← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 211

Sashe 89

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

        Tunda aka fita da Nu'aymah asibiti baba malam ya koma sashensa. Zaune yake a study room ɗinsa saman wata kujera da ke ɗan lilasa idan yana kanta. Duk da rana ce ɗakin yayi duhu sosai kasancewar bai ɗaga labule ko guda ɗaya ba a ɗakin. Bai kuma kunna fitila ba sai ɗan hasken da ake gani kaɗan kasancewar na hasken rana. Kwance yake a jikin kujerar idanunsa a lumshe ya faɗa duniya mafi nisan zango a tunani.
         Tun daga daren jiya har zuwa yanzun zuciyarsa a ruɗani take. Ruɗani irin wanda ƙwaƙwalwa bata iya rarrabe gaskiya da ƙarya, fari da baƙi, haggu da dama........
        Motsin da yaji a kusa da shine ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar. Umm ce ya gani cikin ɗan hasken da ɗakin ke da shi. tsaye take a gefensa dafe da kanta alamar tana a cikin matsala. Zumbur ya miƙe ya riƙota ganin tana layi, ga hakki tanayi kamar wadda tayi gudu a cikin sahara.
      Kujera doguwa dake a ɗakin ƙwara ɗaya kacal ya nufa da ita, ya kwantar da ita jikinsa sai tsuma ya keyi. “Jannat miya sameki?”.
       Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yay magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ɗayan kuma na akan ƙirjinta da ke mata azabar zafi tamkar zai buɗe.
         “Sooraj inaji a jikina mutuwa zanyi, a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al'amarinba. Abban Nu'aymah akwai ruɗani a cikin zancen nan, amma ni kaina na kasa banbance mai gaskiya tsakanin ƴarmu da likitocin nan. Idan da ace likita ɗaya ne ya faɗa sai muce ko haɗa baki akayi da shine, amma kaga harsu uku, ɗayan ma bamu santa ba tunda asibiti suka sameta. Sannan Sooraj a kwanakin cikin nan da aka ambata ya kasance jikin Nu'aymah ban taɓa ganin wani alama na mai ciki tattare da yarinyarta ba, babban tashin hankalina kuma shine tabbas watan da ya shige na azumi banga Nu'aymah tayi jini ba har suka wuce saudia, wancan watan kuma a farkon wata tayisa. Kasan dai ita jininta baya ɓoyuwa a gidan nan saboda lalurar da yake zuwa mata da shi. Sooraj na shiga ruɗani wlhy”.
      Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
       Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe ƙirjin nata har yanzun.
        “Jannat bazaki mutuba, bana fata ki tafi ki barni cikin wannan tarnaƙin, nima zuciyar tawa ba iya ɗauka zatai ba. Ki daure dan ALLAH muyi imani da ƙaddara. Amma kamar yanda kike cikin ruɗani a wannan al'amarin wlhy nima haka nake a ciki. Na ƙiyasta duka zuwan Yoohan cikin gidan nan gaba ɗaya ban iya tunano ta yanda har ya samu keɓancewa da Nu'aymah ba. Wlhy zuciyata ta kasa yarda Nu'aymah da Yoohan zasu aikata wannan ɓarnar. Idan kuma nace ban amince sun aikata ɗinba yaya xanyi da waɗan nan hujjojin bayyanannu kuma Jannat? Ya ALLAH ka bayyanar da gaskiyar al'amarin nan koda a cikin Zukatanmu ne ya Rabbi”.
      Haka sukaita hawaye har sai da baba malam ya fahimci Umm na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa.
       Hakanne ya jawo hankalin su Hajjo da ke zaune jigum-jigum suna jiran jin halin da Nu'aymah dake a a sibiti take a ciki. Har rige-rigen shiga sashen sukeyi, gashi duk mazan gidan sun wuce asibiti tare da Nu'aymah, dama baba malam ɗinne kawai ya rage.
         A hankali inuwar mutum dake a jikin windown tana kallon su baba malam ta kafar labule ta janye daga wajen. Hakan yay dai-dai da fara shigowar matan gidan. Babu wanda hajijiya bata kusan kwasa ba ganin da gaske Umm bata numfashi, ga baba malam yau duk jarumtarsa da kawaici yana zirar da hawaye............

_____________★★★

             A asibiti bayan sallar la'asar Doctors ɗin suka buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. Su duka ukun suka shiga office ɗin, aka bar su Abdallah kawai a waje.
     Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ɗan gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
       Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ɗaya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ƙa'ida bana waje ɗaya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in taƙaice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”.
          Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “ALLAH yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ɗiyar ɗan uwan nasu dama ɗan uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.
Chapter 89 · 0% Book details