← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 211

Sashe 172

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Sosai Nu'aymah batajin daɗi. Dan ma Juliet tsaye take sosai wajen kula da ita. Dan ta fahimci laulayin ciki takeyi. Sosai taji tausayin yarinyar ya kamata. Yaushema aka gama rainonta da za'ace itama ta samu ciki. Gaskiya tana mamakin ganganci irin na baƙar fata. Kasa haƙuri tayi sai da taima Omar wannan complain ɗin. Shiko yay dariya tare da mata faɗaɗɗen bayanin data gamsu, harta koma bin Nu'aymah da addu'ar fatan sauka lafiya.
              Duk da Aymah tanata ɓoyema kowa halin da take ciki na ciwon da ita ɗauka take Thypoid ɗinta ne ya motsa yau dai ta tonama kanta asiri batare data farga ba. Dan suna waya dasu Umm da Muhammad ya takura a kira a kirata ya sanar mata yayi sabuwar Aunty. Bayan sun gaisa da Afrah da Muhammad ɗin Umm ta amsa wayar suka gaisa itama. Cike da shagwaɓa Nu'aymah tace, “Umm Yah Yoohan yazo?”.
      “Oh dama ya shigo ƙasar?”.
“Eh Umm. Yaufa kwanansa uku”.
      “To Abbanki ya manta, ni koma maganar bamuyi da shi ba. Amma kinsan shi da uziri, nasan zaizo insha ALLAH”.
       “Umm idan yazo kiyi min yajin daddawa da farin yaji, da ɗan wake, da alawan madara, da iloka. Da fara. Da manja. Da aya suyan gishiri. Da.......”
       “Oh ni Firdausi wannan lissafin kumafa Nu'aymah?”.
       Baki ta tura gaba kamar tana gabanta. “Umm duk so nakeyi fa dan ALLAH”.
       Ɗan jimmm Umm tai na hasashe. Sai kuma tace, “Niko Nu'aymah ai period ɗinki ya dawo ko?”. Tai mata tambayar cike da salon bugar ciki irin na manya.
      Zimbir Nu'aymah ta miƙe zaune. Dan ita kuwa man kanta ma ya tsiyaye tas ta shafa'a da zancen rashin ganin period. Ai idanma bata manta ba rabonta da jini tun na abinda ya faru. A randa ta fara jin alamun zuwansa kuma Accident ɗin nan ya faru suka wuce Austria. Daga nan bata saniba tayi ko batayi ba? Tunda bata cikin hayyacinta........
      “Kinajina kuwa Nu'aymah?”. Umm ta katse mata tunani.
    Da ɗan rawan muryan shiga ruɗani tace, “Umm wlhy ni tun na lokacin nan ban sakeyiba. Na shiga uku Umm na kamu da wani ciwo ko?”.
      Dariya ce taso kufcema Umm, amma sai ta gimtse da sauri tana saurin faɗin, “A'a lafiyarki ƙalau. Inaga saboda kinyi wancan rashin lafiyarne shiyyasa. Zanma mijinki magana ya baki magani”.
     Cike da sanyin murya tace, “To Umm. Amma dan ALLAH ki haɗamin duk abinda nace idan Yah Yoohan zai taho yazomin da su. Harda garin dawa na tuwo fa Umm. Da daddawa da kuka da bushashshen kuɓewa dan ALLAH”.
         “To zan haɗa miki duka insha ALLAH. Amma kayan kamar zasu masa yawan ai Nu'aymah”.
     “Ni dai Umm dan ALLAH ki taimakeni. Wlhy duk banason abincin garin nan yanzu. Coffee kawai nake iya sha sai gasashen kofi. Amma sauran abincin da naci sai nayi amai. Abincin Austria yafi na nan min daɗi”.
       Umm dai na murmushi ta amsa mata. Daga haka sukayi sallama dan Juliet jiranta suke zasu fita shagon shan coffee ɗin na ƙa'ida. Itama taɗan motsa jiki daga can.

____________★★★

         Tunda ya kawosa hotel ɗn ko sau ɗaya bai tambayesa miya fruba. Shi kuma baice dashi komaiba dan ransa a ƙololuwar ɓace yake. Yadda Al-qur'anin nan yafi komai zafafa masa zuciya. Dan har yanzu fushinsa yaƙi sauka. Daya rufe ido dan yai barci sai ya hango Qur'an a ƙasa a yashe. Daga ƙarshe dai har dasu yin hawaye.
      Sanin halinsa idan yay fushine ya saka Omar yanke shawaran kiran Nu'aymah. Juliet ya turama text message dan taja ra'ayinta.
       A lokacin basuyi ko mintuna biyar da shigowa gidan ba. Aymah na kwance a falon saman tiles idonta a rufe. Sai dai ba barci takeba. Hasalima tunanin Yoohan takeyi dan rabon da suyi waya tun jiya da yace mata zai koma Abuja daga kd....
      Gyaran muryar da Juliet tayine ya saka Aymah buɗe ido tana kallonta. Juliet ta ɗaga mata gira ɗaya tana murmushi, yayinda duk hannayenta ke akan cikinta tana shafawa. “Da zaman tunani ai gara kiyi kiransa” tai maganar cike da tsokana. Murmushi Nu'aymah tayi da gyara kwanciyarta tana fuskantar Juliet ɗin. “Ke dai faɗa mana gaskiya. Ko kina kewar Yah Umar ne ni zaki nanamin?”. Kusan a tare suka kwashe da dariya. Juliet ta miƙe tana faɗin, “1-1 kenan. Ni bara naɗan watsa ruwa na kwanta”.
        Juliet na shigewa Aymah ta sauke numfashi. Cike da son jin muryarsa kuwa ta lalubo hotonsa a wayarta tana kallo. Kamar kuma an tsikareta sai kawai tai kiransa. Shigowar kiran Aymah yayi dai-dai da sake sakkowar hawayen Yoohan. Dan ji yake kamar zuciyarsa zata ƙone. Sam dukan da yayma Gebrail ɗin bai wadacesaba....
     Kamar bazai kula wayar ba sai kuma ya buɗe idanu a hankali. *_My Sweet girl_* daya ganine ya sakashi ɗauka a kasalance. A kunne kawai yasa batare da yayi magana ba. Daga can Aymah ta sauke sassanyan numfashi. Sai dai itama batayi maganarba. Sun share kusa sakan goma sannan ta ƙara sauke numfashi da faɗin, “My boo yau miskilawan ne a kusa?”. Shiru baiyi maganaba. Hakan yasata fahimtar akwai damuwa. Dan a ɗan zamansu ta fara fahimtar wasu da yawa halayensa. Musamman fushinsa da farin cikinsa. Kwanciya ta gyara tana lumshe idanu. Cike da nutsuwar data ɗan farayi na wahalar ciwo tace, “Waya taɓa ɗan lelen Abba ne? To lallai ya nema wajen ɓuya tun kafin na kira Abba na sanar masa ɗan lelensa na fushi da kowa har Silly girl ɗinsa”.
       A bazata murmushi ya ɗan kufce masa. Sai dai idanba lura kayi ba bazaka taɓa fahimtar yayinba. A hankali yace, “Parrot, ke dai bakison barin bakin mutane ya zauna shiru”.
     Baki ta kumbura cike da sakalci tace, “Ai yanzu parrots ɗin biyu ne. Dan kaima ALLAH ka shigo tawaga Yah Yoohan”.
     “Silly girl”.
Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa.
      Murmushi tayi mai faɗi tana lumshe idanu. Sai kuma ta dai-daita muryarta, cikin nutsuwar da inta gadama zaka sameta da ita tace, “I'm so sorry My Handsome. Nifa kaga idan aka bani haushi a gidanmu mi nakeyi da?”.
       Yace, “Uhm-uhm”.
Sake gyara kwanciyarta tayi tace, “Sai in ɗauki Al-qur'ani naita karatu. Zakaga inata kuka a farko, kafin wani lokacin kuma sai na samu nutsuwa na cigaba da karatun da nishaɗi. Cikin amincin ALLAH bana ajiye Qur'anin nan sai zuciyata tamin sanyi”.
      Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Murya da matuƙar sanyi yace, “Zeeynab I love you. Ke ta dabance a rayuwata”.
      Murmushi tayi kawai. Kafin a hankali tace, “Thanks you Uncle Boo”.
     Kansa ya jinjina mata a hankali. Sai kuma ya yanke wayar batare da yace mata komaiba. Omar dake gefe yana jinsa sai dariya yake dannewa. Batare da Yoohan ya kallesa ba yace, “Umar Al-qur'ani”.
      “Okay bara na kawo maka a mota”.

  Cikin mintuna ƙalilan Omar ya dawo masa da Qur'ani. Tashi yayi yayo alwala ya dawo ya zauna. Cike da bin shawarar Aymah ya fara karatu. UBANGIJI mai Rahma mai jin ƙai sai ga Yoohan ya sami nutsuwa cikin lokaci ƙanƙani. jiyay tsoron ALLAH ya ƙara ratsashi. Ya shiga jeramasa kirari da godiya bisa koyarwar Nu'aymah.
      Umar ma yaji daɗin ganinsa ya dai-daita a lokaci ƙan-ƙani, dan haka yaje ya samo masa abinci har suka ɗan zauna suka tattauna akan abinda ya farun. Omar yaji a ransa ba Gebrail bane ya shiga ɗakin Aymah. Ya taka sawun ɓarawone kawai da kuma zafinsa da Yoohan ɗin yakeji dama. amma sai yay shiru baice komaiba. Dan yafi buƙatar Yoohan ya fahimci wanene mahaifinsa da kansa.

______________★★

          A gidan su Yoohan kuwa uffan papa baiceba game da dukan Gebrail da aka kai asibiti a sume da Yoohan ɗin yayi. Su Uncle Mike ne ma keta faɗa da son jin miya kawo rikicin? Sai dai amsa ɗaya suke samu. Shine kowa bai saniba. Dan iya abinda idanunsu ya gani kawai suke faɗa jama'ar gidan.
     Har zuwa lokacin da labarin farfaɗowar Gebrail ɗin yazo kunnensu papa dai yaƙi yace uffan. Sai da daddare bayan sunje sun duba shi a asibiti bisa tursasawar mama debora da maman madam Chioma da yau sukaci masifa har bakunansu sukai tsaho. Bayan barowar tasu asibiti ne papa ya kira Baba malam da shi har yanzu ma baisan Yoohan na ƙasar ba. Dan sunata shirye-shiryen bikin sauka da auren yaransu na gidan marayu nanda bayan salla babba. Yayi Busy da yawa. Rabonsa dayin waya da Yoohan tun yana Oman.
      Yasha mamakin ganin kiran papan. Amma sai ya ɗaga yana ambaton sunan ALLAH. Baiyi sallama ba, sai cewa da yay, “Barka da dare Pastor Goshpower. Yau kaine ka tuna da Soorajidden bin Hashim?”.
      Wani wawan tsaki papa ya sauke a jere. Batare da jiran cewar baba malam ba ya fara zazzaga masifa. “Kai ɗin banza da zan ɗauki waya na kiraka. Gargaɗi na kira na maka a karo na farko kuma na ƙarshe. Ka rikitamin yaro gaba ɗaya ya fita hayyacinsa. Sai yanzu na gama fahimtar manufarka akan ɗana. So kake ka maida minshi ɗan ta'adda shiyyasa ka aura masa wannan shegiyar ƴar taka mai zuciyar dutse? To wlhy Sheikh Sooraj kafin kaga bayana nine zanga bayanka. Sanna kayi gaggawar sakarmin kurwar yaro. Ka kuma saka ya maido maka ƴarka gida tun kafin lokaci ya ƙure maka. Idan ba hakaba na rantse saina halakata da hannuna kafin kaima na halakaka...”
     Kafin baba malam yace wani abu papa ya yanke wayar. Nannauyar ajiyar zuya baba malam ya sauke kawai yana girgiza kansa. a gaba ɗaya kalaman papa babu wanda ya bashi tsoro. Abinda ya fahimta kawai shine cikin fushi yake. Duk da kuwa yasan papan zai iya aikata duk abinda ya lissafa masa. Abinda kawai ya sakashi a ruɗani shine, ‘Miya faru?’.
      Ganin bashi da mai bashi amsa sai kawai ya ajiye tunanin ya cigaba da harkar gabansa.

__________★
Chapter 172 · 0% Book details