Sashe 206
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ta kuma kwanciya.......” Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matuƙar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar ƙanwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al'amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a ɓoyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum ɗin yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum ɗin. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din ɗaga masa ƙafa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi alƙawarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa ƙeyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai gaɓar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al'amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa ƴar uwarsu da mijinta da ɗanta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka haƙura badan zukatansu sunsoba, suka ɗauka wannan itace ƙaddararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen ƴan sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka ɗauka wani ya ɗauke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya ɗaure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an ƙwace duka kaddarorin nasa dake a ƙasar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar ƙasar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matuƙa, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al'ajabi..... Ta ɓasan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da faɗin, “Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu ƙarfin faɗa aji suce wani abu”..............✍ [7/9, 5:30 PM] Sweet Sis: No. 77