← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 211

Sashe 36

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

................Sai da ya kammala ƙalular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.
     Da sauri Miracle ta ɗauki remote ta rage ƙarar television ɗin dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ƙarasa Miracle ta rigashi isa, yana ɗaura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ɗora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ɗago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ɗaya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta zaƙo-zaƙon faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.
          Ita da kujerar ya haɗa ya wancakalar gefe, kafin takai ƙasa ya bita da halbi, sai gata ƙasa wanwar. Ƙarar data firgita kowa a gidan ta ƙwalla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ɗaga hannu zai ƙwaɗa mata mari Gebrail ƙaninsa yay saurin riƙesa, fisgewa yay yayi ƙwallo da kujerar kusa da shi ta dining ɗin ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ƙofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ƙwala masa kira da turanci. “Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci”.
      Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana haɗa steps ɗin da bibbiyu. Kafin ta ƙarasa har ya tura ƙofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi “Yoohan! yi haƙuri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please”. Duk da yaransu take maganar, amma yaƙi buɗe mata. Shi tunima yabar jikin ƙofar harya shige bedroom ɗinsa.
        Zuciyarsa cike da matsanancin ƙunci ya faɗa saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ɗaya duniyar ta masa masifar ɗaci, yaja filo ya danne kansa da shi da ƙarfi.

      A falo kam Mom data sakko a ranta a ƙuntace ta ƙarasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin faɗa tace, “Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za'a gaza ganeki zaki kiyayesa ai”. Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ɗakinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ɓatama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ƴaƴanta.
          Kuka Mira ta sake ɓarkewa da shi iya ƙarfinta su Joy na lallashinta, da ƙyar suka iya ɗagata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa'anni ma da Gebrail ƙanin Yoohan ɗin.
      Da taimakon su Joy Miracle taje ɗakinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. “Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha faɗa miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ƙaramar ƙwaruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? Ƙilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ƙarayi dan baya ɗaukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye”. Yana gama faɗa ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa'arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ɗin. Hawayenta ta share tana danna ƙafarta data buge, da yarensu tace, “Joy wai miyasa Brother ɗinku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wulaƙancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ɓacin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma......” da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ƙofa ta nufa da sauri ta leƙa, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ɗin. Daf da ita ta zauna cikin magana raɗa-raɗa tace, “Ni kaina na daɗe inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wulaƙantaki a gidan nan amma basu taɓa nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har Mom ɗin”. Mira dake sauraren Joy kamar mai ɗaukar karatu tace, “Yayi kuɗi ne shiyyasa ai”. Kai Joy ta girgiza mata da faɗin, “Sam ba haka bane Mira, ki tuna tuntuni suke masa wannan gatan na fitar hankali, makaranta saida ya zaɓa ya darje mai mugun tsada a ƙasar waje, har sai da ya cika burinsa na zama babban likitan da yakema duniya aiki bama Najeriya kaɗaiba, amma kina gani ni da Gebrail a 9ja muka fara karatunmu, sai yanzune da shi yace zai fita damu sannanfa suka yarda”. “Hakane Joy. to ammafa kinsan Yoohan yanada bala'in ƙwaƙwalwa, dan sister Divine tace min sanda suna primary yafi kowa hazaƙa da ƙoƙari a ajinsu, yanzu za'a karanta masa yanzu zai ɗaukesa a kai. Ni yanda ya tsaya yay karatun ya birgeni, dan masu irin shegen kaifin ƙwaƙwalwar nan tasa basu da yawa a cikin mutane, zakiga kuma mafi yawansu sunfi yarda su zama mugaye fiye da mutanen kirki, balleshi daya tashi ɗan gata ma. Amma kigafa shi a ma tsarinsa baya shan komai har giya da ba komaiba, baya neman mata, abinda kawai ya sani a rayuwarsa shine aikinsa da Family ɗinsa. Gaskiya ina masifar son gayen nan Joy, komai nashi yana birgeni”.
        Dariya Joy tayi sosai, ta wani juya idanunta cike da yanga, “Ai bake kaɗaiba Mira, koni da yake Brother ɗina sonsa nakeyi, haka ƴammata da yawa suke haukacewa a kansa, shiko babu wacca ta ishesa koda kallo ma, Mom tace tunda suke da shi bai taɓa ce musu ga budurwarsa ba. Ke nifa da ƙanwa zata iya auren yayanta da Brother Yoohan zan aura fa”. Baki Mira ta taɓe cike da kishi ta ɗauke kanta batare data bama Joy amsaba.
     Joy data fahimci kishi Mira keyi saita kwashe da dariya ta miƙe, amma ita tasan har cikin ranta son Brother ɗinta take da gaske. Kuma harga ALLAH tana kishin ganinsa da wata mace har Mira ɗin, dan yau sosai taji daɗin mazgar da yayma Miracle.

🤣Joy kedai muguwace to.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
Chapter 36 · 0% Book details