← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 211

Sashe 111

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

       Yoohan dake can ɗakin Momy da itama babu lafiyar bayan ya lallaɓata tasha tea ya saka mata ƙarin ruwa. Sai da yaga barci ya ɗauketa ne ya zare hannunsa dake cikin nata a hankali ya lulluɓa mata bargo ya fito. A corridor yaci karo da Miracle. Kallo ɗaya yay nata ya ɗauke kansa saboda shegun kayan barcin dake a jikinta bata da maraba da tsirara. Da alama ma yanzu ta tashi barci. Cike da kishi tace masa “good morning”. Batare daya amsata ba ya wuce abinsa ya barta da ƙamshinsa.
      Sashen sa ya koma. Inda ya iske Solomon a falo yana goge-goge. Gaidashi yayi cike da girmamawa kamar yanda ya saba.
       Amsa masa yayi yana tura ƙofar ɗakin Nu'aymah ya shiga. Solo ya rakashi da kallo tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa. Oho baimasan yana yi ba, danshi tuni ya shige.
           Shashshekar kukanta daya faracin karo da ita cikin kunnuwansa ne ya sashi lumshe idanunsa a hankali ya buɗesu a kanta, cigaba da tsaiwa yayi a bakin ƙofar kawai yana kallonta kamar ya samu television. Ita kam bama tasan da shigowarsa ba, dan gaba ɗaya hankalinta da tunani yana kan ta yanda zata samu mafita akan wannan auren ne. Sai ɗunbin kewar iyayenta da ƴan uwanta dake gaba-gaba wajen tunzura kuka nata.
        A hankali ya sauke numfashi da zura duka hannayensa cikin aljihun baƙin wandonsa. Ya fara taka farar ƙafarsa dake fes babu wani datti a jikinta saboda tsabar saka kwaba shu da yake a koda yaushe ya ƙarasa har gaban gadon dai-dai saitin inda fuskarta take. Har fuska ta rufa bargon. Kaɗan yaja gajeran tsaki a maƙoshi, a ransa ko rayawa yake, ‘Sai shegen tsiwa a bakinta da ƙuruciya’. A fili kam sai ya ɗan ranƙwafo da zare hannunsa daga cikin aljihu ya yaye bargon daga fuskarta. Bai kai ga kaishi kafaɗa ba ta riƙe gam. Idanu ya zubama farar fuskarta da tai jazur musamman saman hancinta da idanunta. Dai-dai da ɗago nata kumburarrun idanun ta zuba cikin nashi. Sai dai sam kwarjininsa ya hanata iya cigaba da kallon tsakkiyar idanun nasa. Hakan ya sakata azamar janyewa tana kumbura baki fal da iska. “Malam ka daina shigamin rayuwa bana so”. Cikin yin ƙasa da murya yanda bazaiji ba tace, ‘Haka kawai a ringa shigoma mutum kai tsaye babu neman izini’.
      Baiji maganar data faɗa ba a ƙarshe dan da hausa tayi, ta farkoce dai tayi da turanci. Amma a yanda tai maganar yaji a jikinsa rashin kunya ce a ciki. Amma sai ya shareta bai kulata ba, sakin bargon yayi ya ɗora yatsunsa biyu a saman goshinta saboda ganin yanda jijiyar kanta tai ruɗu-ruɗu.
     Saurin ja baya tayi hawaye na sakko mata, “Nifa a daina taɓa ni bana so”. Ta faɗa tana hararsa ta ƙasan ido da murguɗa baki kaɗan.
       A karan farko da abin nata yaso bashi dariya, dan haka ya ɗanyi luuu da idanunsa tamkar zai lumshesu amma sai ya buɗe yana kauda kai gefe da sakin murmushi. Barin gaban gadon yayi batare da ya sake magana ba. Abincin da aka kawo mata ya bubbuɗe. Irish ne da ƙwai, sai farfesun kayan ciki, da gasashshen burodi da yaji haɗin salad a tsakkiya. Maidawa yay ya rufe sannan ya miƙe ya fita.
       Nu'aymah da duk tana kallon abinda ya keyi ta raka bayansa da harara tana faɗin, ‘Mutum babu abinda ya iya sai son taɓa jikin mutane dan kwartanci’. (Hhhhhh🤣 Aymah tamu ta mutunci, mutum ya sauke sadaki ki kirashi kwarto dan ƙarfin hali irin naki😂).
Chapter 111 · 0% Book details