← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 211

Sashe 68

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

            Tana shiga toilet ɗin ta maida ƙofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ƙofar ta fashe da kuka maiban tausayi. A ranta tana faɗin yaya zatai da wannan abin kunya da takaici da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da baya bautama ALLAH. Baisan idan ya saɓama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai taɓa ambaton ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine yau akan nata. ‘ALLAH ya isa bazan taɓa yafe makaba’. Ta faɗa a fili tana sake rushewa da kuka. ‘Na shiga uku ni Zainab, ni.........’
       “Nu'aymah!”. Muryar Umm ta hanata ƙarasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
      “Nu'aymah wai baƙya jinane?”.
Umm ta sake faɗa tana matsowa jikin bayin.
      Da sauri Nu'aymah tai gyaran murya. Kafin ta miƙe da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ɗaya taima mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar tata sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito.
      Haɗa ido sukai da Umm da ke a tsaye tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ƙasa da faɗin, “Umm yi haƙuri, ALLAH toilet ne”.
         “Toilet ko kuka?”.
Da sauri ta ɗago ta kalli Umm ɗin. Muryarta na rawa tace, “Umm toilet ne ALLAH”.
      “Toilet ɗin ki kai ma kuka kenan?”.
Baki taɗan tura gaba, “To Umm gudawa fa ce”.
        “Mtsoww! K dai bansan randa zaki bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani ba”.
         “Kiyi haƙuri Umm”.
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka ƙureta, sam bata ƙaunar halin banza.
         Duk da tana buƙatar kaɗaici haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin tufƙa da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ɗaya).
     Tana zama aunty Rafi'a tace, “Hummm! Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen daɗi haka?”.
     Gaban Nu'aymah yay mugun faɗuwa. Ta ɗago da dauri tana kallon aunty Rafi'a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta buɗe baki zatai magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
       Wata muguwar ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke a ɓoye. Tare da saurin miƙewa zumbur ta nufi su Nanah ta rungume.

           Zuwan su Nanah gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin yaƙi barin ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen shaƙar ƙamshin a jikin Nu'aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa da wannan ƙamshin ba. Amma sai bataima Nu'aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.

____________________

       Ya jima zaune matuƙa akan toilet sit kafin ya miƙe ya fara zame jiƙaƙƙun kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito sanye da Bathrobe fara mai ɗan tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa kaɗan. Towel ƙarami ya riƙo a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
        Kallo ɗaya yayma Solomon daya kasa haƙuri ya dawo ɗakin duk da korar da yay masa ya ɗauke kansa. Kan Solo a ƙasa yace, “Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani hali”.
       Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ɗakin. Zama yay cikin ɗaya ya ɗora ƙafafunsa saman table ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
     Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi........
       “Ina buƙatar coffee”. Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
    Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da “Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
      Ba'afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa sai ga cikin ma'aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
      “Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.
Chapter 68 · 0% Book details