← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 211

Sashe 101

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Tunda aka dawo da Nu'aymah sashen baba malam ALLAH ya bata ikon ganinsa saita damƙe hannunsa tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba.
        “Abbah kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Abba kamar ana kartamin ƙarfuna a ciki. Innalillahi... Abbana zan mutu..”
        Cikin rawar harshe baba malam yake girgiza mata kansa da haɗiye abinda ke cinkushe masa maƙoshi da ƙyar. “Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha ALLAH ga Doctor nan zuwa kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Hajjo da Ananah ma hawaye sukeyi. Haka su Abban Abdallah ma duk zukatansu suya suke da tausayinta.
       Sallamar da akayi a bakin ƙofarne ya sakasu duk kallon ƙofar tare da amsawa. Ahmad ne ya fara shigowa, yana sanye cikin tattausan farar shadda harda babbar riga. Har yazo tsakkiyar falon sai kuma ya ɗan juya ganin wanda suke tare bai biyosa ba. “A'a Doctor shigo mana”.
      Kusan seconds biyar kafin a ɗaga labulen ya shigo bakinsa ɗauke da tausasa kalaman sallama. Sanye yake cikin wata shegiyar bugaggiyar shadda getzner kalar royal blue. Wando da riga harda babbar riga. Sai hular zanna daya murza itama royal blue data samu nutsatstsiyar saƙa. Hatta da agogon dake a tsintsiyar hannunsa kalar blue ne. Wanda bai saniba sai ya ɗauka wannan ɗin itace shigarsa dama can tun fil azal. yayi ƙyau harya gaji a cikin kayan. sun sake fidda masa kwarjini da cikar haiba da kamala. Farar fatarsa ta sake haskawa tamkar wata ɗan daren sha biyar. Yanda sajen fuskarsa da kwantaccen gashin kansa dake baƙi siɗik kwance a ƙeyarsa suke ɗaukar ido babu tababa zaka iya sakashi a jinsin larabawa. Idanba faɗa maka akaiba bazaka taɓa yarda Dr Yoohan ɗan gidan Papa da Madam Chioma ne ba wanda ko hausar bai gama fahimtar inda ta dosa ba balle akai ga larabci.
      A hankali ya cigaba da tako ƙafarsa dake sanye cikin baƙar safa cikin falon, dan ya cire takalman a ƙofa.
         Tunda yay sallama  Ananah da Hajjo suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Umm kam kallo ɗaya tai masa ta maida idanunta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin girmamawa ya gaida su Hajjo. Suma sun amsa masa da kulawa harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi. Dan bayan gaisuwar baiji mi suka faɗa ba sam tunda da hausa sukai magana.
      Baba malam da ya tashi daga inda yake zaune ne ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Nu'aymah da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Aymah.
      Da sauri Ananah tace, “Ɗan nan ko akwai matsala ne?”. Ya ɗanji wani abu daga zancen nata. Sai dai bai iya haɗasu a jimlace yanda zai fahimta ba. Hakanne ya sakashi kallon Ahmad dake ɗan murmushi. Faɗa masa abinda tace yayi, hakan yasa Yoohan cewa, “No babu damuwa Mama. Sai dai a ringa kula, indai zata ringa shiga irin wannan yanayin akwai matsala. Aikinmu zai dinga komawa baya”.
         “Yoni yaro bafa jin wannan yaren naku na masu jajayen kunne nake ba, kai Amadu fassara mana mi yake cewa”. Ananah ta faɗa da iya gaskiyarta.
      Gaba ɗaya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ƙofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ƴar tsokana Ahmad yace, “Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan”.
     Daƙuwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ƙeya tana faɗin, “Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ɗauki amanar kanku kuka miƙama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ƙara ƙirƙirowa. Shima Yahaya ɗin kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar”.
      Duk da Yoohan bajin abinda ta faɗa yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ƙwarewa sai masifa da faɗa kamar kajinaye.......
    Hannunsa da Nu'aymah ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abbah ka riƙemin zai fashe”.
       A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
       “Inaga mu bara mu barka kayi aikinka”. Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
    Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abbana”.
      Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Hajjo. Yoohan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH”.
       Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ɗinba sam. 
       Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ɗin da suka shigo yana faɗin, “Brother Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?”. “Yes! Doctor babu damuwa”. Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ɗin.
      Wata irin zabura Nu'aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
        Cikin zafin nama Yoohan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Nu'aymah faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “Relax, Please calm dawn!”
      Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abbah banaso”.
       “Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
     Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, “Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ”.
     Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya miƙama Yoohan da Aymah ta kanannaɗema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. “Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ”.
       Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ɗin da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu............✍

Likita bokan turai😉😜.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 43

............Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
        A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
     Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata.
Chapter 101 · 0% Book details