← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 211

Sashe 195

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

     Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ƴaƴan Addah dake aure da ƙannen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ƙarshe baba malam dake ta ƙoƙarin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ƙaddara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.
     Baba malam ya ƙara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurɓata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ɓale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ɗora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ƙarfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ɗin nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faɗansu da Aymah harta faɗa a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ɗin. Har suka shiga mail ɗin kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaɗai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.
     Lokacin da Nu'aymah taji ƙamshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ƙarfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaɗe Yoohan ɗin yana faɗin. “Kai shasha minene haka?”.
     Murmushi Yoohan yayi sannan ya haɗe fuska. Cikin ƙanƙance ido ya nuna Abdallah da faɗin, “Idan ka bari gangancinka ya ɗora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ɓata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.
     Yana gama faɗa yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuɗi.
      Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ƴan uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faɗa a rayuwarsa. Dai-dai da film ɗin faɗa Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.
      Ƙin faɗama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ƙudirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuɗi. jin maƙudan ƙuɗin da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuɗin, sauran kuwa sai aiki ya kammala.
      Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ƙafar dama. Yo ko Yoohan ɗin sukace ta bibiya akan waɗanan kudin ai ta halakashi kuwa.
       Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.
     Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haɗuwa da Abbansa. koda suka haɗun Abban ya dinga masa faɗan da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taɓa nunawa ko da Umm ba balle su..........✍  
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 75

.............Su Jay dai sun wuce abuja, amma  duk da su Addah na a asibiti suna a ƙarƙashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu'aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ruɗanin data shiga. Ga jininta yaƙi sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm kaɗai ba hatta da ƴan uwan Umm dana Addar wannan al'amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba daɗin zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
      Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala'in gigice ya ke da al'amarin. Bai taɓa ƙawowa a ransa cikin ƴan uwansa za'a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dauɗar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ɓoye, har ji yake gaba ɗaya ƙasar ta fita masa a arai.

___________★★
Chapter 195 · 0% Book details