Sashe 204
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da wani malami dazan dinga ɗaukar ilimi a hannunsa a ƙasar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ƙarshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuƙa. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ɗinmu na tattara zan koma gida ƙasata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haƙuri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ɗin kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ƙasar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ƴarsu?. Shiyyasa suka haɗani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daɗi. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuɓucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ɗaurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ɗaya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ƙarasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuɗaɗe masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huɗu a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuɗaɗen daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ƴaƴansa maza. Na amsa kuɗi na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ɗaurani akan harkar kasuwanci acan ƙasar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daɗin wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuƙa, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haɓaka. Saboda na farane da kuɗaɗe masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ɗunbin farin cikinaba ɗan uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taɓa ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ɗan zauna kafin hutun Anum na ƙarshen shekara ya ƙare. Waɗanan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haɗu mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaɗai). “Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daɗina da wannan ƙoƙari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daɗin yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ƙulla ta yanda zan kwashe waɗanan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ƙudiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”. “Washe gari ma naje na samesu, shine ya ɗaukeni ya zagaya da ni duk inda companys ɗin suke guda biyu. Na ƙara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba ɗan uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ƙara faɗi da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faɗamin hukuncin daya yanke. Naji daɗi, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ƴan sandan ƙasar. Hankalina ya tashi matuƙa ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ƴan sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiɗima na nufi gidan ɗan uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruɗanin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faɗama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ɗan uwana na faɗin to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haɗa ƙarfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ɗauke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haɗamin komai ɗan uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ɗin nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ɗin jikina na cire jin yana faɗin bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ƙyau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daɗi ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba ƙyan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet ɗina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake buƙata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle ƙofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin ɗakinsu binciken takardu dama duk wani abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu'a da fatan tarkon dana ɗana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako”. “Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. Ɗan jaridan dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sarƙewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga ƙasar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke ɗaya a airport, ɗaya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba ƴan sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar ɗan uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu riƙe dana juna. Ga ƴan sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko ɗar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na ƙarasa haɗa duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami'an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin ƙasar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a ƙasar zuwa ƙasar dake maƙwaftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na haɗu da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da ɗunbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana kuɓuta, dan haka yaymin alƙawarin taimakona ta hanyar tabbatar duk waɗannan kaddarori na ɗan uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin ƙulluwar soyayya mai ƙarfi a tsakaninmu har mukaima juna alƙawarin aure. Ta matsa matuƙa muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi ƙasar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana ɗauka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine ɗan uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce ƙasa. Inba