Sashe 49
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
..............“Khadijah tabbas kin cancanci ki damu, amma karki manta nima fa ina cikin damuwarne har kashi biyu. Ta shi da taki kema, dan farin cikinki shine nawa dana sauran yarana. Akasin haka duk a wani hali zaki sakamu. Ko yau ke baki lura da yanda Omar ya yini sukuku ba saboda yanda yake ganinki?. Kofa makaranta bai fitaba sai da nai masa magana”.
Zaune ta tashi sosai tana share hawayenta. “Kayi haƙuri to na daina, amma kodan Adawiya ka sakashi ya biyo Hajjo idan zata dawo suzo suyi salla a gidan dan ALLAH itama iyayensu su ganta, sannan musan yaya zaman nasu yake tafiya”.
Ɗan murmushi yay mata da shafa kumatunta. Yace, “Karki damu zanyi ƙoƙarin hakan insha ALLAH, nima gobe idan ALLAH ya kaimu zanje kanon, inaga Omar ne zaiyi tafsir ma gobe idan ALLAH ya kaimun insha ALLAH”.
Kanta ta jinjina masa da addu'ar fatan ganin wayewar garin lafiya.
_____________________________
Washe gari Abban su Abdallah ya nufi kano domin yin sallama da hajjo da suke shirin wucewa nan da kwanaki biyu. Yako isa da wuri, dan sanda ya shigo gidan ma duk ƴan uwansa na nan, baba malam yanama barci bai tashiba tun ɗazun daya ɗan kwanta. Yaran sun baibayesa da oyoyo kamar yanda suka saba a sashen hajjo, kowa na tambayar ɗan uwansa da suke sa'anni. Yayinda shi kuma yake tambayarsu azuminsu nawa-nawa.
Ya jima yana biyema shirmensu kafin ya nufi ɓangarensu da babu kowa a ciki, sai dai zuwan nasa Hajjo ta saka Amal da Nu'aymah zuwa su gyara duk da yace ba kwana zaiyi ba. Wanka yaɗanyi ya kwanta kafin azhar ya samu ganawa dasu baba malam, dan yama iske Abba Musbahu yana wajen tafsir danshi na safe ya keyi.
Bayan gama gaisuwa da Abban su Abdallah Nu'aymah ta nufi sashensu ranta duk a cinkushe, ko kaɗan bata sha'awar wannan zuwa Umrah duk da tana buƙatar hakan fiye da komai a ƙasan ranta. To amma fitinar da take hangoma kanta a tafiyar ta fahimci sai tafi daɗin yawa.
“Lafiyarki kuwa Nu'aymah? Kina tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”. Umm dake zaune a falo tana duba littafin KITABUT TAUHID ta faɗa tana kallonta.
Zama Nu'aymah tai kusa da ita, tare da ɗora kanta gefen kafaɗar Umm ɗin. “Umm azuminne fa yau nikan tun yanzu na fara jinsa ALLAH, ni koma wajen tafsir bazanjeba yau barci zanje nayi”. Shiru Umm tai kawai tana kallon Nu'aymah, dan gaba ɗaya a watannin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta. Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai. Da yake ta san akwai damuwar Abdallah tattare da ita har yanzu sai take danganta yanayin Nu'aymahn da hakan. Shiyyasa ta duƙufa gayama ALLAH akan lamarin. Idan da rabon aure a tsakaninsu ALLAH ya kawo mafita ayi, idan babu kuma ALLAH ya saka musu salama su duka itama ya bata miji nagari.
Jin Umm batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci.
Sun jima a haka, kafin Umm da taji Nu'aymah ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Umm ɗin.
“Ita wannan lafiya take kuwa?” Baba malam da Umm bataji fitowarsa da isowarsa wajenba ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Nu'aymahn. Ɗago ido Umm tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Nu'aymah.
“Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun yay yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To Alhmdllh, bara na leƙa massallaci Mustapha yasanar min da zuwan baƙi”.
Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu'ar dawowa lafiya. Da amin ya amsa yay gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin Muhammad ba, shi yana inane?”.
“Inaga yana ɓangaren Hajjo, dan tun isowar Abbansu na Abuha ya fice”. Umm ta bashi amsa. “Oh Rizwan ɗin yazo ne?”. Yay maganar yana ficewa batare daya saurari amsa daga Umm ɗinba. Itama ganin ya fice ɗin sai batace komaiba ta maida hankalinta ga kallon tafsir ɗin da takeyi yanzun a WISAL HAUSA.
________________________
Kasancewar baba malam da anyi magriba yasha ruwa yake barin gidan sai suka yanke shawarar ganawa bayan sallar zuhur shi da sauran ƴan uwansa biyu dan Abba Musbahu yana Lagos.
Bayan ya kammala da baƙin da sukazo ganinsa bai shigo gidanba dan lokacin salla yayi. Sai da suka idar da salar zuhur ɗin sannan suka shigo gidan a tare ta ƙaramar ƙofa abin sha'awa. Kansu tsaye sashen mahaifiyarsu suka nufa. Inda suka isketa ita kaɗai sai Kubrah dake fashin salla tana barci a kujera. Sallamarsu kuma ta sakata farkawa. Sai ta koma bedroom ɗin hajjo ta kwanta bayan ta gaishesu.
Duk a ƙasa suka zauna suka zagaye mahaifiyarsu, dan wannan al'adarsu ce inhar suna wajenta basa zaman kujera sai dai ƙasa. Sun gaisheta ta amsa cike da farin cikin ganunsu kamar yanda ta saba. Harda ɗan barkwancinta akan autanta. “Kunzo duk kun zagayeni babu autana”. Dukansu murmushi sukayi, Abbansu Abdallah yace, “Inna ai tunda kin gammu kin gansa”. Dariya taɗanyi irin tasu ta manya. Tace, “Gara dai shima na gansa ɗin dai yaji ɗumina”.
Dariya suke mata cike da ƙaunarta. Kafin su tsagaita su fara tattauna abinda ya tarasu game da abinda suke tsarawa na hidima bayan tafiyarta. Sun shafe kusan awa ɗaya suna ƙulla abubuwa masu muhimmanci da amfani. A cikin maganganun nasu ne Abbansu Adawiya ke kawo shawarar ya kamata su gayyato bawan ALLAH nan daketa hidima a garesu shan ruwa idan a cikin kano yake inhar yanada halin zuwan.
Baba malam da shawarar taima daɗi sosai yace, “Mustapha kaga kuma fa kazo da shawara mai ƙyau gaskiya. Dan wlhy bazan ɓoye mukuba inajin matuƙar son ƙwaɗaituwa da ganin wannan bawan ALLAH. Akwanakin nan kodan na saka lamarinsa cikin raina sai nakanta mafarki da shi duk da ban taɓa ganinsaba. Sai dai yanda mafarkin nasa ke zuwamin sai abin yakan zauna cikin raina sosai. Shiyyasa nakeson mu ƙara ƙaimi wajen masa addu'ar fatan alkairi, idanma wani al'amarine ke damunsa ALLAH ke nunamin ta hakan ALLAH ya warware masa”.
Duk da sun fahimci mafarkin akwai abu mara ƙyau a ciki sai basu takura kansu nason saniba, suka shiga addu'a a garesa da alƙawarin sakashi a duk ibadunsu insha ALLAH. Sunja kusan awa biyu da rabi a wajenta sannan suka fito dan la'asarma tayi. Basu koma ciki ba sai suka nufi massallaci kawai.
________________★
Shirye-shiryen tafiyar hajjo da Nu'aymah da Yah Ahmad Umrah ya gama kammala tsaf, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce. Ta kama dai-dai da cikar azumi kwana goma sha biyar kenan.
Duk hanyoyin da Nu'aymah zatabi nason ganin tafiyar bata yuwu da itaba tabi amma bata samu mafita ba. Hakan yasa taci kukanta ta haƙura ta barma UBANGIJI ikonsa, dan ta miƙa kukanta wajen ALLAH akan wannan tafiya har batasan iyakaba. Ganin al'amarin ya kasa gagara saita ɗaurasa a mizanin hakan shine mafi alkairi a gareta shiyyasa.
Zaunar da ita Umm tayi tai mata doguwar nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba shashanci ba. Tsaf Nu'aymah ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan insha ALLAH zata zama mai himma. Saboda ma ta gujema abinda take gudun ganin daga Adawiya da Yah Abdallah saita ƙudiri niyyar shiga ittiqafin idan sun isa.
Washe gari ƙarfe biyu na rana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki ita da Yah Ahmad da Hajjo. Ta tafi cike da kewar Umm da Muhammad harma da baba malam da sauran jama'ar gidan. Musamman ma su Amal da badan basu ƙarasa jarabawarsu guda biyu data rageba da tare zasu tafi.
To Nu'aymah a sauka lafiya. Duk da muna tare dake dan muji yaya wasan zai kaya ke da Adawiya da Yah Abdallah🤔🤗🚶🏻.
_______________________________
*_DOCTOR YOOHAN_*