← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 211

Sashe 24

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
     Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
    Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
    Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
     Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu'aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
     Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
         “Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu'aymah da Yusrah duk suna hawaye.
         “Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu'aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu'aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu'aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za'ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
     Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za'a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
       Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu'aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
    Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.

      Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
      Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
        Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu'aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
       Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
        Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
______________
DUBAI
________

              Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
     Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
     Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
       Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.

“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki🤣😏”.

               Haka ta yini ita kaɗai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ɗauke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
         Abdallah bai dawo hotel ɗinba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ɗauke kansa. Ya ɗauka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ɗaya daga rukunin kujerun ɗakin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ƙofar. Adawiya ta miƙe jiki na ɓari zataje ta buɗe ya ɗaga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
       Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ɗakin.
      “Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?”. Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu'aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ɗauka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.

★★★★

        Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ƙasarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ɗaya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
     Shiko gaba ɗaya ya ɗauketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ƙasar ya maidashi kwana shida zasu wuce.

         Tun a randa Nu'aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ɗin ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu'aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
            Karan farko da tun faruwar al'amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu'aymah itama.

        Bayan sun gaisa cike da so da ƙaunar juna irin ta ɗa da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumuɗi yace, “Momy ashe Nu'aymah ta dawo?”.
       Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, “Uhmm! ta dawo jiya”.
        “Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake kuɓuce minba Momy, a yau ɗin nan ina durowa koda magriba ne sai an ɗaura mana aur......”
         “Kai! Shashasha dakata min. To idanma mafarki kake maza ka farka ka dawo hayyacinka. Wai kai Abdallah wane irin sakaran banzane halan? Ka fita idanuna tunkan na rufesu da kai a ciki wlhy. Bara makaji na maka mai kankat. Wlhy tallahi idan naga ƙafarka a ƙasarnan batare da ni nace kazoba ALLAH ya isa ban yafe maka ba.....”
         “Momy!!” ya faɗa cikin tsananin tashin hankali.
     “Yes! Abinda kaji shi na faɗa. Idan zakai haƙuri da waɗanda aka baka kayi. Hauka akeyi da za'a manna maka mata har uku ƴan family ɗaya uban ƴan son zuminci? Itama Yusrahn ina nan ina nema maka hanyar barinta wlhy. Adawiyar dai ta tsira tunda ALLAH ya sota ka baro ƙasar da ita da wuri. Idan suma sunada nasu zaɓin nima inada nawa ai, amma aka nunamin fin ƙarfi da ƴan uwantaka. Kai kuma shashasha da yake baka kishina hakan ko damunka bayayi. To wlhy kama cire wannan tunanin a ranka. Kuma ko a waya ka kira wani cikin iyayenku kace a ɗaura maka aure da Nu'aymah shima ban yafe makaba. Idan wannan maganar tasa ka kirani karka sake kirana”.
    Ta katse wayar batare da ta jira cewarsa ba.
Chapter 24 · 0% Book details