← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 211

Sashe 119

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

        Lafiya lau Nu'aymah tai barcinta a sashen ita kaɗai batare dajin ko ɗar ba na tsoro. Dan haka sam dama ba ɗabi'arta bace ba kowa ya sani. Abinda kawai yayta cimata rai shine kaɗaici da kewar ahalinta. Gashi bata da ko ƴar waya balle ta kirasu taji koda muryarsu. Sai damuwa akan waɗan nan mutanen gidan data fahimci sam babu mai ƙaunarta a cikinsu. Sai dai kowa da nasa salon kallon data lura yana mata. Yaran nan su Victoria ne kawai babu ruwansu, sai su maman Destiny. Amma har masu aikin gidan tana fahimtar kallon ƙyama da suke binta da shi duk da kuwa duk suna mata gaisuwa da girmamawa. Lallai kuwa dolene ta ɗaura ɗammarar zama mara jin magana, inba hakaba wahala zata sha tunda ta fahimci shi daya ajiyeta bamai zama bane. Yazama lallai kenan itace zataima kanta yaƙi da kanta basai ta jira daga wurinsa ba. Da waɗan nan tunane-tunanen tai barci a wannan daren, hakan yasa washe gari bata fita a sashen nata ba sai bayan sallar zuhur.
       Yau kam babu kowa a falon sai Abraham kawai yana kallon cartoon, yanda yaron bai tanka mata ba haka itama bata kulashi ba tai ficewarta. Kai tsaye garden ta nufa abinta. Shiru wajen babu komai sai kukan tsuntsaye da iska mai daɗi dake kaɗawa. Ta zauna a bakin pool ɗin tare da zira ƙafafunta ciki tana lumshe idanu saboda sanyin ruwan. Haka ta zauna tsahon lokaci a wajen rabin hankalinta duk yana ga tunani, kamar ance ta waiga sai idanunta caraf akan Gebrail da ita kanta batasan adadin lokacin daya ɗauka a wajenba. Kanta ta ɗauke daga dubansa tana sake tsuke fuska. Yayinda shi kuma ya shiga takowa inda take yana wani rangaji irin na gayu marasa jin magana. A mamakinta sai kawai ganinsa tai ya zauna daf da ita shima ya zura ƙafafunsa cikin ruwan.
          Kallonsa tai da wani irin takaici, shiko ya saki murmushi. Kafin ya furta maganar dake bashinsa taja baya ta fidda ƙafafunta tana jan wani shegen tsaki........ Da sauri yace, “Ayya sorry my aunty, i......”
      Wani shegen kallon da tai masa ne ya sakashi haɗiye abinda ke bakinsa. Ta zira takalmanta ta fice daga garden ɗin gaba ɗaya. Ta kula yaron nan yana son shigar mata hanci, to lallai zata fyatoshi kuwa da gaggawa tunda shi ɗan bunsuru ne.
      Gebrail kam da kallo ya bita a wani irin yanayi yana lashe laɓɓansa, harga ALLAH tun ganin Aymah a wajen dinner ya rikice, dan yarinyar da shekarunsa ta dace bawai yayansa ba.

         Takaicin da take ciki na Gebrail yasata ko ganin hanya batayi take tafiya kawai ta bayan garden ɗin. Dan jitai sam batama buƙatar shiga cikin gidan balle ta sake karo da wani takaicin kuma. Cak ta tsaya saboda jin ana magana ƙasa-ƙasa kamar cikin tashin hankali. Tai saurin komawa baya kaɗan ta maƙe jikin rassan flowers ɗin da suka sarƙe wayar garden ɗin. Ƙafafunsu kawai take gani banda fuska saboda karewa da bishiyan ayaba tayi, saboda da turanci suke haɗawa a maganar ya bata damar jin wani abu a ciki.
     Wanda ke maganar yace, “Boss! Nima ganin hoton nan ya matuƙar tadamin hankali, dan bamu saniba koma bashi kaɗai baneba, tunda wannan ma a tsakkiyar file ɗin nan na companyn na samesa”. Cikin tsananin tashin hankali taji wanda aka kira boss ɗin ya fara magana da yare, kafin ya kuma dawo yi da turanci kamar zai haɗiye harshensa. “Tabbas akwai damuwa idan hoton nan ya shiga idon wani, dan zai iya zama silar buɗewar ɓoyayyen sirrina da babu wani mahaluki daya sanshi bayan mutum huɗu, suma ɗin ba komai suka saniba akai sai abinda na sanar musu. SB kayi gaggawar ɓatar da hoton nan, sannan dolene a cikin watannan mubi kaf takardun nan mu bincikesu dama gidan gaba ɗaya, sai mun tabbatar da babu wani makamancin irin wannan hoton sannan hankalina zai kwanta, zan shigo Lagos ɗin nima amma bari sai tafiya mai tsaho ta sam....”. Sai kuma ya sake komawa yin maganar da yare wancan na amsa masa.
       Gani tai ɗaya na takowa alamar zai fito. Tai azamar sake maƙewa a wajen dan taɗau alwashin sai taga kosu ɗin su wanene?.
       Har yayo nisa taji wancan ya tsaidashi, da turanci yace, “Kaga bani hoton nan kar a sami kuskure, zan ƙonashi ni da kaina kawai”. Batare da wancan ɗin yayi musu ba ya miƙa masa yana faɗin, “Okay sir”. Daga haka ya juyo zai fita.
       Da kallo Aymah ta bisa harya ɓacema idanunta, bata sanshiba, dan babushi a cikin duk waɗanda aka nuna mata a cikin gidan. Jin ana takowa za'a fito ya sata sake komawa da sauri ta maƙe. Wani irin waro idanu tayi ganin Papa ne ya fito. Ta bisa da kallo zuciyarta na wani irin motsi a ƙirjinta. Sai da ta hangi ya shige cikin falon gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito a wajen zuciyarta na mamakin wane sirrine yake iƙirarin babu wani mahalukin daya sani sai mutane huɗu?. Miyasa yace sanin zai iya zama sanadin buɗewar sirrinsa? ‘Sirrin mi to?’ ta ayyana a fili cikin jimami.
     Wata zuciyace tace, ‘Ke ko Aymah ina ruwanki, ko shishshigi da son asani. Hakane fa’. ta sakke ayyanawa a ranta tana barin wajen. Daga nan ma sai ta koma cikin gidan itama.

      Kamar wasa sai ga tattaunawar papa da baƙonsa ta kasa barin ranta. Duk yanda taso yakicewa abin sai sake tisa kansa yake a zuciyarta. Haka kawai takejin ƙwaɗayin son ganin hoton nan. Sai dai idan tacema zata gani a ina zata gansan? Tunda yace ƙonawa zaiyi. Koma bai ƙonaba tayaya zata iya shiga ɗakinsa binciken hoto?.
       Waɗan nan tambayoyi sunta mata kaikawo a zuciya har lokacin Yoohan ya shigo gidan bata sani ba.
Chapter 119 · 0% Book details