Sashe 190
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da Nu'aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser ɗin. Dan yanda suke takun saƙa da Abdallah baisa wani ya taɓa nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saɓani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, ƙarshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu'aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”. “Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina ɗauke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaƙa da hana kaina zaman lafiya danai akan ƙadarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai ƙiyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaɗaitu da son yin ƙyautatawa ga Firdausi koda sau ɗaya ne a rayuwata”. Kuka yaci ƙarfinta da tari. Yanzu kam gaba ɗaya ta cire ɗan-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da ƙyar sannan ta cigaba da faɗin, “Na roƙi Mustapha ya rufe zancen ciwona harga ƴaƴana saboda banason ɗagama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaɓasa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuɓutar Nu'aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoɓo na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoɓi shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaɗaitama Rabi kaima Nu'aymah zoɓon ɗaki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faɗoma Firdausi zan ɗauki cucumber ɗin. Tana fita na zuba maganin. Ina laɓe ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu'aymah zoɓo sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu'aymah tace bazatasha zoɓon ba na shiga damuwa. Inata ƙulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen ɗin ta ɗaura shayi. Dabarar bugar glass ɗin Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta ɗauke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leƙo, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laɓe jikin window ɗinta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaɗe gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na ɗauki Yoohan da Nu'aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu'aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuɓutar da Nu'aymah daga sharrin Lurwan akan kwaɗayin dukiyar mahaifinta...............✍