← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 211

Sashe 13

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        A washe garin da aka cika kwanaki goma da faruwar al'amarine tafiyar Adawiya da Abdallah ta kama.
      Umm da kanta ta samu Addah har ɗaki tai mata ƙorafi akan yanda take share Adawiya. Sai da ta nuna mata ɓacin ranta akan hakan sosai sannan ta ɗora da mata nasiha akan ta yarda da ƙaddara mana.
        “Addah Minene laifin Adawiya tunda ba itace ta saka a ɗaura mata aure da Abdallah ba. Ba kuma itace tabama Nu'aymah shawarar ta gudu ba. A ganina addu'a ya kamata mubi yarannan da shi tare da fatan alkairi bawai tsangwama da hantara ba dan su basu da laifi”.
        “Umm bazaki ganeba wlhy, ke dai kibar......”
      “Naji bazan ganeba Addah”. Umm ta dakatar da Addah da sauri. Ta cigaba da kallonta tana faɗin, “Baki da wani abinda zaki faɗamin da zaki kare kanki, ni dai kawai ki dawo rayuwa da yaran nan kamar yanda kikeyi da. Ki kuma yima Adawiya fatan alkairi kodan sabuwar rayuwar da zata fuskanta a yau dan girman ALLAH”.
      Shiru Addah tai tana sake jinjina ƙyawun zuciya irin na Umm, haka take ita komai tana ɗaukarsa da sauƙi a rayuwarta bata zafafama kanta. Tunda abinnan ya faru babu wanda ya taɓajin furucinta kosau ɗaya akai. Ko a fuska ƙoƙarin ɓoye damuwarta takeyi. Tausayin aminiyar tata kuma ƴar uwarta sai ya sake kamata fiye da da can.

     Umm da kanta ta fita taje ta shigo da Adawiya, zaunar da ita tai kusa da Addah itama ta zauna. Su biyu suka shiga yima Adawiya nasiha kamar yanda sukeyi a duka sauran ƴaƴan Addah uku da aka aurar. Sumayya, Maryam, Badariyya. Sai da sukai mata nasiha sosai kafin Umm ta tashi ta fita ta bar Adawiya da Addahn. 

★★★★

        Kamar yanda tsari da al'adan mutanen gidan yake bayan sallar la'asar iyayen suka sake haɗuwa aka rufu kan Adawiya da Abdallah akai musu faɗa da nasiha sosai. Tare da gindaya musu sharuɗa masu tsauri akan duk wanda wani al'amari mara ƙyau ya ɓullo daga wajensa a cikinsu to lallai zai fuskanci ɓacin rai da fushinsu sosai. Daga ƙarshe aka sake musu doguwar addu'a aka sallami Adawiya da ko sau ɗaya batai hawayeba da iyayensu mata.
     Umm ta tafi da Adawiya sashenta danta kimtsata, suka bar Abdallah tare dasu Baba Malam da Hajjo da suka sake ɗora masa da Nasiha kasancewarsa shine babba.

        Ƙarfe 7:30pm gayyar yaran gidan harna ma'auri su Aysha sukaima Abdallah da Adawiya rakkiya airport dan jirgin 8:30 zasu bi zuwa ƙasar Dubai. Sai sunyi kwanaki goma acan kamar yanda Abdallah ya tsarayi da Nu'aymah sannan su wuce Saudia.
       A yanzuma dai idanun Adawiya ƙifi-ƙifi babu ko ɗigon hawaye a cikinsu. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Addah yayiba. Hakama Momyn Abdallah al'amarin ya bata tsoro, taita kallon Adawiyar cike da alamomin tambaya a ranta, sai dai bata furtaba.

            Ko kaɗan Yusrah bataji komai a rantaba, dan ko kusa bata kawo Adawiya ma a cikin matsalolinta saɓanin Adawiyar dake jin zafin Yusrah babu gaira babu sabar. Ita Yusrah dama za'a warware nata auren da tayi matuƙar farin ciki. Amma ta ɗauka alwashin cigaba da addu'oi tana gayama ALLAH kukanta akan hakan kafin lokacin da akace zata tare.
      Basufi zaman mintuna talati da huɗu ba aka sanar da tafiyarsu. Sai yanzune Adawiya taɗanji babu daɗi a cikin ranta na kewar ƴan uwanta. Amma saita fuske ta shiga binsu ɗai-ɗai tana rungumarsu. Da tazo kan Yusrah saita wuce batace mata komaiba. Ba ƙaramin mamaki hakan ya bama kowaba, duk suka bita da kallo har Yah Abdallahn. Tsarguwa da tai ne ganin yanda ƴan uwan nata ke binta da kallon tuhuma ya sakata buɗe jakkarta ta ɗakko wani abu ta nufi Yusrah, hannunta ta kama ta saka mata abin sannan ta rungumeta kamar yanda taima kowa.
      A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, dan da da yawansu abun yay musu cak a ƙirji hatta da ƴan uwanta da suka fito ciki ɗaya. Musamman Hajarah da taga abinda ya faru a ranar ɗaurin auren tsakanin Addah da Adawiyan.
     Sallama suka sakeyi da juna. Kafin tabi bayan Yah Abdallah da yay gaba abinsa batare da ya saurareta sun jera tareba kamar yanda taso.

“Hummm!! Wasa farin girki Adawiya👁👎🏻”.

___________________
NU'AYMAH
______________

              Tun randa aka barota daga gida bata sake sanin halin da take a ciki ba sai washe gari da yamma. Farkawa tai a tsananin firgice. Sai dai nauyin masifa da kanta yay mata na azabar ciwo ya sakata sakin ƴar siririyar ƙara da dafe kan nata da hannu bibbiyu tana sakin numfashi a wahale.
        Sake ƙoƙarin buɗe idanunta tai da ƙyar saboda nauyin da sukai mata suma. Tabi ɗakin da take ciki da kallo mai ƙaracin haske, sai dai ba dunɗum yakeba. Katifa ce kawai a ɗaki da wasu lalatattun akwatuna guda uku kalar ruwan ƙasa. Sai takalma na maza da aka jera a gefe kusan ƙafa shidda. Sai hanger a jikin bango anyi hanging farar jallabiya ta maza guda ɗaya da wanduna uku duk baƙaƙe. Sake lumshe idanunta tai ta buɗe a hankali dabin jikinta da kallo.
     Hijjabin tane dai a jikinta har ƙasa da ta saka lokacin da zata fita neman wayarta. Ta kai hannu da ƙyar ta laluba jikinta. Towel taji wanda shima shine tasan ta ɗaura a jiyan, sai dai yanzu ya kwance duk ya zazzame daga ƙirjinta ya dawo saman cikinta.
      Juya mata da garin ya farayine ya sakata yin baya ta sake kwanciya a katifar hawaye masu a zabar zafi na silalo mata a saman kumatu. A haka ta cigaba da kwanciya tana zirarar da hawayen jikinta duk babu wani ƙarfi. Tafi mintuna talatin da kwantawa sannan aka buɗe ƙofar.
    Kasa buɗe idanu tai balle taga wanene ya shigo ɗin, tsahon mintuna biyar kafin ta buɗe idon kaɗan ta saukesu akan wanda ke tsaye jikin ƙofa sanye da baƙaƙen kaya, hatta da hannunsa akwai safar hannu baƙake. Hakama fuskarsa da facemask, idanunsa kawai take iya gani. Suma ganin kallon da take masa ya sashi ciro glasess ya toshesu.
    Basket ɗin dake riƙe a hannunsa ya tako gaban katifar ya ajiye batare da yace da ita uffanba ya juya ya fita. Maida idanunta tai da ƙarfi ta rumtse zuciyarta na zafi. Kukanma yanzu sai ya kasa fita mata. Haka ta cigaba da zama a wajen har bayan mintuna kusan goma da fitarsa. Sai kuma ga mace ta shigo sanye cikin dogon hijjab har ƙasa. Itama fuskarta sanye take da niƙaf.
     Batare da tama Nu'aymah magana ba ta kamata ta tayar. Bata da wani ƙarfi ko iya yin magana, dan haka ta cigaba da bin matar kawai a yanda taso. Ƙofa ƙwara ɗaya ƙarama dake a cikin ɗakin suka nufa, sai da suka shiga Nu'aymah ta fahimci toilet ne. Fas yake babu ƙazanta a cikinsa, saima ƙamshin omo da hypo daketa tashi.
      “Kiyi wanka”. Matar ta faɗa a taƙaice batare da ta jira amsar Nu'aymah ba ta fice abinta. Da kallo kawai Nu'aymah ta bita, sai dai bakinta ya mata nauyi ta gaza cewa uffan a yanzunma. Kamar bazatai wankanba sai kuma wani tunanin yazo mata. Rabonta da salla tun ta isha'in jiya. Ga shi a yanzu da alama har anyi sallar la'asar ma. Tana buƙatar ƙarfin jiki sosai, hakan kuma bazai yuwuba sai tayi wankan.
     Cikin ƙarfin hali ta zare dogon hijjabinta da towel ɗin, duk da tsaftar banɗakin a ɗarare tai wankan. Taji ƙarfin jikinta sosai, sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi a jajjere. Alwala tayi ta fito tana daddafa bango, dan akwai yunwa tattare da ita.
     Da mamaki ta kalli kayanta da aka ɗaura a saman katifar, ta bi ɗakin da kallo kamar ɗazun, babu kowa sai kayan a ajiye da kuma kwanikan abincin dake cikin basket ɗin suma an fiddosu ƙasa an ajiye.
        Bata da wani zaɓin daya wuce canja kayan tai sallolin dake kanta. Harta kammala rama sallolin babu wanda ya sake shigowa, ta kwanta saman abin sallar tana hawaye da tunanin ko wane hali yanzu Umm da Abbanta da Muh'd dama duka sauran ƴan gidansu suke ciki a yanzu na rashin ganinta?. Yah Abdallahn ta, tasan zaifi kowa shiga tashin hankali bayan Umm da Abbanta. ‘Minayi suka kawoni nan? Su wanene su? A ina nake?’. Ta faɗa a fili tana sake fashewa da kuka. Taja tsahon lokaci tana ribzar kukanta, har kanta yana masifar sara mata fiyema da ɗazun. Barcine ya fara figarta na wahala. Jin motsin shigowar mutum ya sakata tashi zaune zumbur. Matar ɗazunce, yanzuma batai mata magana ba ta ɗakko kwanikan abincin ta kawo gabanta da mata alamar taci.
      Yunwa Nu'aymah takeji sosai, dan haka batai musu ba taja abincin tahau cinsa. Taci sosai har matar tai mamakin hakan. Matar ta miƙe zata fara tattare kwanikan Nu'aymah ta kalleta cike da rashin tsoro tace,
       “Su wanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku kuma?”.
     Kallonta matar tayi sosai, amma sai batace da ita komaiba ta tattara kwanikan tai ficewarta.
        Tashi Nu'aymah tayi ta nufi ƙofar da sauri, sai dai tana taɓawa tajita a kulle, fashewa tai da kuka ta koma saman katifar ta sake kwanciya tana sambatun kiran Umm da Abbanta da Yah Abdallah.

        Tun daga wannan ranar kullum hakan ta cigaba da faruwa, zasu kawo mata abinci sau uku a rana, matarnan zatazo ta gyara ɗakin ta wanke mata bayi da kayan data cire. Sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta sakata cin abinci. Tambayar duniya tai mata bama bata amsa, haka shima namijin idan zai shigo sau goma tai masa magana baya ko mata tari. Iya kacinsa ya leƙo ya ganta ya koma.

     Haka Nu'aymah ta cinye kwanaki goman nan cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. Babbar damuwarta halin da ahalinta zasu shiga na rashinta. Musamman ma Umm ɗinta da Abbanta da Yah Abdallah da Hajjo. Tayi kuka harta gaji ta bari ta koma gayama UBANGIJI kukanta. Dan tasan shine mai rahama mai jinƙai. Ya fita sanin dalilin da yasa ya jarabceta da wannan al'amari a daren ɗaurin aurenta da yayanta masoyinta.
Chapter 13 · 0% Book details