← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 211

Sashe 70

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

............Sake buɗe idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ɗaya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta riƙeta. Sannan babu wata sarƙa ko ƙarfe da suma suke amsa sunan ginshiƙi a gareta. Da rana hasken *_Rana_* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ƙawata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al'ajabi. Hakama da yammaci lokacin faɗuwar rana takan ƙawatu da kalar sky blue da na yanayin faɗuwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ɗaya. Babu kuɗin haraji babu na ƙarshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai taɓa jiran mu biyasa da ko taro ba?  ‘saboda shi ɗin *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KAƊAICE SA)’_*
         Wani yanki na zuciyarsa ya bashi wannan amsar.
       Samun kansa yay da sake lumshe idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data faɗo cikin kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ɗin nasa ne.
         ‘Tabbas ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?’. Ya amsa tamkar shi ɗin akeyima tambayar kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ƙasa cikin giza-gizai alamar lokacin faɗuwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
        Tabbas wannan tambaya ta tsayama Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ƙarasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai sannan ya iya barin jikin Window ɗin zuwa toilet.
     Ji yake a ransa bazai taɓa samun nutsuwa ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana buƙatar sanin (Hanyar fahimtar ni'imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).

       A gaggauce ya gudanar da komai. Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ƙananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai gajeren hannu. Sai ya ɗora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie ba, maɓallin shirt ɗinma ba duka aka rufe ba. Cikin ƙamshinsa ya baro cikin hotel ɗin batare daya nema inda su Solomon suke ba.
         Safiya ce sosai a garin, hakan yasa da ƙyar ya samu keke napep, shima da mutum ɗaya a ciki. Bai damu ba, duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ɗin. Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ƙyar ya iya haɗa hausan ya bashi amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin abubuwa sosai saboda mu'amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza'a rasaba suma ɗai-ɗai ne.
     Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya miƙama mai napep ɗin. Da mamaki shiko yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba. Sake miƙo masan da yayne ya saka mai napep ƙoƙarin haɗa ɗan turancinsa ya sanar masa naira ɗari da hamsin ne kuɗinsa. Duk da dai turancin bai haɗu da ƙyau ba Yoohan ɗin ya fahimci mi ya faɗa. Dan haka ya ajiye masa kuɗin a jiki yana faɗin, “Na baka ne duka”. Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya kasa haƙuri sai da ya dara.
       Yoohan baibi takansa ba ya nufi ƙofar gate ɗin su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
               Sau uku yay Knocking sannan maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo yana tambayar “Wai wanene haka da farar safiyar nan?” dan yasan su Baba malam ta ƙaramin gate sukaje massallaci yau.
     Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay har sau biyu bashi kaɗai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya gama ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin yace, “Samari lafiya kuwa? Mikake nema ko buƙata anan?”.
        Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan kalmar (lafiya da wasu ɗai-ɗai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ɗinma dai ba fahimtar yayi ba. Sai ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
      “To bakajin hausa kenan?”. Maigadi ya faɗa a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana zuwa). Kafin Yoohan ɗin yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yunƙurowa Yoohan ɗin yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ƙofar.
      Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake fitowa cikin massallacin. Sai kuma sautin karatun yara da shima alama ta nuna daga harabar massallacin ne.
       Nufar gate ɗin massallacin yayi, kasancewar shi a buɗe yake sai ya samu damar shiga kansa tsaye. Sai dai bai kai tsakkiyaba wani cikin almajiran malam ya tsaidashi da sauri, dan kallo ɗaya zai tabbatar maka Yoohan ɗin ba musulmi bane.
      Anyi sa'a almajirin malam najin turanci, sannan kuma duk zuwan da Yoohan yayi gidan sau biyu ya gansa. Ba ƙaramin daɗine ya kama Yoohan ba jin cewar almajirin malam najin yaren da shima yake ji. Cikin sauƙi suka gaisa ya sanarmasa wajen malam yazo. Kuma yana cike da ƙaguwar san ganinsa domin dalilin babban uziri.
         Duk da almajirin malam yayi mamaki hakan bai hanashi yarda zaima Yoohan ɗin iso ba. Dan haka ya nuna masa wani ɗan dakali alamar ya zauna ya jurasa. Shi kuma ya juya cikin massallacin inda yasan malam na zaune yana karatu da azkar kafin ya fara karatu ga magidantan anguwar dakan ɗauki karatun safe da baya wuce zaman awa guda.

      Yoohan bai zauna ba. Sai ma faman bin massallacin yake da kallo. A ransa yana sake jinjina ƙoƙarin da su baba malam sukai wajen ginashi. Dan ƙaton gaske ne, kuma ya ginu da gini mai ƙyau. Gashi an shafesa da farin fenti yanata ɗaukar ido tamkar ba'a shiga cikinsa, sai shukoki da suka sake ƙawata shi suma. Ko ina kuma a tsaftace yake. Daga wajen da yake tsaye yana shaƙo daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga massallacin wanda kullum safiya da maraice Nu'aymah ke zuwa ta sharesa ta saka turaren wuta da kalolin Air Fresheners masu daɗin ƙamshi..........
     Kukan wani yaro ne ya katse masa tunanin nasa. Ya ɗan juya inda yake jiyo kukan. Hakan yayi dai-dai da fitowarta daga cikin ajin da take koyarwa riƙe da bulalar dorina. Sanye take da dogon hijjabi mai hannu fari tas dan har yana jan ƙasa. Hannunta na dama riƙe da Al-qur'ani, na haggu kuma bulala. Yanda take jijjiga bulalan tana magana da nuna yaron ne ya sakashi shagala da kallonta. A ransa ya raya, ‘Ashe kowa ma masifa take masa?’. Jiba dai yanda takema yaro ƙarami duk da kuwa bayajin mi take faɗa. Amma yanayinta ya nuna faɗa takeyi dan tama saka yaron kneeling ne a ƙofar ajin.........
       “Yahya! kai ne da safen nan?”.
Maganar baba malam ta katsesa daga kallon Nu'aymah daya shagala yi. Numfashi ya sauke tare da juyowa ga baba malam ɗin. Baba malam daya juya yana kallon abinda Yoohan ɗin ya shagala kallo shima ya ɗauke kansa ya maido garesa. Sake mai-maita masa tambayar yayi a karo na biyu.
         Yoohan da ya sunkuyar da kai ƙasa yace, “Uncle, inason sanin minene ni'imomin dake a cikin addininku na musulinci?!”.
        Ba baba malam da yayma tambayarba, hatta Abban su Abdallah dake fitowa daga massallacin sai da ya taka wani uban birki.
      Baba malam da jikinsa ya hau tsuma yace, “Yoohan sake maimaitawa naji”.
     Babu musu Yoohan ya kuma faɗin,
               “Ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?!”.

الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
        Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
        Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.
Chapter 70 · 0% Book details