← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 211

Sashe 40

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

               Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ƙafa alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon ƙafane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar taci mutum ɗanye.
      Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta.......
      “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Nu'aymah ta ɗaga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ƙafafuna ciwo”.
      Ɗan ƙura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ƙaraso wajen Nu'aymah ɗin ta durƙusa. “Baby ƙarya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya”.
    Yamutsa fuska Nu'aymah tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Ƙafafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima”.
         Amal dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.

       Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.

     Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ƴan aiki ta shirya na baba malam da sauran ƴan uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
        Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta leƙa bedroom ɗinsa. Yana wanka, sai kawai ta buɗe Wadrobe ɗinsa ta zaɓo masa kayan da zai saka, saboda yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai buƙata ta fita zuwa ɗakin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.

*_08:15am_*

       Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ƴan uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
     Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ƙofar. Ƙarasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya durƙusa har ƙasa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, “Abba ƴan sandane ke sallama”.
       “Ƴan sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?”. Baba malam dake kallon Abbas babu ko ƙyaftawa ya faɗa.
       “Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne”.
       Ran Abban Adawiya a ɓace yace, “Wace irin Nu'aymah kuma? Miya haɗata da ƴan sanda banda shashanci irin naka Abbas?”. “Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna”. Miƙewa sukai su duka huɗun, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.b

________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

14

.................A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma.
      Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu'aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
       Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba'a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu'aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin🙏🏻😭).

     Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
       Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu'aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
        Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
        Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa.
     Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”. 
     Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
      A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu'aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar.
Chapter 40 · 0% Book details