← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 211

Sashe 178

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Washe gari suka tashi da farkawar madam Chioma. Sai dai tanata faman raki akan hannunta. Dan kuka ta dingayi kashirɓan kamar ƴar yaye. Papa kuwa dake nane da ita yana tayata da tattali.
      Yoohan kam Alhmdllh tun a daren ya farka. Ya kuma takurama Omar sai ya nema masa ticket ɗin wucewa U.S. duk lallashin da Omar ya dinga masa sam yaƙi saurarensa. Ya dage akan shifa sai ya bari ƙasar. Kuma bayason papa ya sani. dan duk da ya farka duk shigowar da papa yazoyi dubashi sai ya nuna bai farka ɗinba. Badan Umar yaso ba dole yaje ya nema masa ticket, sai dai bana zuwa U.S bane direct. Amma duk da hakan Yoohan yace ya yarda. Sannan yaje gidan ya haɗoma Yoohan ɗin kayansa na buƙatar yau da kullum kamar su waya da sauransu.
     To kuwa a safiyar yau ƙarfe goma batai masa a asibitinba. Dole Omar ya fita da shi a ɓoye batare da ko Dr Shikurah ta sani ba. Shine ya kaisa airport ɗin ma. Yanaji yana gani Yoohan ya wuce ya barsa da damuwa.
      Asibitin ya dawo, inda ya tarar anata neman Yoohan. Shima kawai sai yayi pretending ɗin shiga cikin ƴan nema. Dan baisan wace amsa zaiba papa akan tafiyar Yoohan ɗinba. Bayan kuma shi kansa Yoohan ɗin ya masa magiya da roƙon bayason su papa susan ya wuce da saninsa. 
             Jin Yoohan ya wucene yasake birkita madam Chioma, yanda ta tashi hankalin nata har mamaki ya bama Uncle Joshua shi dai, amma sai baiyi maganaba dan hakan ba huruminsa baneba. Daga ƙarshe ma allurar barci sukai mata saboda yanda take faman rubzar kukan ita dai a nemo mata yaronta. Shi kansa papan itace ta sake birkitasa. Dan yasan dai Yoohan bazai ɓataba. Abinda kawai ya tsaya masa a rai shine minene ya saka Yoohan ɗin tafiya bayan kuma baida lafiya?. Dama tun jiya yaketa tunanin akan faɗuwar da akace yayi babu gaira babu dalili tunda har waya shidai yayi da shi a ranar da safe, kuma baiji wata damuwa tattare da yaronsa ba a lokacin da shuke wayar. Dan shine ma yace karya faɗama Momyn nasu zai dawo a jiya yana son ya mata surprise ne. Har Yoohan ɗin na masa dariya akan hakanma. Sai kuma gashi ya dawo ya iske waɗanan rikitattun tashin hankali da gaba ɗaya ya rasa makamar riƙewa akan faruwarsu.

___________________

       Nu'aymah na gidan Juliet Omar ya kira akan taje gida ga Yoohan nan a hanya. Abin ya bata mamaki dan sunyi da shi sai nan da sati biyu ma zai koma. Haka dai tai shiri ta koma gidan nata ttareda Juliet da tai mata rakkiya danta tayata gyara waje. Duk da ma tasan baza'a samu datti sosai ba tunda duka yau kwananta biyar da barinsa.
     Babu dattin dai kam sosai. Amma sai da suka gyara komai tsaf. Juliet ta tayata sukai har girki saboda tausaya mata da takeyi na halin da take a ciki. Sai da suka gama komai tsaf sannan ta wuce tabar Aymah na wanka. 
       Bata wani jimaba ta fito tai shiri cikin doguwar rigar atanfa mai faɗi data ɓoye cikinta. Wayarta ta ɗauka ta nufo falo dan yunwa takeji ta bala'i. Turus ta tsaya tana kallon Yoohan dake kwance a kujerar falon idanu a lumshe. koda wasa bataji motsin shigowarsa gidanba sam. Cigaba tai da takawa a hankali inda yake. Batare da tayi magana ba ta zauna a gefensa da kai hannunta ta janye nasa hannun daya dafe kai da shi.
      A hankali ya buɗe idanunsa dake jajur ya zuba mata su. Itama kallonsa take cikin ido sosai. Sai kawai yaji zuciyarsa ta ƙara raunana. A take hawaye suka cika idanunsa. Ɗayan hannunsa ya kai saman cikinta yana murmushin ƙarfin hali.
     Ita dai Aymah kallonsa take tamkar wata sokuwa, dan yanzu kam sai dai ta bama wani labarin mijinta badai ita a bataba. Cikin sanyin murya tace, “Baka da lafiya?”.
        Haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi yayi da ƙyar, sannan ya yunƙura ya tashi zaune yana cije baki daboda kansa dake masa ciwo har yanzun. Zama yay da ƙyau ya rungumota jikinsa, hannunsa nakan cikinta yana shafawa a hankali. Cike da raunin murya yace, “I miss you Sweet girl”.
       Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa kalar tambayar ɗazun. Murmushi ya sakeyi da sumbatar kanta. “Lafiya ta ƙalau baby, sai dai kewarki ce”. Duk da Aymah bata yardaba saita ƙyalesa kawai a hakan. Itama ta rungumesa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Duk da ciwo da ƙunar da yakeji zuciyarsa na masa bai hanashi bata haɗin kai ba. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ɗinma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.
       Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ƙoshi. Hankalin Nu'aymah ya sake tashi matuƙa saboda ta kasa gane kansa gaba ɗaya. da ƙyar dai ta samu yaci kaɗan ya sata ta ɗakko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.
      Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ɓoye mata ne kawai.

*_KANO NIGERIA_*

           A lokacin da madam Chioma ke can neman sa'a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ƙwamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa.
     Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yunƙuri aka fisgota ciki tare da daɗe mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ƙarshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ɗakin da bata saniba. Da matuƙar tashin hankali ta tashi tana ƴan waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa baƙon waje aka kawota......
        Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Murɗeɗen ƙatone da iya gani kasan ya damƙi namiji ma sai ya shinshino ƙamshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ɗakin dake tare da kujera ɗaya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, “An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki”. Ya ƙare maganar da juyawa ya fita abinsa.
     Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ƙoshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ƙila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta sha, dan ita kaɗai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan...

      Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sauƙi sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ɗaya a asibitin. Ranta dai na nan danƙare da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.

____________★
Chapter 178 · 0% Book details