← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 211

Sashe 28

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

             Cike da mamaki Momy ke kallon wayar tata tamkar idanunta zasu zubo ƙasa. A ranta take raya ‘To miya samu wayar Abdallah? Ta shiga bai ɗagaba, daga ƙarshema wayar ta jita a kashe’.
       “Momy lafiya?”. Omar daya shigo falon ya faɗa idanunsa akan Momy dake tsaye tana ta faman juya waya.
     Saurin ɗagowa tai ta kallesa, sai kuma cikin sanyin murya tace, “Omar yayanku ne wlhy, ya kirani bana kusa inaga ko cikin su Amal wani ya ɗaga, shine yanzu dana fito naga alamar ya kira an ɗaga saina kirashi. Amma har missed calls biyar na jera masa bai ɗaga minba, yanzu daga ƙarshema wayar a kashe take”.
        Murmushi Omar yayi yana zama da faɗin, “Oh Momy ƙila to baya kusa ne, kinsan hidimar Yah Abdallah ba ƙarewa takeba. Nasan zai kiraki shima”.
       Kai Momy ta girgiza masa, “Omar ba rashin ɗaga kiran bane damuwata, jin wayar a kashe bayan kuma duka kiran danai sun shiga”.
       “Momy Please ki kwantar da hankalinki, nasan insha ALLAH babu wata damuwa. Koma baida cajine kokuma network”.
    Kamar zata sake magana sai kuma tai shiru taɗan jinjina kanta. Tashi tai ta maida wayar a caji dan fama cajin ta saka ta shiga kitchen tun ɗazun. Yanzuma tana maida wayar a caji saita koma kitchen ɗin suka cigaba da aiki ita da masu aikinta su biyu tabar Omar daya kwanta cikin kujera yana canja chennal a falon. Sai dai kuma abin yaƙi barin ranta sam.

        Har dare Momy na jiran kiran Abdallah shiru, ta kuma sake nemansa itama amma har lokacin wayar switch up. Tun tana danne damuwarta harta bayyana fili. Abbah da tun ɗazun yake kula da yanayinta ya tambayeta ko lafiya?. Batai nauyin bakiba tai masa bayanin abinda ya faru.
     Shi dariyama ta bashi ganin yanda duk tai wani iri kamar ance Abdallahn ya rasu ne, dan haka yaɗan murmusa yana girgiza kansa, batare da ya ce mata komaiba ya cigaba dacin tuwonsa.
        “Abban Abdallah dan ALLAH ko zaka kira min shi da wayarka?”. Sake kallonta yayi da ƙyau, sai kuma yay gyaran murya da ɗauke idonsa. “Khadija ki rage ruɗiyarnan taki, yanzu dan ALLAH Abdallah ƙaramin yarone halan? Maybe baida caji ne kokuma ya shiga wata sabgar. Kiyi haƙuri kiga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan bai kiraki ba”.
       A sanyaye tace masa “to” kawai badan hakan ya mata daɗiba. Sai ma ta tattare kwanikan daya kammala cin abincin ta fice da su. Saida takai kitchen sannan ta nufi ɗakin su Amal. Zaune ta iskesu suna karatu, Amal na ƙarama su Imran. Duk shiru sukai suna kallonta. Itama kallon nasu takeyi.
      “Amal wanene a cikinku ya ɗaga kiran yayanku ɗazun?”.
      “Kira kuma Momy? Wlhy bansan Yayah ya kira wayabama ni, dan tun ɗazun danace miki zanje na sake duba Nu'aymah ina can wajenta ɓangaren Hajjo ni da Yusrah. Amma wani abune ya faru?”. Kai momy ta girgiza mata tana kallon su Imran suma. Da ɗai-ɗai suka shiga bata amsar suma duk basu baneba.
     Kanta taɗan dafe zuciyarta na neman faɗawa a ruɗani, lallai yaran sunada gaskiya, dan idanma tai dubi da lokacin da Abdallah ya kira ai duk basa gidan ma suna islamiyya. Kasancewar yau lahadi sunayin harta safe zuwa uku a tashesu, to indai suna garin suma yaran suna zuwa anan ma. Kuma tunda safen duk suka fita. Amal ce kawai batajeba saboda ta tashi da ciwon mara, daya ɗaga matane tace zataje ta duba Nu'aymah. Sai da ta fita da kusan awa ɗaya ma Abdallah ya kira.
      Ficewa tai taja musu ƙofar tanason tunano ko wani ya shigo a wannan lokacin, to amma kuma babu wanda ya shigo ɗin, daga ita sai ƴan aikinta. Abba ma baya nan, Omar ma ganin datai masa bayan kiranne ya shigo gidan, dan tare suka fita da baba malam tunda safe.

              Momy da taga tunaninta na kaita wasu nazari daban sai kawai ta ajiyesa gefe, ta barsa akan uzirine yayma Abdallah yawa. Waya kuma ƙila sanda yake kira cikin sauran ƙannensa yaran gidan wani ya shigo ya gani ya ɗaga.
     Washe gari da safe batabi takan kiran Abdallah ba ta cigaba da hidimominta kamar yanda ta saba. Abin mamaki kuma har dare bai kirantanba, sai itace dai da dauriyanta ya gaza ta nemesa kusan taƙwas na dare. Switch up dai ɗin yauma.
            Ganin yanda ta zuba tagumi yasa Abba jin tausayinta. Wayarsa yasa ya kira Abdallahn, amma sai yaji layin a rufe. maida kiran yay a ɗayar Number Abdallah ta business. Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yace masa ga Momy.
       Jimmm Abdallah yay kamar bazaice komaiba, sai da Abbah yace, “Nace ga Momynku ko bakajiba?”.
         “Amm sorry Abbah network ne, bata to”.
      Miƙama Momy Abbah yayi, ta amsa zuciyarta na mata sanyi, dan tana matuƙar ƙaunar Abdallah sosai a cikin ƴaƴanta, sai dai tana ƙoƙarin dannewa gudun saka ruɗani a tsakanin ƴaƴanta.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________

            Da ƙyar Abdallah ya danne zuciyarsa ya gaida Momy da fuskarta ke shimfiɗe da murmushin farin cikin jinsa. Ta amsa masa cike da kulawa tana tambayarsa yaya suke? Ina Adawiya?.
           Muryarsa a ɗan cinkushe yace tayi barci, shima shirin kwanciya yakeyi.
           “To Alhmdllh tunda dai lafiya kuke. amma jiya miya samu wayarkane? Na kira har sau biyar baka ɗaga ba, daga baya kuma saima naji switch up”.
           Ba ƙaramin haushine ya kama Abdallah ba dajin maganar Momy, bayan sharaɗin data gindaya masa mai ƙarfi akan abinda yake tsananin so shine kuma zata kirasa?, yanzu kuma dan taga tana kusa da Abbah take nuna kamar batai komaiba. To mizata faɗa masa bayan wanda ta faɗa masan kuma?............
       “Abdallah lafiya kuwa?”. Momy ta katse masa tunani. “Babu komai Momy, wayarce ta faɗi a cikin ruwa bayan mungama waya jiya shiyyasa”.
         “Abdallah ai ni bamuyi way.......”
Zare wayar Abba yay daga kunnen Momy yana faɗin, “Haba Khadijah tunda kinji lafiyar tasu ya isa haka. Bakiga dare yayiba ne? Yanzu kuma Abdallah yanada iyali”.
          “Afuwan Abban Abdallah na shafa'ane wlhy. Ni saima naji muryarsa kamar wanda bayajin daɗi”.
      Kallonta Abba yay sosai, sai kuma ya matsota jikinsa ya gwargwaɗa mata magana a kunnenta. Idanu ta ɗan zaro waje, sai kuma tai saurin miƙewa tana kare fuska da hannu alamar maganar tasa ta bata kunya.
     Murmushi Abba yay yana binta da kallo harta shige toilet. Yaɗan girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.

________________

          Jikin Nu'aymah yayi sauƙi sosai Alhmdllh, sai dai har yanzu bata koma sashensu ba tana sashen hajjo. Tana dai zuwa ta gaishesu da safe, ta kuma taya Umm aiki kamar yanda aka horesu. Babu wanda yay mata maganar Yah Ab a gidan, itama tayi ƙoƙari ta danne tana jira taji daga garesu kamar yanda Yusrah ta bata shawara data dameta da tambayar yanda akayi.

       Kwana biyu da samun lafiyar Nu'aymah su Momy sukai shirin komawa Abuja saboda karatun yara. A wannan karon Nu'aymah jitai batason tafiyar su Yusrah da Amal, dan suna ɗauke mata kewar Adawiya sosai. Tasan kuma idan suka wuce zata koma ita kaɗaine babu wani abokin ƙiriniyarta kamarsu a gidan, daga yayu sai ƙanne sai iyaye.
        Babu yanda ta iya, a washe gari su Amal suka fara wucewa Lagos da safe. Da yamma kuma su Yusrah. Nu'aymah harda hawaye. Hajjo da taji tausayinta har tayi tunanin ko Nu'aymah tabi cikinsu Yusrahn, sai kuma ta tuna ashe akwai shirin zuwa ganin Doctor da sukeyi. Zama tayi taita lallashinta harta saki jikinta, yayinda su Hajarah da sukazo sashen Hajjon suka ɗan rage mata kewar tafiyarsu Amal ɗin.

★★★★★★
Chapter 28 · 0% Book details