← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 211

Sashe 6

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

          Ɓangaren Momy mahaifiyar Abdallah suka fara shiga tace rabonta da Nu'aymah tun a wajen Walima, amma bara a duba kotazo ta shiga ɗakin su Amal bata saniba. Sun duba ɗakinsu Amal babu kowa sai ƙannen Amal ɗin biyu dake barci. Sauran ɗakunan kuma duk akwai baƙi da wahala ace ta shiga can, amma duk da haka sai da suka shishshiga suma. Amma babu ko mai alamarta.
     Sun koma sashen Abba Musbahu nanma dai matarsa Ammi da Ummah sunce basuga Nu'aymah ba, an kuma shiga ɗakin su Yusrah da ƴammatan sashen yayun su Nu'aymahr nanma babu ita, sai su kaɗaine da sauran ƴammata sa'anninsu na gidan da baƙi. Sake dawowa sukai Sashen Addah aka duba ko ina nanma dai babu ita, suka koma sashen Hajjo nanma haka. Zuwa yanzu kam hankalin kowa ya fara tashi, dan ko sallar Asuba wasu sun kasa samun nutsuwar yinta.
      Duk da ba'a tunaninta a sashen samarin gidan haka dai aka shiga canma ko za'a dace. amma kuma bata nan. Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Nu'aymah bata gidan, samarin gidan dasu Baba malam duk sun dawo massallaci suma an haɗu anata taraddadi, sai sake tambayar su Yusrah da akasan suna tare akeyi da Adawiya data dage take rusar kuka tamkar ranta zai fita.
       Gari ya waye tangaran, waɗanda basuyi sallaba suka samu sukaje suka yiyyyi batare da hankalinsu na tare da suba. Umm kam tama kasa magana sai ajiyar zuciya da taje faman sauke a jajjere. Shi kansa Baba Malam binsu kawai yake da kallo. Hajjo tuni ta fara kuka itakam. Ango Abdallah kam nasa tashin hankalin ai ba'ama magana, danshi ya dage sai sake bin ɗakunan gidan yake lungu da saƙo yana dubawa.

       Kamar wasa saiga ƙarfe 11am ta buga babu Nu'aymah babu mai kama da ita, saima cin karo da akayi da takarda a jikin Windown ɗakinsu an ajiye. Sai kayanta ƙwara huɗu da alamu suka nuna jehosu akayi ta Windown maybe.
        Nanah ce taga takardan, dan haka ta nufi inda su Baba malam ke tsaye da sauran ƴan uwansa ta miƙa musu da faɗa musu inda ta gani. Abban Adawiya ne ya amsa takardan daga hannun Nanah, ya buɗe yana gyara tsayuwarsa. Duk idanu su Baba malam suka zuba masa da ƙaguwar sonjin minene a ciki.

        Assalamu alaikum iyayena.

                 Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wlhy yanzu bana son Yah Abdallah akwai wanda zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga yarda, amma wlhy ina masifar son Ameer fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku wajen ɗauramin aure da Yah Abdallah nazo kuma na zama sanadin ɓata zuminci da aka gina tunkan samuwarmu daga baya, shiyyasa na zaɓi bin Ameer mu gudu, shi kuma ku aura masa wata a cikin ƴan uwana. Na muku alƙawarin idan komai ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Ameer. Ina fatan bazakuyi fushi dani ba dan ALLAH 🙏🏻😭.
           Na barku lafiya.
Daga ɗiyarku Zainab Sooraj Hashim (Nu'aymah).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

        Tsit wajen yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Baba malam sai faman kaɗa kai yake kawai zuciyarsa na kaikawo.
      Hajjo ce ta ƙaraso wajen ganinsu cirko-cirko. “Lafiya? Na ganku cirko-cirko? Ko anji labarin inda take ne?”.
       Duk kasa bata amsa sukayi, hakan yasa ranta ɓaci ta daka musu tsawa. “Wai kuna cikin hankalinku kuwa? Ina magana kunmin shiru kai ɗan Malam” ta ƙare maganar idonta akan Baba Malam (Abban Nu'aymah) dan bata faɗar sunansa saboda shine na fari, sai dai tace ɗan Malam.
       “Kiyi haƙuri Innah, da kanta ta gudu”. “Ban gane da kanta ta gudu ba? Kana haukane?”. Kasa amsa mata yayi, dan shi kaɗai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki a halin yanzun.
      Abba Musbahu ne yace, “Innah inaga muje ciki, wannan ba maganar nan baceba”.  Zata sake magana ya kama hannunta suka nufi sashenta tacan baya inda falon mahaifinsu yake. Bin bayansu su Abban Abdallah sukayi, Baba Malam dai bai iya motsawa ba har tsahon wasu mintuna kafin ya bisu.

           Bayan haɗuwar duk wanda ya kamata a falon, Abba Musbahu ya sake maimaita abinda ke a rubuce a takarda, wadda Nu'aymah ta ajiye kamar yanda kowa yaji.
        “Kai wannan zancen ban yarda da shiba, ina Zainabu taga wayon wani yin wannan iya shegen? Wanene ma Amiru yake ko uwarwa? Tunda muke a gidan nan waya taɓa ganin Zainabu da saurayi ma?”. Hajjo tai magana ranta a ɓace.
      Shiru falon yayi, dan kowa yasan maganar Hajjo gaskiyace, babu wanda zaice ya taɓa ganin Nu'aymah da saurayi bayan Abdallah, dan Nu'aymah yarinyace mai shegen tsiwa da rashin tsoro, ko cewa akai ana sonta kai tsaye take faɗin an mata miji a gidansu. Bama ta yarda saurayi yay zuwa biyu wajenta........
      “Ina magana kowa yayi shiru, wlhy ni dai ban yardaba, sai dai idan wani munafukine ya sacemin jikata”. Hajjo ta faɗa tana fashewa da kuka.
       Baba Malam ne ya kalli Hajjon zuciyarsa na masa zogi, yace, “Innah karki saurin kareta, kinsanfa yaran yanzun ka haifesune amma baka haifi halinsu ba, mudai fara bincikar ƴan uwanta ƙila wani acikinsu yasan Ameer ɗin”.
       Girgiza kai Abdallah yayi shima cike da damuwa, “Baba ALLAH koni ban yarda wannan takardar Nu'aymah ce ta rubutata ba, mu dai bincika gaskiya”.
         Baba Malam yace, “Abdallah batun ba ita ta rubutaba kam bazai yuwuba, dan wannan rubutun natane, kuma da bakinta a jiya da daddare ta samemu da batun ita a fasa wannan aure ta fasa, bayan mun lallasheta ni da mahaifiyarta ta tafi sai gashi ta sake dawowa daga baya, sannan muna tare da Rudwan, sai dai nasan ganina tare da shi yasa batace komaiba ta gaidasa ta fita. Kaga kenan a lokacin ta silale tabar gidan?”.
          Addah tai saurin faɗin, “A'a dan ALLAH Yaya karmu yanke hukunci, mudai bincika ɗin ta bakin Abdallah”.
      “Humm” kawai Baba malam ya faɗa zuciyarsa na ƙuna, dukda shima dai wani gefe na zuciyarsa nata masa wasiwasi akan al'amarin.

        Yaran gidan duk aka tattaro, sa'anninta su Amal da yayunsu mata harma da ƙannensu mazan da matan. Ɗaya bayan ɗaya aka tambayesu ko sunsan Nu'aymah nada wani saurayi?.
       Mafi yawancinsu sunce basu saniba, sai ƙalilan da sukace sun taɓa ganinta kusan sau huɗu da wani saurayi baƙi. Sai dai takance Yah Abdallah ne yake aikosa wajenta.
     Da mamaki Abdallah yace, “Ni kuma? Kai gaskiya a'a. Wlhy tunda nake ban taɓa aiko wani wajen Nu'aymah ba sai Ahmad kawai, gashi nan kuma zaune tare damu. danni ko abokaina da yawansu basusan Nu'aymah a ido ba”.
      Sosai abin ya sake ɗaure kan kowa a wajen. Adawiya dake sharɓar kuka tace, “Tabbas akwai wani Ameer dake zuwa wajenta, amma acewarsa shiɗin abokin Yah Ab ne, kuma ko jiyama ai yazo wajen walima”.
     Duk kallonta sukai. Abdallah yay saurin faɗin, “Wlhy kamar yanda na faɗa ban taɓa aiko kowa wajen Nu'aymah ba, amma k Adawiya zaki iya ganesa ne?”.
       Kanta ta ɗaga musu tana sheshshekar kuka.
Chapter 6 · 0% Book details