Sashe 150
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
yayi ya biyota inda ta koma ta zauna akan sofa tana sharar ƙwalla. Ɗaukarta yay cak zuwa bayin tanata wantsala ƙafafu da faɗin ita ya sauketa. Tama fasa koyawar yaje yay Searching a Google ai zai gani. Ko jintama shi bayayi sai da ya direta cikin wajen wankan, zata gudu yay saurin kunna shower ɗin. A take tai musu jalab da ruwan data sheƙo. Ya jawo hannunta ta dawo saman jikinsa. Jin santsin ruwa zai jata ta faɗi dole ta rirriƙesa ruwan na sauka musu a jiki. Da wannan damar Yoohan ya kafe gaban rigarta daya jiƙe da ruwa komai ya fito yanda ya kamata da kallo. Bata fargaba sai da taji hannunsa a wajen. Ƙasa tai da sauri tana ture masa hannu. A ranta kuwa al'amarin sake firgitata yakeyi. ƙara ƙarfin shower ɗin yayi, hakan yasata tilas ta sake miƙewa tana sharce ruwar dake sakko mata a fuska ko gani da ƙyau yana neman hanata. Numfashi ma takai da baki take firzarwa. Shi kansa ruwan ya masa yawa. Amma saboda karta gudu yay haƙuri yana saka hannu yana sharcewa kamar yanda takeyi itama. Sai da ya tabbatar sunyi jagab sannan ya kashe shower ɗin. Ya koma hanyar ƙofar wajen wankan ya tsaya. A mamakinta sai gani tai ya fara cire rigarsa. Ƙasa tai da kanta gabanta na faɗuwa. Ganin wandonsa ya saɓulo ƙasa ta ƙara kiɗimewa. Da sauri ta juya bayanta. Hakan ya bashi damar matsawa ya manna bayanta da ƙirjinsa. “Karki zama malama mai yima ɗalibanta rowar ilimi fa”. Yanda yake maganar yana yawo da hannunsa akan cikinta sai ya nema sake susutata. Tama rasa tunanin da zatayi akan wannan al'amarin nasa mai wahalar fashin baƙi. Tanaji tana gani yay amfani da ƙarfinsa wajen zame mata riga da wandon jikinta. Sai dai fa duk yanda yaso cire harna cikin taƙi yarda sam. daga ƙarshe ma sai ta saka masa kuka. Ƙyaleta yayi ganin dai ankai inda ma baiyi zatoba. A haka ta fara ƙoƙarin koya masa wankan duk dan ta samu ta kuɓuta daga wannan dabaibayin da yayma rayuwarta baki ɗaya. Sai da tai nisa a koyawarne ta fahimci ya iya, dama ashe kawai danya bata wahala da kallar mata jikine ya sashi cewa ta koya masan. Wannan haushin ya sakata harya ƙarasa wankan ya fita ya barta dan taki yarda tayi ita tana antaya masa harara. Duk da ƙaryar datai masa na cewar babu wani wanka daya hau kanta yana fita kuwa sai da tayisa. Dan duk wautarta tasan abinda takeyi tunda tanada ilimin addini. Aiko dai ansha ƙunƙuni. Tana cika baki da iska ta miko hannu akan ya bata Bathrobe da towel, dan yana a bayin bai fitaba. Hand dryer ɗin hannunsa ya ajiye. Ya ɗauki rigar wankan ya kai mata sai dai babu towel. Hannun nasa ma sai da ya sha harara sannan ta amsa. Ganin babu towel ɗin kuma taita ƙunƙuni. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta ganin daga shi sai towel iya ƙugu zuwa gwiwa. Shiko gashinta dake ɗigar ruwa yabi da kallo. A cikin ransa dariya ya sanya mata yana faɗin, ‘Yarinya ashe kinada lafiya tunda saƙona ya isa inda na aikashi?’. A fili kuwa sai ya fuske abinsa. Tai saurin ɗaukar towel ta naɗe kanta wai dan karya gani. Ƙarasa hidimarsa yayi ya fito ya barta. Koda ya fito mai ya shafa yay shiri cikin ƙananun kaya. Baƙin wando da pitch color ɗin shirt mai dogon hannu. Yana fesa turare ta fito. “Kiyi shirin fita”. Ya faɗa yana ajiye turaren. Bata tanka masaba. Tai tsaye har sai da ya matsa a wajen sannan ta buɗe akwatin nasu ta ɗauki jallabiya ɗaya. Bayi ta koma ta sanyo sannan tazo ya jasu salla. Suna idarwa yace ta ƙarasa shirin yana zuwa. Fita yay, ita kuma ta miƙe ta shafa mai, da ƙarasa kimtsawa. Tana gamawa kuwa yana dawowa. Zata fara feshi da turarensa ya amshe yana faɗin, “Silly girl ya isa haka dan ba tallanki nazo yima Austrian ba”. Ita dai bata tanka ba. Bakuma ta yarda sun kalli juna ba dan wannan fushin da takeyi tsabar jin kunyarsace kawai ke ɗawainiya da ita. Tsaf suka fito abinsu gwanin sha'awa. Tamkar ka sacesu ka gudu. idan ka gansu sai ka ɗauka ƙaramar ƙansawarsa ce ma. Yau dinma bata cuci kantaba sai da taita kalle-kalle har suka fito ƙaton reception ɗin hotel ɗin. Zuwa yay yayi signing kamar yanda dokarsu take. Daga haka yaja hannunta suka fito............✍