← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 211

Sashe 171

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

............Sun fito har ƙofar gida Muhammad biye da su zai mata rakkiya. Shima Jay ya jashi a jiki da kulawa. Anan ne yake tambayarsa miyyasa yaga yana fushi. Hawaye cike da idonsa yace, “Uncle Please ka bar mana Aunty anan ta zauna. Kaga Aunty N Uncle Yoohan ya gudu min da ita. sai ni kaɗaine a sashenmu. Ni kuma inason na dinga ganina da abokiya kamar Aunty N”.
      Cike da ƙaunar yaron Jay ya sumbaci kumatunsa yana ƴar dariya. Yace, “Oh woow sarkin wayo. inko hakane na maka alƙawarin Aunty Afrah zatazo maka hutu dan tana hutu dama yanzu haka”.
     Cike da ɗoki Muhammad yace, “Uncle yaushe?”.
     Yanda yayi ɗin har saida yasa baba malam da Afrah da Jay dariya. Jay yace, “Karka damu zaka iya ganinta a koda yaushe”.
      Duk da Muhammad yaso jin ranar da zatazo dai sai yayta ɗoki. ya koma cikin gida da gudu ya sanarma Umm.

     Bayan wucewar su Jay da kwana biyu Muhammad ya addabi su baba malam da zancen yaushe Aunty Afrah zata zo? Shifa idan bazatazoba to shi a kaisa gidansu yay hutu. Ganin ba hutu suka samuba shi sai baba malam ɗin ya kira jay da bukatar yaushe Afrah zata zo ɗin. dan sufa an saka musu zuma a baki kuma duk sun ƙagu. Hakan yama Jay daɗi, dan shirinsu na tafiya yanda ya kamata cikin rahamar ALLAH.
      Bai wani ja zancenba yace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kawota da kansa insha ALLAHU. Wannan shine dalilin samun ƙofar shiga gidan su Nu'aymah da Afrah ta samu domin cika aikin ysyarta. Dan haka a safiyar yau kuma lahadi ta tashi da shirin tafiya can zatai zaman wata ɗaya rak insha ALLAHU.

      Sai karfe biyar na yamma Anuwar ya gama shirin kai Afrah kano gidansu Aymah. Dan haka bayan ya kammala shirinsa tsaf ya saka Al-hassan Ya kira masa ita a can sashen Uncle Anuwar. Dan ita acan take zaune kamar yanda little bee ma acan tai rayuwarta har tayi aure. Tsakaninta da sashen iyayenta sai dai tazo gaisuwa kawai ko hira. Amma ita Uncle Anuwar da aunty Nabeelah ne iyayenta. Sauran yaran kuma Miemaa da Abie.
      Tana zaune a falo hankalinta akan lap-top tana hidimarta Al-hassan ya shigo  da sallama. Kasancewar yayima Aunty Nabeelah laifi yau da safe. ta kuma tabbatar masa idan ta kamashi sai ta zanesa sai ya dogare a bakin ƙofar yana kalle-kalle. Daga can yace, “Aunty Afrah kizo Abie na kiranki”. Bai jira ko amsarta ba ya shilla waje da gudu saboda leƙowar aunty Nabeelah dake kitchen dan jin muryarsa da tayi.
     Aiko mi Afrah zatai inba dariya ba. Tace, “Mamma wlhy kin hana auta Sukunin shigowa sashen nan yau gaba ɗaya. Ɗazun ina kallonsa daya hangoki kin fita har faɗuwa yake wajen tiƙar gudu zai shige sashensu”.
     Dariya Nabeelah tayi itama da faɗin, “Ai ya gama gudunsa babu fashi saina ruɗa masa jiki da bulala tunda shi bayajin magana. Iskancin yaron nan baya tashi sai ya ga su Miemaa na gida. To in ALLAH ya yarda shi abin nema da tsokana ya samu a wajensa tunda yasan basa bari a taɓasa”.
      Miƙewa Afrah tai tana dariya da zura Slippers a ƙafarta. “A daiyi haƙuri Mamma na. Bara naje Abie na kirana inaga ya gama kimtsawa”.
      A take mood ɗin Nabeelah ya canja. Cike da damuwa tace, “Kai ni dai wannan aiki nasu Abie yana moremin, da ƙarfi da yaji ya maida kowa jami'insu a gidan nan, ALLAH banason kina nesa dani ko kaɗan. Amma yaya zanyi, nanda lokaci kaɗanma zaki gudu gidan aurenki ki barni da kewa ta haƙiƙa kamar yanda little taimin.
      Ƙasa Afrah tayi da kanta kawai cike dajin kunaya. Sai dai bata iya cewa komaiba dai.
        Sallamarta Nabeelah tayi ta tafi dan tasan Jay jiranta yake. Ilai kuwa ta iskesu a falonsa shi da Miemaa suna jiranta. sai da tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga. Bayan ta durƙusa ta gaishesu ne Jay ya nuna mata gabansa alamar ta zauna. Babu musu tazo jikin ƙafafunsa ta zauna cike da ladabi da ƙaunar iyayen nasu.
      Gyaran murya Jay yayi yana kallonta fuska babu wasa. Yace, “Afrah!”.
       “Na'am Abie”.
Ta amsa masa kanta a ƙasa.
      Zamansa ya sake gyarawa sannan ya cigaba da faɗin, “Inason ki nutsu ki saurareni. Duk da bani da fargaba a kanki game da aikin nan tunda nasha sakaki inason sake jaddada miki muhimmancin na wannan lokaci. Kisa hankalinki da ƙyau dan banason kuskure a ciki. Baba malam yanada muhimmanci mai girma a gareni dake kanki. Inason kiyi komai da ƙwazo da hikima ok?”.
       “Insha ALLAHU Abie zanyi duk yanda kace. Kuma zan kula nayi komai yanda ake buƙata. Kudai tayani da addu'a”.
        “To Alhmdllh, addu'a kuwa dama akoda yaushe cikin yi muku ita muke. ALLAH ya baki nasara yay riƙo da hannunki kiyi komai cikin sauƙi. Wannan camaras ne”. Yay maganar yana miƙa mata wasu ƴan ƙananan dutsuna tamkar diamonds kusan goma. “Dasu zaki tafi, inason kibi duk sashen gidan ki maƙalasu a kowanne parlors. Idan sun wadata har Backyard na gidan dan suma wajene da masu baƙin hali zasu maƙale suyi magana. Ki ajiyesu da tsantsar kulawa yanda babu wanda zai gane minene. Duk da nasan koda a zahiri suke bawai ganewar zasuyiba inba dai ganinsu da yawa yasa suyi tunanin wani abun kuma daban ba. Inhar kika samu nasarar saka cctvs ɗin nan a ko ina na gidan to aikin zaizo da sauƙi insha ALLAHU. Dan zasu bamu damar kula da motsin kowa hankali kwance. Banason Little da Dawood susan komai kan camaras ɗin nan, wannan aikinane ni kaɗai zakimin.  Abu na biyu shine saka ido akan duk wani baƙo da zai shigo gidan. Ma'aikatan gidan da yaran gidan suma. Banda wauta da surutu mara amfani, duk da namasan waɗanan ba halayenki bane. Biyayya ga nagaba. Aiki basai ance tashi kiyiba tunda nasan iyayenki sun tsaya akanki babu abinda baki iyaba. Dan ALLAH ki kula da mutuncin kanki dan gidane family house akwai samari a ciki. Duk da har raina bana zargin rashin tarbiyya daga wannan zuri'ar koda a mafarkina. Amma dai dolene na jadada miki kame kanki da kuma kula da ibada dan na fahimci aikin zai kaiki har cikin azumi dake gabatomu”.
        “Inasha ALLAHU Abie zaka sameni mai kiyayewa”.
    “To ALLAH yay miki albarka da sauran ƴan uwanki baki ɗaya”.
      Amin ta amsa ita da Miemaa dake saurarensu. itama daga baya ta ɗora da nata nasihan da wasu dabarun aikin. Duk da kuwa tunda aka tsura maganar cikin koya mata take salo-salo harma Jay din kansa. To Alhmdllhi kuwa tana haddace komai. Dan dama itama bata wasan yara bace wajen tsayawa tsayin daka akan aikin nan da ba yau iyayenta suka fara tsundumata a ciki ba.

        Anuwar da kansa ya kai Afrah ɗin Kano. Dan akwai harkar business ɗinsa da zaiyo acan. Koda jirgi ya diresu kuwa ana sallar magriba. Amma duk da haka sai ya fara kaita suka gaisa da baba malam yay sallar har isha'i acan sannan ya wuce nasa harkokin. Duk da baba malam ɗin yaso ya kwana anan amma fir ya ƙi saboda uzirinsa.
         Da ga Muhammad har Umm sunyi matuƙar jin daɗin zuwan Afrah. Dan gaba ɗaya saita ɗauke musu kewar Nu'aymah. Tun a daren Umm ta kaita sashen hajjo ta gaisheta. Nanma ta samu tarba sosai a wajen ƴar tsohuwar. Dan nutsuwar Afrah ɗin ya saka hajjo jinta a ranta. Taita tsokanarta kuwa tamkar yanda takema jikokinta idan taso. Afrah komai bata iya cewa sai murmushi. Dan miskilace ta gaske itama kamar little. Tama dama Jay da bily ɗin a miskilanci dan ta gada a uwa da uba da yaya. Idan kaji tana hira da dariya to Mammata ne (Nabeelah) ko Daddynta (Anuwar). Sai ko Miemaa da Abienta shima.
       Basu baro sashen hajjo ba sai lokacin kwanciya. Umm ta kaita ɗakin Aymah da aka gyara mata tsaf, kayantama tuni suna can. Sosai ɗakin yayma Afrah ƙyau. Taita kallon hotunan Nu'aymah da aka mammaƙala a bango. A hankali tace, ‘Masha ALLAH ƙyaƙyƙyawa da ita kuwa’.

_______________★★★

           *_U.S_*
Chapter 171 · 0% Book details