Sashe 189
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom ɗinki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta faɗi ƙasa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji ƙarar Nu'aymah datai sau ɗaya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin ɗaukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan shaƙama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu'aymah ta faɗo a gadon?. Ban sake yunƙurin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta ƙarshe. Sai dai na saka an daɗe bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na haƙiƙa a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba.......” “Mtsoww!! Malami ko boka dai”. Abban Abdallah ya faɗa a fusasce. Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta ɗauke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah ɗin bai sake cewa komaiba. Addah ta cigaba da faɗin, “Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma laɓe da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya shaƙi iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar laɓe ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan faɗa miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku laɓe na fahimci kina bala'i-bala'in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai ƙananu kawai. Hakan yasa nima na ɗauki ɗammarar bi dake ta yanda kikazo min”. Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood ɗinsa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai haɗiyeta da su. Murmushi tayi da ɗauke kanta ta cigaba da faɗin, “A dalilin son halaka Muhammad na haɗu da babban makirin daya ƙara faɗaɗa ƙwaƙwalwata akan ƙiyayyarki da zuri'arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan”. Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai miƙe a fusace amma Hajjo ta riƙoshi cikin fushi. Babu wanda bai zaro ido ba a jama'ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana ƙoƙarin ƙwace hanunsa daga hajjo. “K baƙar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?”. Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, “Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haɗuwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ɓoyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ɗin nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ƴaƴana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ƴaƴanka da sauran ƴan uwanka susan kai wanene a cikinsu”. Sake zabura yay kanta kuwa da ƙarfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ƙafarta kaima. Ka nutsu ka riƙe sauran mutuncinka”. Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taɓa kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaɗin da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiɗa labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne. A hankali baba malam ya yunƙura ya miƙe hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ɗaya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ɓoye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ƙarta. Bana buƙatar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n.......” “Dolene kuwa kaji ɗan malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ƙetare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa. Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faɗin, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huɗubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ƴaƴa nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ƴan uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ɗaya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ɗaya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ƙarƙashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaƙuwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaɗan soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ƙuruciyarsu. Dan bazaiyi wasaba wajen ɗora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. Ɗari bisa ɗari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faɗaɗa min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunƙulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ƙara tashi yake gameda haɓaka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roƙo. Shima kuma sake ɗaukaka yakeyi fiye da sauran ƴan uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ɗaukakar tasa itama tana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara ɗora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ɗaya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaƙuwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaɗaita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ɗaukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huɗuba itake wargaza mana komai ta hanyar ƙaunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ɗaya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daƙile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheƙa mu samu abinda muke buƙata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ƙaninta abune mai sauƙi a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ɓoyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na ɗauka kawai ƙuruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuƙa matuƙa, dan ina buƙatar farin cikin ƴaƴana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu'aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka ɗin idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu'aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni ɗaura auren Adawiya da Abdallah ya ɗan min daɗin da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruɗanin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba'a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina ƙiyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suɓucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har ƙura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaɗan kwanta”. Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba. Addah ta cigaba da faɗin. “Mun sake son ƙulla auren Abdallah