← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 211

Sashe 57

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Sai dai kuma addu'ar tasu bataci ba, dan bayan kamar mintuna ashirin da barin Yoohan wajen Rich da ya ga bai dawoba ya miƙe ya biyo bayansa bisa umarnin Madam Chioma. Yanda yaga Guards ɗin sunyi diri-diri da idanu lokacin da yake tambayarsu ina Yoohan ya sakashi daka musu tsawa. Sake rikicewar sukayi, kowa na inda-indar bada amsa. A haka Madam Chioma itama data biyo bayan Rich ɗin ta samesu. Sake ruɗewa sukayi, dan sunsan idanma azaba ce tafi papa akan Yoohan, ga Rich shima ɗan babu sauƙine.
    Da ƙyar driver ya iya dauriyar faɗa musu yanda akayi, jikinsa har rawa yakeyi. Yanda Madam Chioma ta rikice sai ka rantse yaronta ɗan shekara biyu ko uku ne ya ɓata. A take ta birkice lissafin Guards ɗin Yoohan da securitys ɗin church ɗinma kansu. Ta kuma tabbatar musu nanda awa biyar idan Yoohan bai dawo ba saisun gane kuransu.
      Ana a cikin wannan dambarwar ne aka tashi daga church ɗin. Mutane suka fara tururuwar fitowa suna nufar inda ake rabon abinci. gudun kar ai abin kunya Rich ya shiga lallaɓa madam Chioma akan ta kwantar da hankalinta maybe Yoohan gida ya nufa, tunda duk sunsan a yanayin da yake baya buƙatar kowanne kalar hayaniya. Zata iya yuwuwa ya ƙosa ne da zaman shiyyasa. Da wannan ya samu yaci ƙarfinta suka koma ciki inda suka tarar duk wanda zai fita sai yaje ya jefa kuɗin baikon sa tare da karɓar wani abu da papa ke saka musu a baki sannan mutum ya fice.
     Matsawa madam Chioma tai kusa dashi tai masa magana a kunne, kansa kawai ya gyaɗa mata yana murmushi. Ita kuma ta juya ta fito yaranta da su Mira na biye da ita. Koda suka fito sai manyan mata suka zagayeta anata miƙa gaisuwa ga matar Pastor, harma da mazan da matasa kowa burinsa ya gaisheta. Yayinda wasu keta tambayar ina Yoohan dan sun riga duk sun gansa ɗazun. Da yake shi dama zuwan nasa bawani sosai bane saboda yanayin aikinsa sai yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa a daren sha biyar.
      Cike da yaƙe madam Chioma ke basu amsa da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay gaisuwa da kowa.

      Da ƙyar ta samu kanta daga wajensu, gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira yaƙi ɗaga waya. Daga ƙarshe ma wayar bata shiga.
     Tun shigowar motocinsu ƙaton harabar gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam Chioma ta ƙwalama maigadi kira cikin ƙaraji. Jikinsa na ɓari ya ƙaraso gareta cikin cika umarni.
            Kafinma takai ga jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar Yoohan baizo gida ba. Gaba ɗayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo waya suka shiga nemansa..........😒

🙄😏Mufa an ishemu kamar wani ɗan gwal🤕😤.

_____________________________

          Koda Yoohan yabar gidan wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ƙyar yake jan motar saboda nauyin jiki dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
        Yana tsaida motar a inda ta dace ya ɗan kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ɓangaren na ƙarfafasa akan dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. Ɗagowa yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa tana gab da tsinkewa.
          “Na shigo” ya faɗa kawai cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da buɗe motar ya fita.
       Wani matashin saurayi da zasu iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ɗauke da murmushi. Kallo ɗaya zakai masa ka shaida shiɗin musulmine, dan yana sanye cikin shadda bara sol dataji ɗinkin tazarce, ga ƙaton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza baƙar dara mai taushi.
           Tunda ya tunkaro Yoohan ɗin kallonsa yake ta ƙasa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa yana busar iskar dake kaɗawa ta hantsi mai gauraye da ɗumin rana.
         “Ina fatan dai baƙo nane?”. Saurayin yay maganar fuskarsa ɗauke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa ya gama shaida Yoohan ɗin ba musulmi bane.
     Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai batun yanzuba, a mabanbanta ƙasashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar yanda aka ɗorasa a hakan tun ƙuruciya. Ya dai yarda zai ƙyautatama mai buƙatar taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
      Sai dai kuma gashi yau a karan farko na tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a jikinsa. Duk da babu ɗigon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai miƙama saurayin hannu.
        Saurayin ya sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yana faɗin, “Ina godiya ƙwarai da amsa wannan gayyata tawa da banyi zaton zata karɓu ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan kamfani namu mai albarka”. Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. “Dr Yoohan Goshpower”. Ya faɗa a hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ɗinsa mai amo fita da ƙyau ba. “Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor”.
       “Karka damu” Yoohan ya faɗa a taƙaice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ɗinsa dake a haɗe masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci da lafiya ga jikin al'umma.
    Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ɗin. Godiya Yoohan ɗin ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gyaɗa kansa tare da yima kansa mazauni shima.
     Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ɓoye-ɓoye Hamza Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da miƙa masa envelope yana faɗin, “Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar amma taƙi isa gareka. Shiyyasa na buƙaci dama nazo ni gareka da kaina na kawo maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
       Yoohan daya gama duba takardar ya ɗan ɗago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya haɗiye abinsa a rai yana ƙoƙarin maida takardar cikin envelope ɗin.
         Duk da Hamza yayi mamaki da ganin Yoohan ɗin a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya haɗiye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce, kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, “Yallaɓai ina fatan dai zaka amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a gareka domin nuna girmamawarsu a kanka”.
      Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman hikima sukai masa daɗi a rai, har yay wani ɗan motsi da laɓɓansa mai kama da murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ɗan lumshe na wasu sakanni yana nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar hayani, ba kuma ya buƙatar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ƙuntatama wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa.
     Buɗe idanunsa yay a hankali ya ɗan gyaɗa kansa, “Babu damuwa zanje ɗin, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai”. “Ni kuma Doctor?”. Manager ya faɗa yana ɗan waro idanu. “Indai kace bazakajeba nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka buƙaci yimin karamcin da bai shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai shiga tarihin farko da ƙarshe na rayuwata”.
         Manager ya gyaɗa kai a ransa yana faɗin ‘daga ganin wannan a Christians ɗinma inaga ɗan ɗariƙar Catholic ne, ALLAH yasa ina ɗaya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu haske’ a zahiri kuma sai yay murmushi da faɗin, “Babu damuwa, indai kana buƙatata a tawagar masu rakkiya bazan ƙi ba”.
    Hannu Yoohan ya miƙa masa tare da yin godiya, kafin ya miƙe alamar zai wuce dan yasan hankalin families ɗinsa nacan a tashe da rashin ganinsa.
     Har mota Manager yay masa rakkiya yana ƙara masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ɗin ke jin daɗin shigowarsu cikin manyan Customers.

★★★

         Lokacin da Yoohan ya iso gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma yana shirin kiran police station yay report.
     Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai abinda ke faruwa a gidan, dan yaga baƙin motoci da yake ƙyautata zaton na Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ɗinsa da sauran securitys ɗin gidan na sauke manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba ya nufi ƙaton ƙofar falon nasu na glass da yaja manya kuɗaɗe masu nauyi koda ba'a faɗaba.
Chapter 57 · 0% Book details