← Book details Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 225

Sashe 7

Yar Dandi Ceh Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Kankana ya bisu da gwalo. Dai-dai suka karaso bakin kofar dakin hilwah me lamba chasa'in da tara, hadin sigah yayiwa dakin key Ya bude ma hilwah handle din dakin ta shige a matukar gajiye ya biyota a baya, babu abinda ke tashi a dakin nata se kamshin turare me sanyaya zucia,. daki ne me dauke da gado six by six ne Wanda yaji lumtsetsiyar katifa an lailayesa da zanin gado kalar mint color me dauke da y'ay'aye wato throw pillows, se daga gaba kuma katotuwar teddy dinta ce me mugun kyau Kalar teddy din kalar peach ce se gabanta an mata ado da white inda aka rubuta HELLO da manyan baki, teddy din nada kyau ainun. Se drower din kaya na gadon me madubi sak kalar gadon kalar drower din babba ce drower din tanada kofofi guda hudu ko wacce kofa akwai madubi a jiki, fuskar gadon peach ne hk akayima drower ado da peach color, sosai tsarin bed da drower din sukayi kyau, komi na tarkacen gadon akwai kama daga kan mirrow, abin sagale bags, gun ajiye takalmi, dade sauransu, dakin nada dan girma ba lefi. Sannan akwai wata doguwar gujera irin ta kwanciyarnan ta hutawa itama kalar peach ce kmr de yadda kalar peach din saitin gadon yake hk kalar kujerar take itama tayi kyau ainun, se canter table shima duk na gadon ne, akwai tamfatsetsen TV a manne a bangon yamma a dakin. tako ina ka wulga idanuwanka picture din wata kyakyawar mace zaka gani, wadda a kalla bazata wuce 35yrs ba a side drower din gadonma pictute din matar nan ne, wadda kamanminta daya dana Hilwah sede Hilwah ta fita dara-daran idanuwa marabarsu kenan amma kamaninsu daya, duk picture din matar babu dankwali sumar knta ta kwanto ta rufe kirjinta, matar tafimin kamannin da larabawa ko ince indians sam babu alamar nigeria a tattare da ita, kama daga kayan jikinta zuwa yanayin launin fatarta, matar nada matukar Kyau Na ban mamaki, sannan tanada karamin jiki kmr de irin jikin hilwah,dan zakayi tsammanin matar bata wuce 30yrs ba nanko 35yrs take. Karasawa ga Ac din dakin kankana yayi ya kunnashi, kana ya dawo ya zauna kan kujera yana sauke ajiyar zucia idonsa na kan hilwah wadda ke aikin warware mayafin dake kanta nan da nan uwar uban suman dake knta ta bayyaba ta gangaro har zuwa duwawunta, cikin hanzari kankana ya taso ya dauko abinda take riqe gashinta dashi ya nade mata sumar ya riqe mata da abinda take riqe gashin nata dashi, sam bata iya nade gashin nata sede wani ya nade mata saboda yawansa, bayan ya gama nade mata gashin ya kame can cikin kanta ta masa godia ya zuba ma halitattarta ido kmr yau ya saba ganinta, juyawa tayi ta kalli tamfatsetsen watch din dakin inda ya buga 1:42pm. Karasawa tayi kan kujerar inda kankana ya koma ya zauna ta dauki ledar maganin ta fito dashi ta balli guda biyu ta afa a baki kankana ya dauko mata bottle water a madaidaicin frij din dake dakin ya bude ya bata ta amsa ta kora mgnin da ruwa, seda ta sha rabi kana ta mikawa kankana gorar ruwan, ya amsa ya rufe idonsa na kanta. juyawa tayi ta fada bathroom dinta dake dakin, kankana yabi tamfatsa tamfatsa din duwawukanta da kallo, seda ya hadiye wani irin miyau me cike da sha'awarta, babu namiji me lafiyar daze kalli hilwah beji sha'awartaba, koda mara lafiyarma inada tabbacin in har ya kalli hilwah se yaji wani abu ya darsar masa a rai, saboda ta hada kayan dadin duniya, ba duk matan duniya keda shiba.
Chapter 7 · 0% Book details