← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 211

Sashe 99

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        A kwanaki ukun nan kullum sai Yoohan dake a birnin ikko yanzun sai ya kira Dr Aysha yaji yanayin jikin Nu'aymah da suka maida sumammiya, dan tunda ya bar kano a yanayin barci take, sai dai drip da ake ƙara mata a koda yaushe da allurai a ciki. Haka suke buƙata ta sami isashen hutu. Allurar kuma daya sa aka kawo masa daga canada tun wadda akai mata randa aka kawo ba'a sakeba. Dan ƙa'idar allurar sai bayan sati ɗaɗɗaya za'ayita, hakan yasa bai bama kowa ba ya ajiyeta a office ɗinsa a waje mafi sirri. Dan daga Lagos nan kano yake fatan dawowa ya duba Nu'aymahn. Kamar yanda ya sabarma kansa kuma kullum sai ya kira baba malam sun gaisa safe da maraice.

       A gidan su Nu'aymah kuwa shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dan yau saura kwanaki shida kacal a ɗaura auren su Hajarah. Da Abban su Adawiya yace a ɗaga har sai Nu'aymah ta samu sauƙi. Amma sai baba malam ya hana hakan. Ya ce babu abinda za'a fasa ALLAH zai bata lafiya itama.
         Yayinda aketa shirin biki Abdallah da Naser ƴar tsama a tsakaninsu kullum sake faɗi da tsauri takeyi akan Nu'aymah. Gashi sun maida asibiti wajen yininsu duk da ita wadda sukeyi domintama batasan sunayi ba ma. Duk sunbi sun tashi hankulansu akanta. Yayinda Adawiya ita nata hankalin yafi nasu tashi. Dan har yanzu Abdallah yaƙi maida auren nasu. Su baba malam kuma babu wanda ya sake cewa da shi komai akan hakan.
      Sosai Adawiya ta rame, kamar ba itace suka dawo ta zama lukuceciya ba. Tabi ta ɓoye kanta a gidan babu mai ganinta sai ƴan sashensu. Ita kuma Addah tayi kamar bama tasan halin da Adawiya ke a ciki ba. Dan tun lallashin datai mata na farko taki saurarenta saita watsar da ita bayan ta babbanka mata zagi da yi mata kaca-kaca.
       Ƴan uwantane kawai da Umm ke tausayinta, dan Hajarah tamafi kowa damuwa da halin da Adawiya ta jefa kanta. Har kwatance take mata da yanda Yusrah tai kamar komai bai dametaba tanata harkokinta ita. Hakama Nu'aymah lokacin da aka rabasu aka bashi aurensu. Amma sam Adawiya taƙi fahimta. Sai bin hanyoyin da zatai magana da Abdallah takeyi shi kuma ya toshesu ya hanata kowacce dama. Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ga takarar neman yardar Nu'aymah da take a rabin duniya da barzahu.

       A washe garin da Yoohan ya cika kwanaki huɗu da tafiya su Papa sukazo kano shida ƙannensa da abokansa uku. Babu wanda yasan abinda ya kawosu. Shi kuma baba malam bai faɗama kowa ba sai ƴan uwansa da Hajjo da Ananah kawai.
     Amma yanda Papa da gayyarsa suka koma ransu a ɓace zai baka tabbacin zaman baiyi daɗi ba. Dan shima baba malam ɗin dai ranar yini yayi babu walwala tattare da shi.

★★★★

        Ana saura kwanaki huɗu ɗaurin auren su Kubrah Yoohan dake a birnin ikko har yanzu ya kira Dr Sa'ad ya sanar masa su tsagaita da yima Nu'aymah allurar barci haka nan, idan ta farfaɗo a kowanne lokaci a kirasa a sanar masa.
      Haka kuwa akayi, ƙarfe kusan sha biyu na daren rar Nu'aymah ta farfaɗo............✍

_________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 42

.............Wani irin zabura Yah Ab yayi tamkar wanda yay gamo da mala'ikin mutuwa. A tsananin razane yace, “Nu'aymah kina nufin Naseer?!!”.
        Fashewa tai da wani sabon kukan tana jijjiga masa kanta. “Yah Ab kayi haƙuri, yanzu shine ya fi cancanta da hakan a gareni, kai ma dan ALLAH ina roƙonka ka maida matanka. Dan ALLAH ka kare mutuncin danginmu, karka bari wannan ya zama sanadin rusa zuminci ko saka ƙiyayya a tsakaninmu. Kayimin afuwa mu rungumi ƙaddara, UBANGIJI ya fimu sanin hikimar dake a cikin hakan. Dan........”
        Da sauri ya ɗaga mata hannu jikinsa na wani irin tsuma na yunƙurowar zuciyar tasu ta gado. Ya duba iyayensu da duk sukai tsit suna kallonsu tamkar babu su a cikin falon. Sai kuma ya duba Naser dake ta zuba murmushi idanunsa a lumshe bakinsa na motsawa alamar addu'oin godiya ga UBANGIJI yake jerawa. Batare da yace komai ba ya juya zai fice.
         “Abdallah!”.
Baba malam ya kirashi cikin muryar rashin wasa.
     Cak ya tsaya, sai dai bai iya juyowa ba. Cikin bada umarni Hajjo tace, “Dawo ka zauna”. Hawayen da suka cika masa idanu ya share. Kafin ya juyo a hankali ya dawo inda yake da, ya sake zama batare da yayi magana ba.
           Kallon Nu'aymah dake kuka hajjo tayi. “Zainabu tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abdallah suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar ana gasa mata ita bisa garwashin wutar gasa balangu.

     ★★<>★★

  Tun wannan zama da akayi Nu'aymah bata sakeji daga bakin kowa ba a gidansu. Dan zuwa yamma ma gidan sai ya sake cika maƙil da baƙi dake ta sake ɓullowa ta kowanne irin kusurwa saboda walimar da za'a gabatar daga ƙarfe huɗu. Hakama su Yah Ab bata sake ganin kowa ba a cikinsu, harma iyayen nasu. Garama Abba Musbahu taji muryarsa bayan la'asar ɗin ya shigo suna magana dasu hajjo a falo.
          Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani Muhammad ƙaninta ke rairawa cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi. Lamo tai a kan gadon hajjo dan bata da sha'awar fita wajen walimar. Fitar tata zai iya fama mata ciwuka masu yawa da suka zame mata gyambo a zuciyarta. Hakan yasa ta zaɓi cigaba da zamanta tunda daga nanma tana iya jiyo komai da ake faɗa tamkar tana a wajen.
            A wajen walima kam bayan Muhammad ya gama karatu baba malam ya buɗe taro da addu'a ga amare da angwayensu dama al'umar musulmai gaba ɗaya. Daga nan aka fara abinda ya tara mutane.
       Duk yanda akaita ragargaza wa'azi mai ratsa jiki a kunnen Nu'aymah ne, duk ba itace amaryarba sai da ta taya su Aunty Hajarah hawaye. Lokacin sallar magrib nayi akaje akai salla aka sake dawowa. Sake ɗorawa da wasu nasihohin sauram manyan malamai abokan su baba malam sukayi. Daga haka akaci aka sha kowa yay haniƙan, aka kuma raba abubuwa kamar yanda suka saba duk lokacin aurar da yaransu ko yaran gidan marayunsu.

       Lokacin da aka tashi tuni Nu'aymah data koma sashensu tai barci a falon baba malam. Umm bata sani ba, dan tana can wajen taimakawa baƙin da zasu kwana a sashenta samun wajen kwana. Sai da baba malam ya shigo wajen sha biyu sannan ya ganta kwance a doguwar kujerar falonsa ta naɗe waje guda alamar sanyi takeji. Zama yay a kujerar gefen da kanta yake yana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar ɗiyar tasa mai tsananin kama da mahaifiyarta abar sonsa da ƙaunarsa. Ɗan murmushi yayi tare da shafa kumatunta sannan ya miƙe. Batare daya tadata ba ya cire babbar rigarsa ya lulluɓa mata. Yana jinta ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya ɗauka remote ɗin ac ya rage mata shi sosai sannan ya wuce bedroom ɗinsa cike da tausayinta.

*_JUMA'A_*

          Da asuba baba malam bai wuce massallaci ba sai da ya tada Nu'aymah. Bayan an idar da salla bai jimaba ya dawo dan yau basuyi zaman karatu ba daman. A falo ya iske Nu'aymah inda tai salla tana karatun Al-qur'ani. Zama yay kallonta da sauraren zazzaƙar muryarta da a yau take fita da sanyi matuƙa. Yayi kusan mintuna arba'in sannan Umm ta shigo falon da sallama. Tray ɗin hannunta ta ajiye a gabansa tana kallon Nu'aymahn da mamaki. dan ita dai bataga wucewarta ba. Kallon baba malam tai, ya sakar mata lallausan murmushi tare da maida idanun nasa shima kan Nu'aymah da batasan sunayi ba.
      Zama Umm tai a kusa da shi. Cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Yaushe tazo nan?”. Murmushin ya sakeyi kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ɗan sauke numfashi yana riƙo hanun Umm cikin nasa. Cikin wani irin yanayi yace, “Anan ta kwana. Nima na dawo wajen walima na sameta anan da alama bama taje wajen walimar ba”.
           Guntun numfashi Umm ta furzar, batare da tace komaiba ta zare hannunta cikin nasa. Shayin daya saba sha duk irin wannan lokacin ta shiga haɗa masa. Yayinda Nu'aymah keta karatunta batare da tasan mi sukeyi ba. Sai dai tana ɗan jin motsinsu kaɗan-kaɗan, dayake hankalinta baya a tare da sune yasa batajin mi suke faɗa.

        Duk hidimar da ake a gidan da sake cika da yake yi da baƙi Nu'aymah tana sashen baba malam taƙi fitowa. Yau tare da shi ma sukai breakfast. Sashen nasa ma itace ta gyara masa yau. Bayan yayi wanka ya fito ta shiga ta gyara masa bedroom ɗinsa tsaf, ta dawo falo inda yake zaune shida ƙannensa da huhunan goro dana alawa da aka shigo da su, magana suke ƙasa-ƙasa alamar tattauna wani abu mai muhimanci a garesu. Cike da girmamawa ta gaidasu, duk suka amsa mata da kulawa tare da tambayarta yaya ƙarfin jikinta.
     Har zata fice baba malam yace ta koma tai wankan a bathroom ɗinsa tunda mutane sunyi yawa a gidan. Daɗi taji sosai, dan haka ta juya cike da ɗoki ta koma bedroom ɗin baba malam ɗin.
Chapter 99 · 0% Book details