← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 211

Sashe 7

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Hajjo tace, “Nifa gaskiya har yanzu ban yardaba sai naji ta bakin Zainabu, ko naga wata shaida da zata tabbatarmin da cewar guduwa tai da kanta. Kowafa yasan yanda Zainabu keson Abdallahi a gidan nan tunma bata san kantaba, bata tashi nuna mana bata sonshiba sai daren da za'a ɗaura mata aure da shi. Waye ya kawo wannan takardar? A ina kuma ya ganta?”.
        Nanah tace, “Hajjo nice na kawo, abayan Windown ɗakinsu na gani an ajiye, kuma harda kayantama a ƙasa”.
        “Muje na gani”. Cewar Hajjo tana miƙewa. Sauranma duk tashi sukai suka bita. Kamar yanda Amal ta faɗa haka suka taras, hardama ƙarfen zif ɗin akwati da alamu ya nuna ɓallewa yay wajen rufewa ko buɗewa.
      Maigadin gidan baba malam yasa aka kira masa, aka tambayesa ko yaga fitar Nu'aymah a gidan?. Yace shikam bai ganiba, dan tun sha ɗaya da kwata ya rufe gate ma, kuma babu wanda ya sake shiga da fita.
       Omar ne ya bada shawarar a duba ta ƙaramin gate na massallaci to. Babu musu akabi shawararsa, da yake yau da asuba ta babban gate duk su baba malam suka fita massallaci sai ga sayin takalma an gani dana akwati. Ƙaramin sayi na mace, sai babba da alama ta nuna takalman mazane, sai sayin jan akwati dake biye da sayin takalman har wajen massallaci, sai dai kasancewar akwai kwalta a titin layin sai ba'aga inda sayin ya tsaya ko ya nufa ba.
       Sun dawo cikin gida ana taraddadai saiga wani yaro riƙe da wayar Nu'aymah acewarsa cikin filawoyin massallaci ya gani.
      Amsar wayar Abba Musbahu yayi aka hau dubawa bayan anba Adawiya ta cire lock ɗin dan ita kaɗai ta sani. Ana buɗewa a kan WhatsApp aka samu wayarma, cikin kuma inbox ɗin wani datai saving da suna (Sweet Ameer). Scrolling saƙwanin Abba Musbahu yayi ya koma har can farko ya fara karantawa.
     Gaba ɗaya hirarrakine tsakanin Nu'aymah da Ameer kuma ta soyayya harma da alƙawarin auren juna kota halin ƙaƙa. Har zuwa saƙon ƙarshe-ƙarshe da duk ya zam na ƙulla yanda zasu gudu ita da shi.
     Zuwa yanzunkan kowa jikinsa yayi sanyi, Umm da baba malam sai faman haɗiyar zuciya suke na ɓacin rai, duk da zuciyar Umm sam taƙi gaskata gaskiyar wannan al'amari, dan tafi kowa sanin wacece ɗiyar tata da halayyarta harma da tarbiyyar data bata. Babu abinda Nu'aymah ke ɓoye mata a rayuwa, dai-dai da hira idan tayi ita da Abdallah saita sameta har ɗaki ta bata labari, daga ƙarshe-ƙarshen nan nema take ƙwaɓarta dan kartaje bayan sunyi aure tace zata cigaba dayin hakan. Abinda ya tsoratata a zancen shine sunan Ameer, dan lallai kusan sau huɗu Nu'aymah na kawo abu tace Yah Abdallah ya aiko mata ta hannun abokinsa Ameer, kuma gaba ɗaya saƙwanin har gida yake zuwa ya sameta ya bata. To gashi kuma shi Abdallah yace baida abokima Ameer ɗin balle ya aikosa wajenta. ‘Innalillahi wa'inna ilairraji'un. Mike shirin faruwa da ɗiyarta ne haka? Ya ALLAH ka bayyana abinda ke ɓoye akan wannan al'amari dai cikin sauƙi’. Wannan sambatun Umm keta famanyi a cikin ranta zuciyarta na mata zafi da ɗaci. Yayinda ɓacin ran da take gani shimfiɗe a fuskar mijinta ke sake tada mata hankali.

       A yanzu kowa ya yarda Nu'aymah guduwa tayi, sai dai Hajjo dai bata daina faɗin cewar tana wasiwasiba, dan da cataima sai dai idan Ameer wani abu yayma Nu'aymah harta bishi. Babu wanda yabi takan zancenta dan suna ganin akwai ruɗun tsufa tattare da ita.
          Ana cikin wannan taraddadi Abdallah yaci karo da saƙon Nu'aymah a wayarsa wanda baisan da shiba. Danshi tunda yay mata magana yaga bata bashi amsaba ya jiya wayar bai sake bi takantaba, tunda da safe kuma an tashi da tashin hankalin rashintane.

          Assalamu alika.

    “Yah Ab kayi haƙuri karkaga ban maka adalciba, kasan shi so tsuntsune, gobe ya tashi kan wannan ne ya koma kan wancan. Tabbas na soka a baya kamar babu wasu maza a duniya sai kai kaɗai. Kaima kasan akwai ƙuruciya a kaina a lokacin, shiyyasa sam na kasance bansan Zaɓin daya dace dani. Yanzu kam idanuna sun buɗe ras, zuciyata ta samo zaɓinta. Nasan kozan shekara faɗama iyayenmu bana sonka yanzu bazasu yardaba, bakuma zasu fahimceniba sai sun aura min kai, shiyyasa na zaɓi guduwa, idan komai ya lafa saina dawo a auramin zaɓina. Kaima dan ALLAH ka nema dai-dai kai ka aura kaji. Na barka lafiya Yayana, ina fatan bazaka zauna jirana ba, kuma bazakayi fushiba.

         Ƙanwarka Nu'aymah Sooraj Hashim.

      Cikin matsanancin fushi Abdallah yay wurgi da wayar hawaye na sulalo masa saman kumatu masu masifar zafi, jikinsa sai rawa yake na ɓacin rai. Dama shi haka yake bai iya fushi ba.
        Duk kansa samarin sukayi suna tambayar lafiya?. Kansa ya dafe yana cigaba da kukansa kamar wani yaro ƙarami. yace, “Wlhy ina sonta, amma miyasa Nu'aymah zatamin haka? Minene aibuna dan ina ƙaunarta. Wlhy bazan iya auren kowaba sai ita”.
        A tsawace Baba malam ya miƙe yana faɗin, “Dole ne kuwa ka auri watanta a yau ɗin nan Abdallah, ita bata isa kunyatamu ba, bayan mun tara mutane. Inaso daga yau, daga yanzu ka manta da Nu'aymah a cikin zuciyarka har abada kamar yanda nima na manta da ita matsayin ɗiyar cikina”.
          Cike da tashin hankali kowa yake kallonsa a falon, dan kowa yasan dama Baba malam yanada zuciya, sannan kaifi ɗaya ne shi, idan yace A dolene A ɗin za'abi, idan yace A'a shima dolene abi............✍

Wannanfa shi ake kira da gaba kura baya sayaƙi😥. Nu'aymah kizo ki bamu gaskiya batu ko masan ina matsalar take ne?.😭

  ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_Typing📲_*

*_SARAN ƁOYE!!_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

Free page😋

No. 4

WAIWAYE ADON TAFIYA.

          Malam Hashim musa shine asalin mai gidan. Babban malami mai tarin ilimi daya taka rawar gani a duniyar musulunci. Yasha gwagwarmaya ƙwarai da gaske na ganin ilimi ya yaɗu da faɗaɗa cikin al'ummarmu ta nagartattun hanyoyi.
       Kasancewar yayi gwagwarmayar rayuwarsa ta neman ilimi lokacin ƙuruciya a garin Jibiya ta jihar katsina sai ake kiransa da suna ɗan jibiya.
        Matan Malam Hashim ɗan Jibiya biyu kacal a duniya. Zainabu (Hajjo) sai Zulaiha.
     Ƴaƴansa Huɗu duk maza, kuma dukansu Hajjo ce ta haifesu, dan har Zulaiha ta koma ga ALLAH bata taɓa ko ɓatan wataba.
        Sooraj mahaifin su Nu'aymah da ake kira da Baba Malam shine babban ɗansa. Sai Rudwan mahifin Abdallah wanda shima yanada iliminsa sosai, amma shi yana kasuwanci ne, duk da suma su Baba malam suna kasuwancin. Sai Mustapha Mahaifin su Adawiya, shima dai malamine dan tare da Baba Malam suketa ƙoƙarin cigaba da ginin da mahaifinsu ya bari na yaɗa ilimi. Sai auta Musbahu, shine mahaifin su Yusrah, shima dai malamine, yanama addini hidima yana kuma business.
         Kamar yanda kukaji a farko gidansu Nu'aymah gidan manyan malamaine sananne, sannan kuma ƴan kasuwane na gaske, dan har sunada kamfanin dake sarrafa Mangyaɗa da kuma sabulu, suna kuma sufurin kayan masarufi sosai ta hanyoyi daban-daban cikin farashi mai sauƙi duk daga kamfaninsu mai suna ƊAN JIBIYA FAMILY.
          Kamfaninsu sanannen kamfanine dake da haja a lungu da saƙo na ƙasarnan sabida sauƙin kayansu. Sannan kuma sanannun malamaine da duniyar musulinci ke alfahari dasu a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sunada manyan makarantun da ake koya ilimin addini zallah a cikin kano dama wasu jihohi maƙwafta, suna kuma da gidan marayu nasu na kansu da suka assasa domin ladan ya ringa isa zuwa ga mahaifinsu da ALLAH yayma rasuwa kusan shekaru ashirin da suka shuɗe.
     Family ne da alkairansu a bayyane yake wa duniya duk da suna ƙoƙarin ɓoye kansu dan kar asan sune keyi. To amma masu iya magana kance alkairi dankone baya faɗuwa ƙasa banza.

           Sooraj (Baba Malam) shine ya zame musu tamkar mahaifi bayan rasuwar Malam Hashim, ya kama ƴan uwansa ya dunƙule kansu waje ɗaya babu mai jin kansu sai ALLAH. Suna ƙaunar junansu matuƙa da mutunta juna. Komai nasu sai sun nema shawararsa kamar yanda shima idan zaiyi wani abu sai ya tarasu ya nema tasu duk da suna a ƙasa dashi.
       Tun mahaifinsu nada rai suka gina wannan gida daya kasance gari guda, dan malam Hashim ya mallaki filin ne tun anguwar babu wasu gine-gine kirki, da farkoma noma yakeyi a filin, sai da yaransa suka fara tasawa ya zagayesa yay massallaci da islamiyya, ya kumayi ƙaramin gida a ciki yana zaune da iyalansa. Bayan rasuwarsa arziƙin kasuwancinsu ya ƙara haɓaka sai suka gyarashi aka faɗaɗa massallacin da Islamiyyar, suka kuma ginama kowa sashensa inda zai zauna da iyalansa. A hankali harkoki na ƙara haɓaka musu suna sake gyara gidan har ALLAH ya kaisu ga wannan matsayin suka kasance cikin tsakkiyar birnin kano.
Chapter 7 · 0% Book details