← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 211

Sashe 205

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hakaba kuwa babu makawa sai an bankaɗo ainahin gaskiyar nine mai laifi ba ɗan uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya ɗauka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, ɗan uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen ɗaukar ƙyawawan halayyar ɗan uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na ɓoyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin ɗan uwana ba na mallakama mamana da ƙannenmu dukiya ba, sai dai naja ƴan uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin harƙallolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro ɗina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matuƙar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar ƙara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da kuɗaɗenta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin harƙallata, sun kuma san John ba ɗana baneba”. “Abinda ya faru baisa na daina harƙallataba, sai harkokine suka sake buɗewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara huɗu kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata ƙaramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara huɗu, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba'a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka taɓa kawowa a ranka ba dɗanmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na ƙara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta ƙwaceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro ɗina. Dukiyar ɗan uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan nasoba kuwa dole na haƙura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar harƙalla daban-daban. A wannan lokacin ne naje ƙasar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangarɗa akan zamana pastor. inda acanne muka haɗu da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da ƙyarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba ɗaya. Dan nayi alƙawarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama'ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko'a wancan karon dama bansan taka-maimai shi ɗan ina bane, nadai san musilmine ɗan arewa. a zahiri kuma na lulluɓe True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kanƙanin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na ƙyamar addini da wasu abubuwan namu duk da ƙanƙantar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar muɗin ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba ɗaya, koda ya girma bazai taɓa kawo a ransa muɗin ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji daɗin wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban taɓa yarda yasan ɓoyayyar harƙallataba Mamana ma da sauran ƴan uwana nasa akai musu asirin da bazasu taɓa tunanin ko kawowa a ransu niɗin ba ɗan uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa ƴaƴan, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami'a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga yaƴa uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon ƙasashensa da aiki ya tilasta masa yin gamo da wani dangin mahaifiyarsa ƙwaɓata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon”. “Abu mafi ɗagamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan alaƙa hankalina yayi ƙololuwar tashi, na kumayi murna dan sanadin John maƙiyina dana ɗauki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har ƙauye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa ƙiyayyarsu tun yana yaro, amma daga ƙarshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company ɗin yanata haɓaka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka haɗu wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za'ai ya iya gano shiɗin wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John ɗin mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da ɗimautar ƙwaƙwalwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntuɓi John akan mike alaƙarsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj ɗin. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina daɗi nakeji zai ɗaukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma daɗe ina addu'ar haɗuwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da ɗiyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin ɓata lokacine, da ƙyar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban taɓa faɗa mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da ƴaƴanta, kodan shita fara samu matsayin ɗa ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar ɗiyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala'in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min ɗaki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima ɗin na yarda ba ita ɗin bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa harƙalla ɗaya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin ƙaunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan harƙalla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota leƙen asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor ɗin da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sauƙi kafin na dawo kan John ɗin shima. Naji daɗin abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba ɗaya da zarar sun dawo ƙasar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma ɗauketa daga Austria ya canja mata ƙasar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga ƙasar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu ƙasar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa ɗaki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina ƙanƙanin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a waɗannan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa ƙasarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga baƙar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba ɗaya. Randa na gama shirya ƙudirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin ƙwallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma ƴan sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga ƙasar Cameroon. Da ƙyar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi ƙoƙarin zuwa ya isarmin da saƙon na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka ƙulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema ƴan sanda da nayi, sai da na bada ƙafa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani ɗan leƙen asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da ɗan da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan ƙura
Chapter 205 · 0% Book details