← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 211

Sashe 67

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu'aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.       
       ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,
        *Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo ƙaton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta ƙarfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ruɗu, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni'imtaccen yanayi yana masa murmushi da miƙa masa littafin nan na musulmai (Al-Qur'ani), yakan ringa ce masa_______*
        *_“Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake ƙunshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman riƙo dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya ƙyaƙyƙyawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin taƙama da riƙo sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka riƙe gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga saɓama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi alƙawarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka karɓi kalmar LA'ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*
          A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al'amari sai yay azamar ƙwaɓar kansa harma da alƙawarin nisanta kansa da su baba malam ɗin. Dan yau ɗin nanma da ƙyar manager ya lallaɓa shi sukazo nan ɗin. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.

       Kafin su ƙarasa hotel ɗin daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ruɗanin kalaman Nu'aymah da mafarkinsa. Sai ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi.
     Motocin na tsayawa baiko jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards ɗinsa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key ɗin ɗakin Yoohan ɗin yanama a hannunsa ne.
     Ɗan gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin tare. Solomon ya buɗe masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga.
        Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon ɗin sai ya bisa yana faɗin, “Sir lafiya kuwa?”.
        Cak Yoohan ya tsaya da ga yunƙurin shiga Bedroom ɗin da ya keyi, batare da ya juyoba ya ɗagama Solomon ɗin hannu da masa alamar ya barsa.
      Da baya-baya Solomon ya rinƙa tafiya harya fice da ga ɗakin, yaja masa ƙofar a hankali gabansa na faɗuwa da yanayin ogan nasu.............✍

🤔🤔🚶🏻Tofa, Dr Yoohan yaya dai?🚶🏻

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta_*.

No. 27

............Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ɗan naushi gadon da faɗin, “Noooo!!!”. Da ƙarfi kamar mai magana da wani.
    Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ɗin yarinyar da ko sunanta baima sani ba. Miƙewa yay daga gadon ya shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin, ko takalman dake ƙafarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ƙarasa gaban shower ya tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ƙarfi, tamkar itace tai masa laifi.
     Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon lokaci ya gama jiƙewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ƙarasa saman toilet sit ya zauna yana mai riƙe kansa da hannu biyu....

_______________________

          Duk yanda Nu'aymah taso sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta miƙe daga zaunen da take kusa da Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
    Sai da taɗan saci kallon Addah da tai banza dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. “Um.....u.... Zanje su Aunty Zulfah na jirana”. Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata kifa dan sauri.
     Karo suka kusan ci da Malam ƙarami da ke shigowa. Tai saurin komawa da baya tana faɗin, “Yi haƙuri Yaya, bansan ka taho ba”.
     Murmushi ya mata da cewa, “Karki damu Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm”. Ɗan kallonsa tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake faɗaɗa murmushin sa, “Dama ba wani abu bane, baƙon da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki. Shine naje kai miki na Iske baƙya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki”.
      Tunda ya ambaci baƙo gabanta ya sake tsananta faɗuwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin gaskiya. Sai kuma ta ɗan juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin faɗin, “Ni banaso Yaya”.
    Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon. Shi malam ƙarami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka shiga ƙyalƙyala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
     Hajarah ce ta fara farga da yanayin Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana faɗin, Aunty Kubrah ALLAH dama nasan ba ciwon kai Nu'aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su Addah shine duk take a ruɗan nan”.
    Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma mikewa tai ta bar falon tana wani ɗan murmushin da su duka basu fahimci ma'anarsa ba......

Nidai nace, “Humm”.

        “K lafiya? Kika shigoma mutane tamkar wadda aka koro!”. Umm ta faɗa a tsawace tana kallon Nu'aymah data shigo falon a guje.
      Duƙar da kai tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace  “Umm babu komai fa, zanje toilet ne”. Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ɗakinta da sauri.
      Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai banda Umm da tabi Nu'aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta faɗa ba.
Chapter 67 · 0% Book details