← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 211

Sashe 21

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena
Ya sauke wani irin ajiyar zuciya.

Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had'a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana

Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k'arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad'aya.

Shi kuwa ganin naki kallonsa yace "Taimakamin da ruwa in Sha Naeema"

"Mik'ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan.

Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d'ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa.

D'auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb'ensa duk ya bushe.

"Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani"?

Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba

"Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu'a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin dashi kana kallon irin dukan da take wa Zahira duk sabida tsabar tsanar da tamin ta ringa jifanta da mugayen kalamai Wai baza tayi albarka ba Yar iska zata Zama kuka na fashe dashi Dan kalmomin Nan data jefi Zahira dashi ya balain yimin ciwo na cigaba da Magana Ina iya wanan Bai isheta ba ta d'auke min Nadeeya tsabar bakin cikin an ganta Naseer ta fito tana kururuwa Tana watsawa kanta kasa Naseer da kiyayyar ta zata tsaya iya kaina wlh Zan jure amma yanzu ta fara tab'a min Yara bazan jure ba Naseer ba tare aka halliceni dakai ba zaka iya rabuwa Dani ka cigaba da rayuwarka kana da Daman da zaka auri Mata hud'u ka Shimfid'a irin rayuwar da kake so dasu a ganina idan kana kaunata zaka so samun kwanciyar hankalina na Kuma Rayu cikin farinciki Ina kaunarka har a Raina Amma idan akwai cutarwa gwara mu hakura ka sauwake min ikon Allah yasa kagani a zaune a yanzu har nake maka magana a cikin Minal ba irin azabar da Umma Bata gana min ba ta window na duro danake nakudarta sabida Kar ta kasheni banajin addua Zai iya sauko da Umma ta kaunaceni Allah na tuba Umma sosai nake ganin tsanata a idonta Dan Haka Naseer na hadaka da girman Allah ka sauwakemin albarkacin yaran Nan ka gyara min gidanan da iyayena Suka barmin na Rayu da yayana cikin kwanciyar hankali idan ma bazaka iya bani jari ba Ni zan nemi aikin da Zan ciyar dasu Naseer Dan Allah ka sauwakemin na gaji wlh Nagaji"

Na karashe Ina fashewa da kukan da nakejin yinshi ne kawai zai saka naji zuciyata ta rage nauyi da zafi idan har Zan tuna wani zalunci da umma tamin sai kirjina yyi nauyi Haka Zan ta kuka har sai naji sanyi a Zuciyata

Naseer kuwa Bai iyamin magana ba in Banda idonsa daya kad'a.yayi ja jijjiyoyin kansa sukayi rud'u rud'u ni nasan sabida gaban yayansa yake shiyasa yake ta mayar da hawayen daya cike Masa ido.

Zahira kuwa da Nadeeya duk da karancin shekarunsu Haka suka hau kuka suma.
Naseer kuwa kamar maganuna bulala Suka Masa a jiki a Haka ya zauna jiki duk ba kwari nasan Dan muna gaban yarane da ya janyoni ya rungumeni ya rarrasheni.

Sai Dana ci kukana na koshi na mik'e tare da d'aukar Humaira.

Ban kalleshi ba nacewa su Zahira suzo mu koma gidan Mai unguwa Dan ko tabarma babu a gidan namu bansan wayanda suka kwashe ba

Naseer Bai mana magana ba har muka fice

Muna zuwa na bawa Zahira tabarma da ruwa a buta Akan ta Kai Masa yayi sallar Magriba.

A hanyar Kai masa ruwa da tabarmar

Mai unguwa ya ganta ya hau tambayarta inda zata je ita kuwa tace Masa Abbanta zata kaiwa.
Take Mai unguwa ya hau washe baki cikin farinciki zuwan Naseer

Yana iddar da sallah ya shigo har d'akin da aka bamu muka zauna da yayana ya daga labulen Yana "Ashe babansu yaran Nan yabi yo sahu Kai Masha Allah naji dadin zuwan da yayi Allah ya daidaita ku Dama kullum sai nayi addua akan Allah ya sa ya mayar dake dakinki Dan shine rufin asirnki an Riga an haifi Yara har hudu ai sai Kuma ayita zaman hakuri Allah ya Kara kau da fitina Zan Masa magana shima Bari na saka a kiramin shi

Nauyin Mai unguwa da yanda ya nuna farincikin zuwan Naseer yasa na kasa Koda magana har ya fice daga gidan.

Sosai naji da gasken bazan koma gidan Naseer ba shiyasa na bi dashi ta ruwan Sanyi Dan ya bani takarda ta Amma idan yak'i kuwa ya zama Dole na fito na gayawa Mai unguwa halin da nake ciki da mahaifiyarsa nasan shima idan yaji bazai so na koma ba tunda neman rayuwata Dana yayana mahaifiyarsa take.

Ana iddar da sallah ishai Mai unguwa ya aiko a kirani
Ina zuwa yace na Kira Masa Naseer ba yanda zanyi Haka na juya na nufi gidanmu Dan na Gaya masa rufin asirinsa shine ya sauwake min cikin ruwan Sanyi sabida bana San na ringa fallasa Sirrin mahaifiyarsa.

Ga mamakina Ina Isa Naseer na zaune a Inda muka barshi ga tabarma da ruwan da Zahira ta Kai Mai a gefe ya tsurawa waje daya Ido kirjinsa sai sama da kasa yake

Bansan lokacin Dana taka da Sauri na Isa wajensa tare da durk'usawa a gabansa ba

Yana dagowa ya wawuroni ya kankameni cikin wani irin murya daya karyar min da ba iya zuciyata ba komai na jikina

"Naeema taya Zan soma rayuwa batare da ke ba Taya Zan soma rayuwa da wata matar idan ba ke ba Naeema nafiki Jin ciwon halin da kike ciki sanadin halin Mahaifiyata na kamu da mumunan hawan jini ban taba fada Miki bane Naeema Tayaya Zaki ce na sawake Miki ya kikeso nayi da Raina ke da yarana nake gani nayi farinciki da Ana canja uwa da na Dade da canja Umma badan Mahaifina da Abba sun tabbatarmin da ita ta haifeni ba Naeema da sai nace Umma ba Mahaifiyata bace Dan Uwa da tausayi aka santa uwa bata cutar da dan data Haifa na rasa yanda zanyi da Umma nayi nasihar nayiwa waazin duk tak'i ji bakece Bata kauna ba Naeema Ni data Haifa nine Bata so Dan tasan farinciki da kwanciyar hankalina kune Naeema wlh da Umma zata ce na mallaka Mata duk abinda nake dashi zata barni mu Rayu cikin kwanciya hankali ko daki dayane na Kama Mana na ringa dako muna ci muna Sha da.naji dadi na.rasa yanda Zan mata Dan Allah Naeema rabuwa Dani bashine mafita ba na yarda Zan Kara nema miki wani gidan batare da saninta ba Ni Kuma zance Mata har yanzu banganki ba"

"Naseer bazan koma Garin kano ba sai dai ka gyarmin Wanan gidan ka ringa zuwa kana ganinmu "

"Ya zamuyi da Karatun yaran namu kasuwanci na fa danake yi a garin Kano wlh Zan iya takuna bazan Bari Umma ta.san naganki ba Zan ringa zuwa ko sau ukune sati Dama akwai wani karamin gida Dana siya a sharada inaso na zuba Yan haya tallansa akamin Mai gidan na bukatar kudi shine na siya kawai Zan gyara miki ki koma can wlh Umma bazata Sani ba"

A takaice duk ta Inda na b'ullowa Naseer sai ya zame ya kalamanceni abinka da tsakanin mata da miji sai Allah tuni Naseer ya shawo kaina duk alwashin Dana Sha yabi iska muna zuwa gaban Mai gari yayi wa Naseer fada da naseeha washegari muka fara shirye shiryen komawa Naseer sai lallab'ani yake Yana riritani (Nafeesa Naseer na balain Sona rabuwa daya k'iyi Dani ya jawo Mana masifu da ko makiyina bana fatan yyi kwatan rayuwar da mukayi)

Matar Mai unguwa ita ta yarfamin kitso da Jan lalle na garjajiya yayana ma.aka musu kitso

Naseer kuwa ya cika Mai unguwa da abun arzki da matansa da yayansa tun kafin mu taho aka fara gyara gidanmu Inda Naseer ya bawa Mai unguwa kwangilar Ana Gama gyarawa a nemi Yan haya a saka a ciki kudin Kuma ya ajiyemin.

Hotel ya Kama Mana da muka iso sosai Naseer jikinsa ke rawa kamar Wanda yayi sabon aure duk wani Abu daya gani sai ya siyo Mana Dan sati daya ya kama Mana abinda ke fita dashi kawai gyaran gidan sharada ne da Abubuwan bukata da zamu yi amfani dashi.

Inama Umma ta saka Mana albarka a aurenmu ta daina daga Mana hankali da sai nafi kowace mace dacewa da gidan miji Dan ranar da muka kwana biyar Naseer ya siyomin set din sarka da dankunne har da zobe na daham Dubu talatin a lokacin ba karamin kudi bane sababin Kaya kuwa Haka ya cike Mana shi a akwati biyu atamfofi na ma kuwa Mai karamin kudi a ciki shine dari bakwai Wanda a kudin yanzu Zan iya yin Dubu biyar.

A Dan tsakanin kuwa sosai na dage da Addu'a Naseer kuwa shima Bai zauna ba.

A ranar da muka cika sati daya muka tare a karamin gidan Naseer dake sharada.

Cikin kwana biyu ya samowa su Zahira makaranta har da Minal suka fara zuwa

Har wani Dan sheki yake Yi na kwanciyar hankali.

Ni kuwa Inda ya kasance d'akina sai Dana rataya abinda Mallam Musbahu ya bani Dan dazan tafi sai Dana cire na kaina kuwa bana Wasa dashi sai idan Zan shiga bandaki nake cirewa Ina fitowa kuwa na maida kayana.
Chapter 21 · 0% Book details