Sashe 86
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A rikice baba malam da Umm da barci ya fara ɗauka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ƙarar Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ƙwalwar kansu.
Kwance suka isketa a ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ɗakin mai haske, Umm kuma ta nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.
Baba malam daya nufosu shima a rikice yay sauri ja da baya jin ƙafarsa cikin wani abu mai ɗumi. Kallon inda ya taka ɗin yayi. gabansa yay bala'in faɗuwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya durƙusa da kai ɗan yatsansa ɗaya yaɗan dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka yace, “Jini kuma?”.
Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace, “Jini kuma malam? A ina?”.
Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk sun shigo sai dai sun dakata a a falo.
Hankalin kowa ya tashi da ganin wannan jini. Ga dare ya fara.
Hajjo tace, “Mafita ya kamata mu nema ba wai koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti”.
Addah data maida Nu'aymah jikinta ta share hawayen da ke ziraro mata itama da faɗin, “Hajjo inaga a kira Doctor Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali”.
Dukansu sunyi na'am da zancenta. hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa mike faruwa?.
A taƙaice ya basu amsa yana ƙoƙarin kai waya kunnensa.
Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ƙarami ne yaje ya shigo da shi, yay masa iso har ɗakin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ƙoƙarin saka abu ana kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba malam kuma sun koma da ga ƙofar ɗaki.
Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga. Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. Ƙoƙarin tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.
Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda domin ƙoƙarin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na riƙe da Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ƙarin ruwa bayan an samu ta farfaɗo. Fita yay ya basu waje dan su ƙarasa gyara mata jikinta.
Yana fitowa duk suka yo kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ƙoƙarina na ganin cikin bai dalwantaba amma hakan ya gagara, sai dai haƙuri”.
Ga ba ɗayansu wani irin kallon rashin fahimta suke masa. Cikin ƙarfin hali Hajjo tace, “Kai ɗan nan bamu fahimci zancenka ba. Miya haɗa Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai bana haihuwa ba?”.
Shima ɗin dai kallon mamakin yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, “Mama ina nufin ciki na haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?”.
Kallon juna suka shiga yi ƙirjin kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar harshe Umm tace, “Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?”.
“Ikon ALLAH! Hajiya wlhy ciki ne da ita ɗan sati shida ma kuwa”.
Umm zata sake magana baba malam da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da faɗin, “Doctor yanzu wane hali take ciki ita?”.
“Ah Alhmdllh malam, yanzu haka tama farfaɗo, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ƙarfin jikinta za'a kaita asibiti dan na sake dubata da ƙyau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ɓarin yazo mata da matsala kamar”.
“To shikenan, mungode sosai Doctor, ALLAH ya saka da alkairi”.
“Amen” Doctor Sale ya amsa saboda jin daɗin addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya tafi ya barsu da ruɗani.
Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ɗauka kaɗan-kaɗan ce ta ɗan zauna jin zata faɗi. Cikin ƙarfin hali Hajjo ta shiga ɗakin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun kammala kimtsata harma sun lulluɓa mata bargo, ga ƙarin ruwan da aka saka mata yana tafiya dai-dai.
“Kunga kuje ku kwanta dare na ƙara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su kwanta”.
Babu musu sukai mata sallama suka fita. Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.
Su Abban Adawiya ne kawai sukace Alhmdllh, amma babu wanda yay yunƙurin tafiyar sai da Baba malam yay magana. Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta miƙe da ƙyar. Ɗakin Nu'aymah suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ɗago tana kallonsu.
Saurin yin ƙasa da kai Umm tayi, dan sai yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ruɗanin bayanin Doctor Sale. Wani sashe yana gaskatawa wani sashe na ƙaryatawa. Hakama baba malam a matuƙar ruɗanin yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa yana buƙatar lokacin yin tunani akan hakan..........
Hajjo ce ta katsesu da faɗin, “Ban yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matuƙar tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?”.
Kan baba malam a ƙasa, muryarsa a matuƙar cinkushe da tashin hankali yace, “Inna bazamuyi saurin ƙin gaskatawaba, tunda kinga ai aikinsane hakan”.
“Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan ALLAH ya kaimu”.
Basu iya mata musu akan hakanba da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun.
WASHE GARI
Da safe Doctor Sale ya dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay alƙawari. A lokacin Hajjo ta gyara Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ɗakin ita kuma.
Ya dubata yanda ya kamata, ya kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sauƙaƙa al'amarin. Ita dai Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.
Ya bada magungunan da zatay amfani da su, da waɗanda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa. Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.
Baba malam baiso maida hankali akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ƙarfe goma na safen shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.
Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matuƙar tada musu hankali akan result ɗin shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.
Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ƙarfin halin masa godiya.
Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ɗauki Nu'aymah suje asibiti kawai, kuma na gwamnati take so.
Ɗari bisa ɗari su Abba Musbahu sun yarda da maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ɓarin cikin Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma a ƙasan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.
_____________________