← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 211

Sashe 166

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Sallar la'asar data riskesu a hanya sukai ƙoƙarin gabatarwa. Bayan sun idar Aymah ta fara wucewa kitchen ɗin. Kayan da duk suka siyo ta fara buɗewa tana ajiye komai inda ya dace da zamansa. Tana kammalawa kenan ta ɗakko tukunya zata ɗauraye Yoohan ya shigo waya manne a kunnensa yana magana. Idonsa a kanta ya dafe kitchen cabinet ɗin dayin ɗan tsalle ya haye samansa ya zauna. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta ita dai, dan ta fahimci wayar tasa mai muhimmanci ce.
         Sai da ta gama wanke duk abinda zatai aikin da shi sannan ta jawo rigan girki ta ɗaura. Dai-dai kuwa da kammala wayar Yoohan. Sauka yay ya nufeta da ɗan alamun gajiya tattare da shi. “Wlhy duk kin gajiyar da ni Sweet girl. Inata murna yau zan huta a gida bazanje asibiti ba. Amma sai da kika sakani yawo”.
        Hararsa ta ɗanyi tana riƙe ƙugu da duk hannayenta. Cike da rigima tace, “Uhm uhum uhmyy. Wani aiki sai rago dai wlhy”.
      “Oh nine ma ragon?”. Ya faɗa yana wani hangame baki.
      Gira ta ɗage masa tana wani juya idanunta manya masha ALLAH. Tace, “Na gaske ma”.
         Wata dariyar mugunta yayi yana matsota, da sauri ta manne jikinta da cabinet ɗin tana marairaice fuska. Kafin ta samu damar magana yazo dab da ita. Matseta yay a wajen ya hanata ko guntun space yana wani ɗage gira sama da ciskule fuska. Hannayensa na a gefe da gefenta ya kai fuskarsa gab da tata suna shaƙa da busama juna numfashi. Ga idanunsu cikin na juna kowa kwarjini da sirrin na ɗan uwansa na ratsa masa jiki da zuciya. Da wani irin karya harshe na ma'abota shauƙin soyayya yace, “Yarinya kema kinsan ni ɗin ba rago bane. Amma zan sake tabbatar miki kuwa a yau ɗin nan da iznin ALLAH. Sai wannan bakin rakin naki ya kai titi saboda neman agaji”. Ya ƙare maganar da ɗallar laɓanta da yatsunsa biyu.
           Da sauri ta dafe bakin hawaye na cika mata idanu. Ta kai hannu bisa damtsen hannunsa yay saurin kaucewa yana wata shaƙiyyar dariya ƙasa-ƙasa dan yasan muguntar da zatai masa.
     Kumbura tayi tai fam. Cike da haushi ta kama rigar zata kunce ya riƙe hannunta. “Ai yarinya baki isa ba. Kin riga da kin yarda da game ɗin nan dan haka girki dole ne”.
       Baki ta tura masa tana kwaɓe fuska da faɗin, “Na fasa game ɗin. Girkinma sai dai kay.....”
        “Hhh daga baya kenan hajjaju Zenaba ƴar farar bakanuwa ƙyaƙyƙyawa”.
    Yay maganar da riƙota hannunta ya maida ɗaurin rigar yana mata wani dariyan iya shege a gefen wuya.
        Gaba ɗaya neman susuta mata jiki yake da salonsa. Saurin zame jikinta tai ta koma gefe tana faɗin, “Ai inba yau a kwai gobe indan ALLAH ya kaimu. Ka ɗauka yau ɗin kaine a sama ni a kwana. Sai dai kuma zaka dawo kwanar ne ni na koma ciki...”
   Ta ƙare maganar da wani salo tana kashe masa ido ɗaya.
       Da gasken gaske saƙonta ya iso inda ta turosa. Dan gaba ɗaya jijiyoyin Yoohan suka saki dama kwana biyun nan rakinta ya sakashi ɗan bata ƙafa. Lip ɗinsa ya cije da ƙarfi yana wani jan ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba ya jawo wayarsa ya miƙa mata. Yana mata wani kallo ƙasa-ƙasa. Amsar wayar tayi da tura baki gaba tana ƙunƙuni. Ta kalli hoton abincin da ƙyau sannan ta ɗan dubesa ta ɗauke kanta tana murmushi.
        Kujerar dake gaban tebir ɗin tsakkiyar kitchen ɗin yaja ya zauna. Ya wani miƙe ƙafafu da bajewa da ƙyau, irin fa shine boss ɗin nan.
         Nu'aymah bata sake bi ta kansa ba ta fara ƙoƙarin ɗaura girkin tana addu'a a ranta da fatan yin komai yanda ya kamata.

         Ko ɗauraye cokali bai tayataba, tunda ta fara. Yama ɗauke kansa gaba ɗaya daga gareta sai danne-dannen waya yake yi hankalinsa kwance. Duk da kuwa a baɗini duk wani motsinta nakan idonsa ne.
       Kasancewar ta kwana biyu batai girkin ba yasa takeyin komai cike da ɗoki. Kafin cikar awa ɗaya kuwa sai ga ƙamshi ya gama gauraye kitchen ɗin gaba ɗaya har falo. Shi kansa Yoohan shaƙa yake cike da jin daɗi da kwaɗayin son cin abincin. Tsaf ta kammala komai ta gyara kitchen ɗin da ɗauraye duk abinda ta ɓata duk yana zaune dai yana kallonta. Abincin ta zuba a plate tare da ɗan ɗora kwalliyar data ƙara ƙawatashi ta ɗauki cokali tazo ta dire gabansa tana wani shan ƙamshi.
      Idanu ya tsirama abincin dake ta tashin ƙamshi mai saka yunwa. Kafin ya ɗago ya kalleta. Ɗauke fuskarta tai gefe murmushi nason kufce mata. Sai kuma taje ta tsiyayo apple and orange juice ɗin data haɗa a glass cup tazo ta ajiye shima a gabansa. dai-dai yana gyara zamansa. Bai fahimci minene ba, amma yaga sanda take markaɗa abu dai. Cokalin ya ɗauka ya ɗiba abincin kaɗan ya kai bakinsa tare da yin bismilla. Duk da daɗin daya ratsa masa baki da kunne da ƙwaƙwalwa sai ya wani yamutse fuska harya haɗiye. sake ɗiba yay yaci nanma fuska a yatsine. Aymah dai na kallonsa baki a ɗage dan tasan wlhy ƙarya yake yace abincinta babu ɗanɗano.
       Cike da son danne dariyarsa na ganin yanda tai da fuska ya kai lauma ta uku. A hankali ya lumshe idanunsa da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Sai kuma yay mata alamar jinjina da kashe ido ɗaya ya haɗe yatsunsa biyu👌🏼 alamar komai zam.
       Itama ajiyar zuciyar ta sauke a hankali da juya bayanta idanunta na cika da ƙwallar farin ciki dajin ƙaunar Umm ɗinta mai tsanani. Dan itace ta maidata tauraruwa wajen tsayawa akanta tun tana ƴar mitsitsiyarta. Ƙanƙantarta baisa Umm ta taɓa rangwanta mata ba akan aikin gida duk da sunada mai aiki. Kamo hannunta da Yoohan yayi ya ɗora bisa cinyarsa ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
      “K ta dabance Cutie”. Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa cikin rigarta.
      Idanunta ta lumshe itama da kai hannunta ta shafo kwantaccen sajensa mai laushi dake cin kuɗaɗe wajen gyaransa. Kiss ya bata a wuya tare da ɗagowa ya kamo fuskarta ya manne bakinsu waje ɗaya. Bata hanashi ba. Dan ya riga da ya koyar da ita wannan sirrin.
      Sai da taga wasan na neman canja salone ta ƙwace kanta da ƙyar tana masa dariya. Sai ko ya ƙwaɓe fuska tamkar zaiyi kuka dan da gaske ya zurma da yawa.
         Plate ɗin abincin ta ɗauka ta ƙaro musu tare da ɗakko juice ɗin gaba ɗaya shima. Sai lokacin Yoohan ma ya ɗauki wanda ta fara kawo masa yasha yana sauke ajiyar zuciya. Cike da ɗage gira yace, “Kin haɗu a abubuwa da dama Hausa girl”.
     Murmushin jin daɗi tayi, dan har ranta tanajin nishaɗi idan ya kirata Hausa girl. Tana son yarenta tana alfahari da shi fiye da zaton mai karatu. Tanaji a ranta komi ta zama dolene duniya tasan itaɗin ƴar ƙabilar HAUSA ce gaba da baya.
       Sunci abinci cike da farin ciki, yana bata tana bashi har suka kammala. Da taimakonsa yanzu kam suka tattare wajen suka fice a kitchen yana faɗin ta zaɓi ƙyautarta.
    Ita dai dariya take masa kawai. Sai da suka fito falo ya zauna da ita a jikinsa sannan ta dubesa tana murmushi. “Soyayyarka da kulawarka a gareni kaɗai ta isheni tukuyci my sweet boo”. Tai maganar cike da salon da take ƙara ƙwarewa wajen koya a hannun Aunty Hajarahn mai sonta da ƙaunarta.
      Rungumeta yay a jikinsa ƙaunarta na sake ratsasa. A ƙasan ransa kuwa godiya yakema ALLAH da samunta tare da jin girma da darajar iyayenta a cikin ransa. Fatansa ALLAH ya basu ƴaƴa masu albarka suma su basu irin wannan tarbiyyar tata abin son kowanne ɗa nagari.

__________★★

      Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa ga Nu'aymah da Yoohan cike da farin ciki da tattalin juna kasancewar har yanzu a amarci da ɗokin juna suke. (Kunsan shi farkon aure dama haka yake. Za'aita nunama juna soyayya cike da zalama. Ku kanku jin kanku kuke tamkar babu ya ku a duniya. Sai rayuwa ta fara nisane abubuwa ke fara tsauri. Sai dai da yake UBANGIJI mai rahama ne da jinƙai sai kaga hakan baya hana a nunama juna soyayya da kulawa koda saɓani na shiga. Duk da jarabawa kan ratsa a zamantakewar ma'aurata kaga matsalolin nata yawaita fiye da hasashe. ALLAH ya cigaba da zaunar damu a gidajenmu lafiya tare da mazajenmu da ƴaƴanmu da abokan zamanmu baki ɗaya mata sarakunan gaskiya a fadar gaskiya😘😍🤗).

      Kwansu goma sha uku a U.S Yoohan yay shirin zuwa Oman yin wani aiki na kwana biyu. Daga can kuma zai wuce Nigeria insha ALLAH.
         Yasha taɓara kuwa a wajen Aymahn sa. Dan kuka sosai ta dinga yimasa akan saita bisa. Da ƙyar ya lallaɓata da tabbatar mata Juliet matar Omar (Rich) tana zuwa daga 9ja a daren yau. Idan ma batason zaman anan gidan ita kaɗai sai ya kaita gidan Juliet ɗin ta zauna a can harya dawo.
     Da ƙyar ta amince kuwa. Shima sai da aka haɗa da hajjo wajen lallashi. A ranar kuwa Juliet ɗin ta iso. Sun tarbi juna da mutuntawa. Kuma har cikin zuciya Nu'aymah taji zata iya zama tare da Juliet ɗin. Musamman yanda taga itama Juliet ɗin na nuna mata ƙauna da yaba komai nata tana sake taya Yoohan murna. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana bin mutuniyar tasa da kallo ƙasa-ƙasa.
      Washe garin da zai wuce sai da ya rakata gidan Juliet sannan ya wuce ya barta da kewarsa kamar yanda shima ya tafi cike da tata kewar.

★★★★

          Tamkar jira jikin Aymah keyi Yoohan ya wuce ta fara ƙananun ciwuka. Kullum da zazzaɓi take wayar gari, zuwa ƙarfe ɗaya na rana kuma sai ya gudu. Tun Juliet bata fahimtaba harta fahimta saboda shaƙuwar dake ƙara shiga tsakaninsu da Nu'aymah. Dan Juliet tanada sauƙin kai sosai. Bata taɓa kuma nuna ƙyamar addinin Nu'aymah ba koda kuwa akan fuskartane. Wani lokacinma idan Aymah na salla ko karatun Al-qur'ani har zama take taita kallonta. Dan itama zuwa yanzun tasan mijinta Omar (Richard) ya musulinta............✍

*_Gaba ɗaya na manta yau monday fa😥🤦🏻🏃😂_*

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Chapter 166 · 0% Book details