← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 211

Sashe 137

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Dukkan abinda ya dace Yoohan ya kimtsa akan tafiayarsu ya tattara. Yayi sallama da kowa na gidan. Momy dai nata baƙin rai dan tace zata bisu yace a'a. Ta bari idan papa ya dawo sai suzo tare.
         Bayan la'asar ƴan gidan su Abba suka iso, har dasu Adawiya. Duk ƙiyayyar da Adawiya kema Aymah yau sai da tai hawayen tausayinta kamar yanda su Yusrah keyi suma. Ƙarfe biyar dai-dai Ambulance da zata ɗauki Aymah ta shigo gidan tare da Dr Shikurah.
     Yoohan ya ƙara duba komai na sashen nasu, ya tabbatar ya kashe duk wani kayan wuta, an kuma fidda duk abincin da zai iya lalacewa. Da kansa ya kulle ko'ina ya saka keys ɗin a jikkarsa. Duk ƴan gidan sun fito compound, babu dai wanda ke nuna jin daɗinsa da halin da Nu'aymahn ke ciki a zahiri. Sai dai a zuciya ALLAH kaɗai yasan karatun kurma.
         Duk waɗanda zasu musu rakkiya airport sun shiga mota, harda Uwaliya da zata koma da zama gidan Abba sai su Aymah sun dawo. Haka motocin suka fita a jere waɗanda aka bari na binsu da addu'ar ALLAH yasa a dace. 
      Tafiyar mintuna kaɗan ce ta kaisu airport. kasancewar jirgin nasu na gab da tashi aka shiga da Aymah cikin jirgin, kafin suma su Yoohan da sauran passengers su shishshiga. su Abbah na binsu da addu'a kafin suma su taho. Basu bar airport ɗinba sai da jirgin ya ɗaga a samaniya ƙarfe biyar da rabi dai-dai.
           Sun sauka a Dubai, daga can suka shiga jirgin kaisu Austria.

________★★★_______

        Tun jiya Nu'aymah keta zuwama Umm a rai. Ta kira wayarta kusan sau uku kuma a kashe. Gudun karta saka abin yay mata tasiri a rai sai ta barshi akan Aymah bata da cajine maybe. Ko kuma ta kashe wayar a wajen shiriritan ta.
       Haka taita juriya har washe gari da baba malam ya dawo daga tafiya. Shine ya lura da yanayinta. Cike da kulawa ya shiga tambayarta ko lafiya?. Duk yanda taso dannewa kartace komai saita gaza. Muryanta a sanyaye tace, “Haka kawai taketa zuwamin a zuciya tun jiya. Na kirata kuma wayan nata a kashe. Na nema Uwaliya mun gaisa nace ta bata tace min wai barci takeyi. dana sake kira daga baya kuma itama wayan tata a kashe. sai nakeji a raina kamar ba lafiya ba”.
       Ɗan jimm baba malam yay yana kallonta. Dan Abbah ya kirashi bayan sallar magriba ya masa bayanin cewar jikin Nu'aymah ya motsa sosai harma sun wuce Austria yau da yamma. Murmushin ƙarfin hali yayi dason kwantar mata da hankali. Yace, “Babu komai insha ALLAH sai alkairi. Kimata addu'a kawai nasan zata kiraki idan ta kunna wayar. Nima tun jiya da safe bamu sake waya da itaba ma. Karki damu Jannat, ALLAH na tare da Zainab a duk inda take”.
        Yanda ya ambaci ainahin sunan Nu'aymah ya sake sakata jin wani iri. Amma sai ta danne dan karta sake ɗaga masa hankali shima.
    Daga haka suka bar maganar, sai dai daren ranar daga farkonsa har ƙarshe akan sallaya Umm da Baba malam suka kwana suna mikama UBANGIJI kukansu akan lafiyar yarinyarsu. Duk da ita dai Umm batasan ainahin abinda ke faruwarba.

____________********___________

          Jirgin su ya sauka lafiya a babban birinin ƙasar Austria, Vienna International airport. ananma dai Ambulance ce tazo ta ɗauki Nu'aymah, Yoohan da Richard & Solomon kuma suka shiga taxi. Tafiyar mintuna kalilan ta kaisu katafaren babban asibitin Vienna daya haɗu harya gaji. Babu ta yanda za'ai ka ɗauka asibiti ne na gwamnati inba faɗa maka akaiba. Sannan abun zai matuƙar birgeka a yanda suka samu tarba. Ko hakan yanada nasaba ne da sanin Yoohan ɗin oho.
         Ɗaki na musamman inda sam babu hayaniya aka kai Nu'aymah. Da alama ma an tanajesane domin irin masu matsalarta. Wajen koda takalmi mai ƙara ba'a shiga. Kai ko key ƙaramin alhaki ba'a buƙata. Duk wani abinda ke'a sashen na amfani zaka samu na robane saboda tsabar sanin makamar aiki. (a raina nace hummm ya kaga irin haka a 9ja😁).
          Gaba ɗaya Aymah batasan a inda kanta yake ba, dan tun daga 9ja aka yo mata allurar data sakata doguwar suma saboda ba'a buƙatar duk wani motse-motse a kusa da ita.
         Sai da Yoohan ya tabbatar an ɗorata akan matakin farko sannan suka bar asibitin. Hotel ɗin da Yoohan yafi sauka idan ya shigo ƙasar suka nufa. Acan suka kama masauki. A kallo ɗaya zaka fahimci shima yana buƙatar kulawar, dan haka Rich ya matsa masa akan yay wanka yaɗan kwanta koda bazaiyi barcinba zai huta.
      Bai musaba yabi shawararsa. Shi kuma Rich ya fita zuwa nasa ɗakin. Bayan ya fito a wankan gorar ruwan addu'oin da Abba ya bashi ya fiddo, yay bismilla ya sha tare da shafe fuskarsa zuwa kansa sannan ya kwanta yana ambaton sunayen ALLAH da tuni ya gama haddacesu a kansa. Tun yanayi laɓɓansa na motsawa har ya komayi a zuciya. Cikin amincin UBANGIJI gagara misali sai gashi nannauyan barci yayi gaba da shi cikin lokaci ƙanƙani. Sai dai yayisa ne cike da mafarkin Nu'aymah. Hakan yasa bai wuce awanni uku ba ya farka. Alhmdllh ko yaya dai yaji sassauci ba kamar ɗazun ba. Ganinma lokacin salla yayi sai kawai yayo alwala yazo ya kabbara salla. Ko raka'ar farko bai ƙulla ba Richard ya shigo ɗakin domin son dubashi.
       A wani irin mugun shock yace, “Jesus!! Yoohan!! Salla ka komayi?”.
       Bai samu amsa daga Yoohan ba dan shi gaba ɗaya ma hankalinsa baya a nan kusa. ya nutsu sosai wajen bautar ALLAH.
      Ruɗani iya ruɗani Rich ya shiga. Dan a take gumi ya jiƙesa sharaf ya nata kaikawo da surutai kamar wani zararre. 
         Shi dai Yoohan bai katse sallarsa ba, sai da ya idar a tsanake yay addu'oin fatan samun lafiya ga matarsa sannan ya dubi Richard da ya kasa zaune ya kasa tsaye. A daƙile yace, “Lafiyarka kuwa?”.
         “Kai zan tambaya kana lafiya kuwa Yoohan?!. Salla fa naga kanayi?!”.
      Idanu kawai Yoohan ya tsurama Rich dake maganar da yare tamkar zai haɗiye harshensa.
     Ganin kallon da yake masa ne ya sake harzuƙa Richard ɗin, ya hayayyaƙo ma Yoohan da iya masifarsa, “Yanzu wannan ƴar yarinyar har takai ta canja ka ka bar addininka na gaskiya ka koma nata. John What's wrong with you? Are you mad? Are you............?”.
        Saurin katsesa Yoohan yayi ta hanyar ɗaga masa hannu.
      “please Richard!!. Ni ƙaramin yaro ne da zaka zauna kana min ihu a kai? Karka manta shekarata ɗai-ɗai har talatin da biyu. Kasan kuwa inada right ɗin zaɓama kaina abinda nasan ya dace dani ko?.......”
       “Yes! Kanada zaɓi, kuma shekarunka sun kai. Amma tabbas alamu sun nuna baka a cikin hankalinka ne. Shin ƙyawunta ne ya ruɗeka kokuwa kuɗin da mahaifinta ya mallaka? Sunan da yay? Kokuwa asiri sukai maka?”.
      A kanran farko Yoohan yay wani malalacin murmushi, sai kuma ya tsuke fuska tare da jan tsaƙi yana bin Rich da wani irin shegen kallon ɓacin rai da fusata. “Richard! Mubar wannan maganar dan ni ta shafa.......”
      “Nima ta shafeni Yoohan. Dan ka wucemin aboki kai ɗan uwana ne jinina da zan iya bama kariya a kowanne irin yanayi a kuma kowanne irin hali”.
        “Tunda kasan hakane sai ka bani lokaci dan ka fahimceni”.
        Baki Rich ya buɗe zai ƙara yin magana Yoohan yay azamar ɗaga masa hannu.
        “Please Rich, kana ƙaramin headache. Ka bani lokaci zamuyi magana”.    
          Zama kawai Richard yayi batare da ya sake magana ba. Dan yasan Yoohan ɗin ya kai maƙura kenan. Idan ya cigaba da jan maganar komai zai iya faruwa a tsakaninsu. A ganinsa kuma yanzu na lokacin samun matsala bane. Kamata yay ya taimakama Yoohan ɗin ya dawo cikin hankalinsa dan ya fahimci an gusar masa da hankaline kawai ta hanyar asiri. Shiru ɗakin ya ɗauka har zuwa wasu mintuna kusan ashirin. Kafin Yoohan ɗin ya fara miƙewa ya ɗauka jacket ya ɗora saman ƙananun kayansa. Batare da yayi magana ba ya nufi ƙofar fita. Shima Richard ɗin miƙewa yay yabi bayansa suka fice daga hotel ɗin. a waje suka tari taxi dan komawa asibitin.

__________★★★★___________

*_WASHE GARI_*

       A yau data kama ranar da za'aima Nu'aymah aiki su baba malam sukaso tahowa shi da Abban Abdallah. Sai dai a bisa dalilin wani ɗan tsaiko hakan ya gagara. Tafiyar tasu ma ta tabbata sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu.
      Hakan baisa sun sare zaman jigum-jigum ba. Sai sukai zaman yin addu'oin samun nasara a aiki dan yanda Yoohan keta maimaita a tayasu da addu'a yana ƙara saka tsoro a zukatansu. Shi kansa sun fahimci a tsoratan yake. Saboda bai ɓoye musu ba game da haɗarin da aikin da za'ai mata ke da shi tun farko. Sai dai idan ALLAH ya amince sai ayi kaga kamarma bata taɓa shiga makamancin matsalar ba.
       Hajjo har abincin sadaka tasa akayi, aka kuma sayi abubuwan wasan yara da makamantansu aka rabama yaran gidan marayunsu don suyi farin ciki suma. Maybe darajar hakan ALLAH ya saka musu hannu a lamarinsu suma.

*_ƘASAR AUSTRIA*

          A nan kuwa Yoohan cike yake da fargaba. Sai dai yanata ƙoƙarin dannewa saboda kwarin gwiwa da Dr Liam Ke basa akan aikin. Dan shi da Rich sai a hankali. Ya ɗauki fushi dashi babu gaira babu sabar. Shi kuma sai hakan yay masa zafi ya tattarashi ya watsar. Ko game da harkar asibitin ya daina tuntuɓarsa da komai. Idan abu yake buƙata zaisa Solomon ne kawai yayi masa. Kai a yau ma gaba ɗaya baisa Richard ɗin cikin idanunsa ba har yanzun da suke shirin shiga da Nu'aymah ɗakin da za'ayi aikin.
         Baya buƙatar haɗama kansa damuwa da yawa. Shiyyasa ya ɗauki lamarin Rich ya ajiyesa gefe. Dan shi dai abinda ya sani bazai taɓa komawa abinda Richard ɗin ke buƙataba dan ALLAH ya nuna masa ƙyaƙyƙyawar hanya a yanzu mai cike da ɗumbin haske. Ai ko papa dake matsayin mahaifinsa bai isa sashi komawa kafiri ba balle Richard duk da kuwa yana sonsa har cikin ranshi.
Chapter 137 · 0% Book details