← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 193 OF 211

Sashe 193

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sanin rayuwarba balle daɗinta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”. Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ɗaya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaɓa yaya malam ta ƙarƙashin ƙasa aka maidasa Abuja aka buɗe masa company wanda ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ƙarshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuɗaɗen company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ƴan ƴaƴansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ƙananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haƙƙin yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ƙyautata rayuwar ƴaƴanmu a gidan nan. Kaɗanma kuka fara gani yanzu kuma”. Momyn Abdallah daketa kuka tun ɗazun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaɗai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haƙƙinmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ɗaura ɗammarar shiga haƙƙin wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ɗan adam ɗin da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuɗin neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raɓe-raɓe basu da ko kangon da zasu raɓa. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ƙasƙance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waɗanda suka raɓu da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ɗari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ƴaƴa maza da mata, ga wasu can suna nema da miliyoyin kuɗaɗe basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baɗala. Duk waɗan nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waɗan nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waɗanda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ƙoƙarin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baƙin cikin cigaban mai ƙyautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ɗoramin yaro akan mummunar aƙida da kukayiba........” Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ƙwaƙwaran motsi, kansa duƙe a ƙasa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake. Baba malam ma dai kansa a ƙasa yake duƙe. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?..... Jin kowa bai ƙara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faɗin, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haɗa bayanansu sai mu miƙasu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”. Tari Addah ta fara kaɗan-kaɗan, hakanne ya saka baba malam ɗagowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ɗaya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miƙata asibiti kawai....” Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ƴan baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ƙarƙashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya ƙare maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune. Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”. Tarin Addah daya ƙara ƙarfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ƙareba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haɗa duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ƙaramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buɗe masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba. Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saƙo na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuɗe. A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje. Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ɗagawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”. Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.
Chapter 193 · 0% Book details