← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 211

Sashe 188

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage raɗaɗi. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. “Fauza dan ALLAH ina roƙonki a karo na ƙarshe ki ƙaryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau ƙaddara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji saɓanin tunaninsu a kanki Fauza.......” Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a ƙasa kuma taƙi kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. “Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin ɓoye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na zaɓi bin komai mataki-mataki ne saboda sauƙaƙa firgici a zuciyar waɗanda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye”. Da sauri Addah ta ɗago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a ɗaure. “Bayan Hamisu akwai ƴarki Kubrah ko, sannan akwai......” Da sauri ta ɗaga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen ɗan kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli ƙafarta dake naɗe da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin raɗaɗin azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune. “Ko babu ƙarfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu'aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da huɗubar shaiɗan. Wannan Fauzar maƙasƙanciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai ɗauke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni kaɗanne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ƁOYE”. Tarine ya kuma sarƙeta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. “Da wahala shara'ar alƙalin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara'ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya ƙure musu”. “Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin ƙuruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la'akari dana fiki komai a rayuwa. Ni ƴar gatace ko a gidanmu, duk wani jin daɗi da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta ƴan gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke kaɗaiba duk ƴan gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu ƙyau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan ƙwaɓemu akan hakan. Nasararki a kaina bata taɓa kaini ga ƙololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki”. Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da faɗin, “Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna ƙosawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na ɗunbin begensa, sai dai a randa na buɗi ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe”. Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da ƙyar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba. “Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga ƙarshe sai nayi haƙuri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na haƙura na barmiki, duk da dai son nasa na nan maƙale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban taɓa cin karo da rana mai ciwo da raɗaɗi ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. Ƙaddara ta riga fata, dan kuwa haɗuwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani ƙin amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima ƙaninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja'in-ja ya bashi. Na sake shiga ruɗani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake ɗorani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada yaƙinin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka haɗa da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna”. Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm. “Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan gaɓarma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata ɗaya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana ɗaya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane ɗauka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku kaɗaine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban ɗa a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya ɗan sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera huɗu sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan ɓoye mikiba naji matuƙar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada ƴaƴa har huɗu a lokacin. Dan idan ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunar buɗar ido naganki da wani cigaba daya ɗara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana ɗan tayinsa. Duk da ban taɓa tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum huɗuba takemin na ɓarar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya ɗaukeki kuka wuce saudia, nayi baƙin ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da ƙudirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn.........” Cikin ɗacin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, “Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?”. Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a ƙasa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sarƙeta har jini na fita guda-guda yanzun. Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka ɗinne. A take gaba ɗaya falon suka ɗauki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon ƙasa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai miƙe Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba'azo inda take buƙatar ba. Jay ne ya katse shirun nata da faɗin, “Ke muke saurare”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa. Da ƙyar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da faɗin, “Na shaƙa masa maganine, irin wanda naso shaƙama Nu'aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu'aymah kin barta ta dinga leƙata a ɗaki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da ƙudirina, sai akai rashin sa'a kafin na shaƙama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a ƙasa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin ɓoyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina ƙoƙarin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu'aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin faɗuwar tata ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa sai naji daɗi a raina saboda bushewar zuciya da huɗubar sheɗan”. “Likita ya fara ɓusa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma
Chapter 188 · 0% Book details