← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 211

Sashe 2

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A waje kam dai har yanzu ba'a kai ga fara gudanar da komaiba, sai dai wata ɗaliba a cikin ƴammatan da zatai sa'anni da amaryace ke karatu cikin zazzaƙar muryarta, wanda hakan yasaka wajen yin tsitt ana saurarenta.
Wasu zafafan motocine guda biyar suka shigo cikin layin, duk da mutane hakan bai hanasu kutso kaiba kansu tsaye jikin ƙofar babban gate ɗin harabar massallaci. a take mafi yawan mutanen dake a wajen walimar hankalinsu ya koma ga kallon motocin da sukai parking a jere abin birgewa. Kowa ya zuba ido yaga su wanene zasu fito a ciki?....
Ni kaina sai da na sauke numfashi da faɗin Masha ALLAH, saboda fitowar wasu samari masu ji da lokaci da gayu daga motar, da gani babu tambaya waɗanan abokan angone dama angon kansa, bankai ga cankar angonba wani mafi ƙyawun haiba da tsarin kwalliya a cikinsu ya fito a motar tsakkiya waya manne da kunnensa yana murmushi. Sanye yake cikin ɗanyar shadda Maroon color sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ya saki lallausan murmushi yana gyaɗa kansa alamar amsa mai maganar daga can, sai kuma ya sauke wayar ya tura aljihu dabin abokansa dake tsaitsaye suna kallon ƴan taron walimar da suma mafi yawansu su suke kallosu da kallo. Kafin yace wani abu ɗaya daga cikinsu ya juyo yana faɗin, “Woow Ab harfa na canko amaryarka”. Ɗan hararsa yayi da ɗauke kai kamar bazaice komaiba, sai kuma ya sake kallonsa yana wani furzar da numfashi. “Malamai dalla kallon ya isa haka, ku bakwa ganin su Baba Malam duk mu suke kallo suma”. A tare duk suka juyo da kallonsu garesa suna dariya, wanda yay magana ɗazunne ya sake faɗin, “Hahh! Go gefe malam, kai dai faɗa mana kishi kakeyi dan ance anga Angel ɗinka”. “Shashasha, to idan nayi kishin laifine?”. Abdallah ya faɗa yana ratsa tsakkiyarsu yay gaba.
Cike da shaƙiyanci sukabi bayansa suna dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Shege uban zumuɗi, anya kuwa zaka cika alƙawarin da kaima su Baba Malam na barin ƙwailarnan taka tai karatu? Karfa muji nanda wata tara ana nemanmu a labour room”. Duk da yana jinsu sarai bai tankaba, sai dai ya ƙawata fuskarsa da wani sassanyan murmushi daya ƙara fidda ƙyawun fuskarsa...

“Huuhm Nu'aymah! Gafa Soulmate ɗinki nan tafe tamkar wani ɗawisu a tsakkiyar furanni”. Iman ta faɗa a hankali cikin kunnen Nu'aymah da kanta ke'a duƙe lulluɓe da abaya batasan wainar da ake toyawaba.
Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan ɗagowa kaɗan, idanunta ne suka sauka akansa. Taja ajiyar zuciya tana lumshe idanunta wani sanyi na ratsa mata ƙirji. Sosai take tsananin son Yah Abdallah, kamar yanda tasan itama yana sonta fiyema da yanda take sonsa. Yah Ab farin cikinta ne, jinin jikinta ne, nutsuwarta ne, shiɗin na musamman ne a gareta, dan yana ɗauke da mataki uku ne na martaba a gareta. Shi ɗin jininta ne ɗan uwanta, sannan masoyinta tun batasan kantaba. Malaminta kuma na farko ta ɓangaren ilimi. Shiyyasa komai nasa abin girmamawane a gareta......
“Hy Baby! Kallon ya isa haka karki cinyesa mana”. Nanah ta faɗa tana ɗan mangare kan Nu'aymah. Karon farko da tunda aka wayi garin yau Nu'aymah tai murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana, ɗan harar Nanah tayi da Iman da suke mata dariyar shaƙiyanci. Ta maida kanta ƙasa tana faɗin, “Sa'idiniyya kawai”. Nanma dariyar sukayi, ita kuma ta lumshe idanunta daga cikin hular abayar tana maijin nutsuwa da farin cikin isowar angonta lafiya bayan tsahon shekaru biyu kenan basuga junaba sai dai a waya da hoto da video call.

Isowar ango Abdallah da abokansa tayi dai-dai da shigar lokacin sallar la'asar, dan haka aka sanar da zuwa ai salla.
Mimmiƙewa mazan suka shigayi suna nufar bayan masallacin domin yin alwala, masu alwalar zuhur kuma da bata karyeba suna shigewa ciki. Matanma ba'a barsu a bayaba, wasu cikin gida sukaita shiga, wasu kuma sama inda massallacin mata yake.

★★★★★

Baƙi da suka janyema Umm hankali ya saka Adawiya samun damar silalewa ta nufi ɓangarensu. Nan ɗinma akwai mutane babu laifi, musamman da a yanzu aketa shigowa domin gabatar da sallar la'asar. Sashen Abbansu ta shige, inda ta tabbatar bazata samu kowaba sai su ƴan gida. Ilai kuwa babu kowa sai ƙamshi dake ta tashi mai daɗi. Ɗakin farko dake a falon sashen ta buɗe ta shiga, babbane yasha kayan more rayuwa tsaf, ta zube a saman gadon tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai tafiya da kuka mai ƙarfi da hasala zuciya.......
Turus Addah data fito daga bayin ɗakin fuskarta jiƙe da ruwa alamar tayo alwalar yin salla tayi a bakin ƙofa tana kallonta, a take idanunta suka rine da ɓacin rai, cikin faɗa tace, “Wai wane kalar shashancine wannan kikema mutane haka Adawiya?!!”.
Adawiya da sai yanzu tasan da shigowarta ta taso da gudu ta faɗa jikinta da sake fashewa da wani sabon kukan, “Addah Wlhy ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wlhy saina kashe kaina Addah. Dan nafita sonshi ku taimakeni.............”
Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Addah ta bita harta zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Adawiya tai zaune ta riƙo hannunta. “Wlhy Addah inhar baku aura masa niba saina kasheta!!”.
Baya Addah tai da sauri zata faɗi ƙasa tana mai waro idanu waje sosai akan Adawiya, bakinta na ɓari tace, “Ki kasheta Adawiya?!”.
“Da hannun nan nawa kuwa”. Adawiya ta faɗa tana zazzaro idanu waje itama da ɗaga hannunta tana nunama Addah............✍

Hummmmm!!!! Turƙashi. Masu karatu wannanfa shine ana dara sai ga dare yayi😲. Mi kuke tunani akan wannan labari? Wacece Adawiya? Sannan wacece Nu'aymah? Wanene Kuma Abdallah?. yaya zata kasance? Minene zai faru kuma? Wace amsa Addah zata bama Adawiya?......
Amsar waɗanan tambayoyin duk suna a Littafin SARAN ƁOYE!! da ke cikin tawagar littatafai biyar na zafafa 2021 dake shirin zuwa muku insha ALLAHU nan bada jimawa ba😉😋.

Wlhy karku bari ayi babuku, dan ZAFAFA BIYAR 2021 fa da zafinsu suke tafe, na tabbatar muku tafiyar wannan shekarar ta dabance MASOYAN AMANA😋🤗🤗😀😀.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

*_SARAN ƁOYE!!_*

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

Free page😋

No. 2

.................Tsaki Addah taja tana ballama Adawiya harara, ta tsallaketa ta wuce tana faɗin, “Sai kije ki kashetan shashasha kawai mara tunani”.
         Kuka sosai Adawiya ta sake fashewa da shi. Ta rarrafa har inda Addah take shirin kabbara salla ta riƙe mata ƙafafu. Cikin fushi Addah ta ƙwace ƙafafunta tana nuna Adawiya, “Wlhy idan baki shiga hankalinkiba Adawiya zan bala'in saɓa miki, wai wane irin iskancine wannan? Ki shiga hankalinkifa tunkan nai miki abinda zakiyi dana sani a taron bikin nan. Dalla tashi ki ficemin anan, ba kashe Nu'aymah ba ki babbakama gidan wutama mu ƙone ƙarewar hauka. Wawuya kawai!!”.
          Yanda Adawiya taga ran Addah ya ɓaci tasan zata iya cin ubanta kamar yanda ta faɗa, tana ganin ta kabbara salla saita tashi ta fita tana kukanta. Addah mace ce mai yawan wasa da fara'a, idan har kaga fushinta to lallai an kaita maƙura, shiyyasa idan tai fushin dolene kaji shakkarta. Su kansu ƴaƴanta tana rayuwa da sune tamkar ƙawayenta, hakama sauran yaran gidan. Wannan halayar tata tajan yaran a jiki yasa kowane yaro yazama ɗan ɗakin Addah a gidan, suna sonta sosai, hakama iyayensu sunajin daɗin yanda take son ƴaƴansu da basu lokacinta.
Chapter 2 · 0% Book details