Sashe 52
Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
..............Aiko ALLAH ya amsa masa, dan cikin amincinsa Yoohan na komawa gida bai rufa awa ɗaya ba wani irin barci mai daɗi da saka kwanciyar hankali yay awan gaba da shi. Sai ga Yoohan da ya kwanta tun kusan shida na yamma bai farkaba sai goma na safiyar washe gari.
Wannan al'amari ya bama Yoohan da su Papa mamaki, suka shiga masa tambaya akan yaya akai yay barci jiya?. Bai ɓoye musu komaiba ya basu labarin haɗuwarsa da mutumin da bai sani ba, bai kuma san inda zai sake samunsa ba a yanzun. Duk da sunji daɗin hakan sai suka nuna rashin damuwarsu da sanin wanene mutumin ko inda zasu samesa, saboda kawai sun fahimci musulmi ne. Yoohan ɗin kuma ya koma inda suka haɗu da mutumin har kusan sau huɗu bai samu koda mai kama da motarsaba ma balle shi ɗin. Haka ya haƙura badan yasoba ya koma makaranta.
Wannan shine dalilin samun sauƙi sosai daga matsalar Yoohan, ya koma yana barcinsa lafiya lau kamar kowa, sai dai lokaci-lokaci abin nasa kan buga, idan kuma ya juyo yana tsintar kansane cikin mawuyacin hali na baƙin rai da fushi da tsangwamar kansa. Dama gashi dalilin hakane sanadin maidashi mutum mara fara'a da son hayaniya.
To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Yau kwanakinsa uku kenan da dawowa ƙasar, amma ko barcin mintuna goma ya kasa ɗaukarsa. Yanda yake ganin rana haka yake ganin dare. Ya mugun fita hayyacinsa a kwana ukun nan, ya daina magana da kowa, abincima ya masa yajin aiki sai abinda ba'a rasaba yake ɗanci idan yaji yana neman halaka a banza.
★★★★
Cikin murya mai cike da lallashi papa ke kiran sunan Yoohan ta jikin Window da suke a tsaye shi da Madam Chioma. Duk da yana jinsu bai fasa wurgi da abinda duk yaci karo ba a ɗakin, har wani sashe na gilas ɗin dake zagaye da ɗakin ya tsage, dan ya jefa ƙarfe ne ya bigi gilas ɗin dake a matsayin bango ɗakin.
Sai da ya jigata dan kasan sannan ya zube a ƙara yana wani irin sauke ajiyar zuciya mai ƙarfin daban tsoro.. Duk da hankalinsu ya ɗan kwanta ganin yabar jefe-jefen basu daina kiran sunansa da roƙon ya buɗe musu ƙofarba cike da lallashi. Shi kuma yayi banza dasu tamkar baisan da zaman nasu a wajenba.
Papa ne ya tuna da extra keys ɗin sashen nasa, dan haka yabar wajen Window da sauri zuwa bedroom ɗinsa. Mintuna ƙalilan sai gashi ya dawo cike da farin cikin samo keys ɗin. Hakama Madam Chioma saboda daɗin da taji har kiss taima papa tare da rungumesa. Zagayawa sukayi domin buɗe ƙofar, sai dai kuma key ɗin yaƙi shiga alamar yabar wani key ɗin a ciki. Ransu duk a jagule suke bin ƙofar da kallo, madam Chioma har hawayenta sun dawo kwarara.
Solomon ne ya kawo shawarar bin ƙofar can baya dake sada mutum da ɗakin motsa jikinsa kai tsaye. Su ruɗewama ta sakasu mantawa da ƙofar. Da sauri suka zagaya tacan, cikin amincin ALLAH kuwa suna gwada key ɗin da suketa kokwanton ba nata bane sai gashi ya buɗe musu.
Har rige-rigen isa garesa kuwa sukeyi. Duk da yana jinsu bai motsa ba, sai da sukasha fama, dan Yoohan akwai taurin kai dama, da ƙyar ya yarda suka tadashi zuwa ɗakinsa. Madam Chioma da kanta ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda papa ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama tana tasiri ga Yoohan ɗin.
Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Yoohan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu, matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda papa yay masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur. Cike da basar da abinda ya fahimci zatayin ya nufi toilet yana ɗingishi, dan da alama yaji ciwo a ƙafar tasa ne.
Duk binsa da kallo sukai ita da papa, yayinda ranta ya sosu sosai akan yanda Yoohan ɗin keyi mata a duk lokacin da ta nufi yimasa makamancin waɗan nan abubuwan. Tarasa dalilinsa na yimata hakan, ‘shi kodai ya fara tunanin.......’ sai kuma ta kasa ƙarasawa ta girgiza kanta alamar ba haka bane. Dariyar papa ta sakata saurin kallonsa. Ya ɗage mata gira da matsowa shi ya rungumeta yana faɗin, “Ɗanki fushi yakeyi dake yau, kinga yamaƙi yarda ki rungumesa. ni zo na rungumeki”.
Fuskarta a yatsine taɗan turesa, cike da salon yaudara ta matsa baya da juya masa keya irin maganarsa ta ƙara mata haushin nan. Shiko ya sake matsowa jikinta ya rungumeta ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. “Wasa nake miki Momyn Yoohan, shima nasan yanayin da yake cikine kawai ya sakashi aikata miki hakan”.
Duk da haushin da take ciki sai maganar papan taɗan sanyaya mata rai, dan ita ada tunaninta ba haka yake kawo mata ba. Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Darling! Anya kuwa bazamu nema mutumin nan daya taɓa yimasa maganiba shekarun baya da suka wuce sannan muna farko-farkon zuwa Abuja?”.
Papa dake kallonta ya ɗan ɓata fuska yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune momyn Yoohan, sai dai kuma a ina zamu samesa? Shi kansa Yoohan ɗin bana tunanin zaima iya ganesa idan ya gansa ai”.
Kafin ta samu damar bama papa amsa Yoohan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu fuska a turɓune.
Ahankali madam Chioma ta sauke idanunta akan buɗaɗɗen jikin yaron nata dake ɗauke da wata lafiyayyar farar fata mai santsi da ɗaukar idanun mai kallonsa. Basai an faɗaba a kallo ɗaya zaka fahimci shi ɗin ya tashi cikin kulawar rayuwa da jin daɗi, dan sam babu alamar rama tattare da shi......
Jikinsa ya fara ja da baya yana ƙara tamke fuska, hakan yasa Mom saurin tashi tsaye har tana neman faɗuwa, da yarensu tace, “Ina zaka kuma yaro na? Kaga zo na shafa maka man ma da kaina idan bazaka iya b.....”
Kafin takai ƙarshen maganarta harya maida ƙifar bayin ya rufe, jingina yay a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara ƙarfin bugu. Duk da yanda take buga ƙofar a hankali tana kiran sunansa bai motsa ba, sai ma wani haushi dake sake ziyartarsa. Sam bayason wannan halin da Mom take masa, a ganinsa bai daceba, yakamata tasan da ba yanzu bane, yanzu fa ya girma, shekararsa talatin har da biyu a duniya, miyasa bazata daina masa kallo kamar ɗan shekara goma ko ƙasa da hakaba?. bawai yana saka abinda take masan a wani mizani daban bane, dan yasan soyayyar da suke masa mai yawa ita da papa ne ya jawo hakan, amma ya kamata ta fahimci yanzu ya wuce ta dinga masa wasu abubuwan kanta tsaye ai......
A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Papa ke lallaɓa Mom akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya.
Badan madam Chioma taso hakanba ta yarda suka fita ɗin ranta na mata ƙuna.