← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 211

Sashe 93

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Bayan samun damar shiga ɗakin da Nu'aymah ke kwance da sukayi ɗai-ɗai suka dubata duk da bata farfaɗo ba baba malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba'a buƙatar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfaɗo.
      Suna tafiya baifi da mintuna talatinba shima ya amshi key ɗin motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ɗin. Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi. Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
      Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai ta danne ta amshesa da fara'a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji daɗi kuwa sosai, tare da sake jin ƙaunar ƴar tsohuwar har cikin ransa.
     Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu.
     Bayan shuɗewar shiru na wasu mintuna Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
            Sosai mamaki ya kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya ɗago ya duba baba malam, “Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba taɓa aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ƙasata. Nasan anyi hakane kawai don shiga tsakanin alaƙarmu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu. Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ɓatanci da za'aimin koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi kaɗai. Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ɗaya ba ma, dan kuɗin nagartattun mutanene masu ƙyawawan zukata. Zan faɗa muku ainahin gaskiyar abinda ya faru”. Cikin nutsuwa da ɗacin rai ya bayyana musu tun daga haɗuwarsa da Nu'aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ƙarya ba tun yana kafirinsa, balle yanzun da ya ƙara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ɗan adam. dan haka ko kissing ɗin Nu'aymah da yayi bai ɓoye musu ba ya faɗa. Ya ɗora da faɗin, “Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku alƙawarin bincike akan cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku hujja a yanzu da yardar ALLAH”.
      Gaba ɗaya sun gamsu da bayaninsa har Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ɗin dan da turanci yay bayaninsa.
       Baba malam ya ɗanji nauyin zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi kwanciya da binciken Yoohan ɗin fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya fara karkata akan wani abu da ban kuma.
    Ko mintuna goma Yoohan bai ƙara a gidanba ya fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun ƙarama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ƴaƴansu. Ya sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ƙyamatar abinda wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe take masa daban akan wannan ƙullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma zuciyarsa na kinsa masa papa.

           Tare suka koma asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ɗinba.
     Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk wani bincike akan Nu'aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta danƙama wanda ta aminta da shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
     Kansa kawai ya iya ɗaga mata, dan yana lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take matuƙa. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya taɓukawa a wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da leƙa Nu'aymah da suke tsumayen farfaɗo warta a kowane irin lokaci.
       Misalin ƙarfe biyar saura na yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ɗin bincikensu. Ko buɗewa baiyi anan ba ya miƙe da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da Ahmad biye da shi.
      Har zuwa yanzun su baba malam duk suna gida suna jiransu. Yanzun dai saɓanin ɗazun, duk mazan gidan ne suka taru banda ƴammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce kaɗai mace ma a cikinsu. A maimakon Yoohan ya buɗe yanzun ma sai ya bama Abdallah damar buɗewa dan ya tabbatar musu zai gane.
            Tun a result ɗin farko Yoohan yaji saɓanin abinda yay tsammani. Hakama sauran ƴan gidan, aka tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ƙarasa na ukun ba Yoohan ya miƙa hannu a hankali ya zare file ɗin da takardun results ɗin ke a ciki yana binsu ɗai-ɗai da kallo. Tabbas babu ƙarya dai-dai Abdallah ke faɗa. Dan kuwa duk Results ɗin sun nuna Nu'aymah tasan ɗa namiji, ta kuma ɗauki cikin sati shida da wasu kwanaki, cikin kuma tayi ɓarinsa kwana biyu kenan.
      Dimmm kan Yoohan yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
       A harzuƙe Abdallah yace, “Yanzu kuma wace ƙarya zakai mana dan ka kare kanka?”. Yay maganar yana riƙo rigar Yoohan.
        “Abdallah!!!!” Abbansa ya daka masa tsawa yana miƙewa. Ransa a ƙololuwar ɓace yace, “Sake sa”.
        Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya saki Yoohan ɗin da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. Ɗan hankaɗashin da Abdallah yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ɗagowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin wajen.  A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da basira.
      Kallon sashen da baba malam yake yayi, ya ɗanyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ɗan sirka yana wani bahagon murmushi, kamar zai lumshe su sai kuma ya ɓuɗesu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai kauri da amo data hadu da ɓacin rai a yanzun yace, “Uncle wannan tatsuniyar akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ɗin fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi yarda da shiga ƙarƙashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma'adanai. Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba gangancine ya kaisa ba, tsabar ƙwarewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani aurenta idan ta girma?”.
         Kowa a falon sai da ya zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka tsaya akan ƙafafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu haɗiye Yoohan da ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ƙarasa Abban Adawiya ya daka musu tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
         A karon farko baba malam yay tattausan Murmushin da har haƙwaransa sai da suka bayyana. idanunsa ƙyam akan Yoohan. zamansa ya gyara da ƙyau yabi duk jama'ar falon da kallo, su Abban Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ƙarami ke fassarama maganar yoohan ɗin.
          Murmushi baba malam ya sakeyi a karo na biyu, kafin yace, “Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma kaje zanyi magana da ƴan uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka insha ALLAHU”.
         Duk da Yoohan yaso samun amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da hakan. dan haka ya miƙe yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da Abdallah da wani irin kallon na ban ƙyaleku ba kuma, kamar yanda suma suke binsa da kallon kishi da tsana.

       A yanzun kam zamu iya cewa komai ya harmutse musamman a gidan su Nu'aymah. Dan tun bayan barin Yoohan gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin baƙi akan kalaman yaron mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ɗinsa tamkar mai safa da marwa. Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matuƙar tashe yake, dan su dukansu suna tsananin son Nu'aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu'aymah ya kamata ta aura bane damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ɗiyarta shine tashin hankalinta. Itace ta haifi Nu'aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata taɓa kamata da kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ɗorata ba. To tayaya za'ace hakan ta faru?  Kanta ya kulle gaba ɗaya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci da Nu'aymah. Dan zuciyarta taƙi aminta ƴarta zata aikata haka, to sukuma likitocin mizaisa su musu ƙarya? Ta yama zasu musu ƙarya bayan sun kasance daban-daban?.
Chapter 93 · 0% Book details