← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 203 OF 211

Sashe 203

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faɗa ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ɗaya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ɗaya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taɓa faɗa mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faɗin mama debora ta haifi waɗanda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ƙabilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ƙyawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ɗan uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ɗan uwana a wajen, niko saɓanin haka shine zaɓi na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ɗan uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faɗa zamuyi yafi ƙarfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ɗaya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ɓatama ɗan uwana rai, tun yanamin nasiha da faɗamin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ƙarshema muka raba ɗakin kwana, dama ba department ɗinmu ɗaya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama riƙaƙen mara jin magana dan har harkar ƙwaya na fara, sannan na shiga cikin ƴan Cult. Mun kammala degree ɗinmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ƙasar Italy ƙaro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buɗewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaɗanba wajen karɓar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ɗan uwana keyi, tare da yawan ƙoƙarin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar ƙarshe daya kamata mu kammala degree ɗinmu na biyu ɗan uwana ya haɗu da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiɗe zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ɗan uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harƙallar dake tsakanina da ɗalibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haɗu da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ɗan uwana ne. Da farko na harzuƙa matuƙa, sai dai ƙyawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ɗan uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ƙareba bayan taga ɗan uwana. Shin ya warware mata mu ƴan biyu ne, kokuwa ya karɓa mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ɗan uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ɗan uwana daba musulmi ba”. “Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuƙa, dan kodai babu komai shiɗin ɗan uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ƙasar Germany. Haka na tafi al'amarin ɗan uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huɗu, lokacin da muka dawo ƙasar Italy saina samu munyi graduation, course mate ɗina duk sun kama gabansu har ɗan uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ɗan uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saɓanin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ɗan uwana maƙudan kuɗin aikin da mahaifinmu yay aiki a ƙarƙashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ɗan uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ƙasar, bakuma susan ainahin ƙasar daya tafi ba. Yadai bar musu kuɗin da zasu ishesu, tare da musu alƙawarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaɗan labari. Nayi ƙwafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haɗa harƙalla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuɗin. Sunko amince tare da min alƙawarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faɗaba nasan ɗan uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”. “Ban sake sanin ina ɗan uwana yakeba, ba kuma mu sake haɗuwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alƙawarin daya ɗaukama iyayenmu na komawa garesu da daddaɗan albishir. A lokacin naje kai kaya ƙasar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ɗina tare da balarabiyar yarinya dana taɓa haɗuwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ɗan uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ƴan yanki ɗaya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaɗarsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”. “Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faɗa ina dariya da tafa hannu, kafin na miƙa hannun ya ɗoramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ɗan uwana kaɗan. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faɗin mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haɗu. Na amsa masa da jin daɗi, dan koba komai ina buƙatar keɓancewa dama da ɗan uwana dan naji yaya batun kuɗin daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaɗan banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buƙaci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danƙareriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haɗarin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ƙaton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ƙoshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ɓoye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”. Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haɗu a jami'ar Italy dakaƙi nutsuwa ka ƙarasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ɗaya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ƙaunarta. Nai alƙawarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ƴan uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ɓacin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taɓa shiga tsakanina da itaba. Bata taɓa yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ƙyau. Ni bamma taɓa kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haɗa jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ƙasa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ƙasar saudi-arebia suka fahimci jirgi ɗaya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaƙar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga saɓanin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ɗin. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ƙyauta maiban mamaki ta maƙudan kuɗaɗe wai na riƙe kaina, tare da haɗani
Chapter 203 · 0% Book details