← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 211

Sashe 102

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Ihun Nu'aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
       A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
        Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin, “Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
       Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi. Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
      Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake faɗaɗa.
       Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
      Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”. Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu'aymah a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
        Ƴar dariya Ahmad yayi yana ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A'a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
      Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ɗin? Tab za'aga likitoci kam”.

       Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
       Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
     Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita ta, ruɗanin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
      “Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
      A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.

         A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
       Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
       Koda suka koma can baba malam da kansa ya ɗauki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa. Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba.

         Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan.
      Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
      Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne.
     Haka suka fita a jere ana bin amare da addu'ar tafiya a sa'a. Dama mafi yawan ƴan biki na kusa duk sunata guduwa suma. Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun tafi.

★★★

        Su baba malam sun fara miƙa Hajarah ne dan itace ƙarama. Gidanta mai ƙyau da tsari a anguwar GRA, kowa ya yaba da addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ɗin suma cikinsu harda maza uku. Bayan sun ɗan zauna a falo akai addu'a baba malam ya kama hannun Hajarah har cikin Bedroom ɗinta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu'a da saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta riƙe hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa har ƴayan ƴan uwan nasa ƙaunarsu yake har cikin ɓargonsa. Duk kuma sanda yay irin wannan rakkiyar sai yayi ƙwalla dajin ɗacin rabuwa da yaran nasu ta dalilin aure ƙanin mutuwa.
     Hajarah data buɗe fuskarta ta share hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, “Abbah dan ALLAH inason in roƙeka wani abu”. Kansa ya jinjina mata, yace, “Komi kikeso zan miki inhar baifi ƙarfina ba Hajarah, dan haka faɗamin koma miye kinji”. Sake share hawayenta tayi tana jinjina masa kai. “Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa”. Jimmm baba malam yay yana kallonta. Sai kuma yace, “Uhm Hajarah miyasa kika buƙaci hakan? Bayan kinsan shi ɗin mai laifine”. “Abbah zan faɗa maka dalilina amma ba yanzu ba, dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na roƙesu har Hajjo”.
       Numfashi baba malam ya ɗan sauke, sai kuma yace, “Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki zazzaɓi. ALLAH ya baku zaman lafiya”.
    Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da rabzar kukanta.
      Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama dai gidan ya haɗu masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ɗakin ya ƙara mata addu'a sannan ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.

____________________
Chapter 102 · 0% Book details