruwah ne sbda tsabar sanyi. "Mamman na ta'alah Ya kamata muje a dauko motarka dake hotel dinnan fa...'' Cewar Alhasan dake zaune kn 1ct gogan kuma yana zaune kan 2ct yana sauraron me Alhasan ke cewa mikewa yayi tsaye hadi da cewa "tashi muje plx danni gobe zan bar garinnan ..." Alhasan ya tashi a tare suka fice a falon, suka hau motar Alhasan din, suka nufa gidan Alhasan din suka dauki car key din AB'ILAL dake hotel din kana suka hau hanyar zuwa hotel din. Nan fa suka tadda uban holdup ko motsi bayayi .... Duk suna cikinsa har akayi sallarh
magrib ma duk basu fita a holdup dinba wanda suka shigeshi tin 5:30pm takaici da bakim ciki ya cika zuciyoyonsu musammanma AB'ILAL se uban tsuki yakeja kai kace tsaka ya hadiya. Alhasan ya sauke motar tasu a kn titin ya shiga bi ta layi ta yadda zasu isa da wuri. "Da kasan da wannan layin shine ka barmu a wancan tsinannan holdup din..." Cewar AB'ILAL alhasan yayi bnza dashi yana me cigaba da duba area din sbda hnyar bata da kyau sosai wahalar tuki sbda ba kwalta, se kacau kacau yaketa cin karo dashi.