← Book details Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 211

Sashe 149

Saran Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma kamar jiya bayan sallar asuba sunyi zaman karatu. Koda suka idan tasha magani shi kuma ya fita motsa jiki. Da ya dawo ma ya sameta tana barcin. Wanka kawai yayi ya fiddo lap-top ya fita ƴar barandar Aymah ta jiya bayan yayi order ɗin abinda zaici. Acan ya shafe tsahon lokaci har Aymah ta tashi a barcinta. Ganin baya ɗakin tai tunanin ko ya fita. Wanka tayo tazo ta shirya cikin sauran kayan jiya. Yau dai wando ne ta saka yellow da black t-shirt. Tayi ƙyau yauma sosai, ta gyara gashinta tana ɗan yatsina fuska ganin yana bukatar wanki. Badai tayi maganaba dan bason a taɓa mata kai takeba daman. Kobi takan abincin data gani batayiba. Ta ɗauki buk ɗin jiya dake a durowar gefen gadon ajiye ta nufi wajen zamanta na jiya. Kasancewar ya rufe yasa bata fahimci yana a wajenba sai da ta fito. Yoohan dake zaune a kujerar ya ɗora ƙafafunsa bisa table ɗin, lap-top a saman filo daya sa kan cinyarsa yanata aikinsa ya ɗago idanunsa jin sabon ƙamshin turarensa data bunkuɗa a jiki. Suna haɗa ido ta turo baki gaba tana kauda fuskarta. Baiyi maganaba shi dai. Bai kuma daina mata kallon ƙurilla ba, dan kayan sun matuƙar mata ƙyau, kodan yau ne ya fara ganinta a cikin irinsu oho. duk da kuwa yana bala'in son yaga tayi shigar Hausawa dan tana masa ƙyau. Amma yauma dai tayi irin ƙyawun da yake buƙatar ganinta a ciki. Haɗiye abinda ya tsaya masa yay a maƙoshi yana furzar da nannauyan numfashi. Yanda yayi ɗinne ya saka Aymah dake tsaye kamar an dasata kallonsa. da alama kunyace ta hanata motsi kokuma ganin da tai masa a wajen a bazata. Saurin janye idanunta tai ganin har yanzun kallonta yakeyi. Harga ALLAH ita tanajin nauyin ganinsa da kaya irin waɗanan. Rigace armless fara tas a jikinsa, sai wando dako cinyarsa bai gama rufewaba oxblood. Duk da lap-top ɗin daya ɗaura bai hanata ganin farare cinyoyinsa da gargasa suka kwanta ba.. Cikin sanyin muryar da baisanta da ita ba tace, “Good afternoon”. Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta. Sai kuma ya maida ga lap-top ɗinsa yana faɗin, “Same, How are you?”. Hararsa tai ta gefen ido saboda jin yanda ya amsa gaisuwar. Da tamayi niyyar komawa ciki, amma yanda ya amsa matanne ya sakata takowa ta ƙaraso inda yake. Kujerar taja itama ta zauna tanata wani faman haɗe fuska irin batason wargi din nan. Duk abinda takeyi Yoohan na kule da ita. Sai faman ƙoƙarin danne dariyar dake taso masa a rai kawai ya keyi. Aikinsa ya cigaba da yi ita kuma ta karatun novel. duk da kuwa bama karatun takeba satar kallonsa kawai takeyi tana gulmarsa a zuciya. Tunda ya fahimci kallonsa takeyi shima sai ya kasa ci gaba da yin aikin. Saboda tsabar neman magana ya tura ƙafarsa ya tanƙwaɓe littafin nata ya faɗi. Ya kuma fiske abinsa yaƙi kallonta tamkar bashi ne ya aikata ɗin ba. Ƙara tsuke fuska tayi tanabin buk ɗin dake yashe a ƙasa da kallo, ɗan bakin kuwa sai motsawa yake amma ta kasa magana. Cike da takaicin daya kumeta ta ɗauki filo ta maka masa a ƙafa harda cije baki. “Ouch!” ya faɗa yana saurin janye ƙafarsa. “Silly girl!. Wane mugunta ne haka? Mina miki?”. Harara ta balla masa. batare da tace komaiba ta duƙe zata ɗauki buk ɗinta. Sai dai kuma hannunta bazai kaiba dole sai tazo ta gabansa. Fitowa tai tazo har inda littafin yake. ta ɗauko harma ta miƙe zata koma inda take ya saka mata ƙafa. Sai ko gata a kan cinyarsa ɗare-ɗare. Mutsu-mutsun ƙwace jikinta ta fara ya saka hannayensa yay mata zobe. Duk yanda taso ta motsa kuwa sai ta kasa. Sake kumbura baki tayi da ƙyau, dan haka kawai ta tuno randa ya taɓa rungumeta a gidansu har Aunty Kubrah ta gansu. Kansa ya ɗora bisa kafaɗarta yana busa mata numfashinsa. Cikin magana raɗa-raɗa yace, Silly girl, K ba'a zama lafiya da ke sai kinja faɗa ko?”. Wani shegen mintsini ta bashi a cinya wanda ya sakashi sakinta babu shiri. Miƙewa tsaye tai daga jikinsa tana masa gwalo. Yanda ya ɓata fuska kamar zaiyi kuka ya sakata ƙyalƙyalewa da dariya tana nufa hanyar ƙofa. Yatsu biyu ta ɗaga masa, ɗayan hannunta riƙe da ƙugunta tace, “Wannan na yadda buk ne na maka. Saura na......” Ganin ya miƙe ya sata kwasa da gudu tai ciki batare data ƙarasa faɗaba. Baya ya rufa mata har cikin ɗakin. Nanfa suka shiga zagaye ɗakin. Duk yanda yaso kamata taƙi tsayawa, duk da dai da alama ya barta ne kawai. Ganin yanda yake hakki da nuna matuƙar gajiya ya saka taketa ƙyalƙyala masa dariya tana masa gwalo. Harda yin yanda yara keyi na tsokana. Tana saka yatsunta a kunne da jujjuyasu tana masa gwalo. Shiko ƙara narkewa yake irin shifa ya gaza kamata. daga ƙarshe ma ya faɗa saman gado yana hakki da faɗin, “Silly girl”. Zuwa tai har inda yake kwance ta shuri ƙafarsa zata gudu. Dama tarko ya mata. Yako harɗota da ƙafar sai gata a jijinsa. Da dai taga da gaske an kamatan saita fara kukan ƙarya tana kai masa ƙananun duka a ƙirji. Dariya ya farayi ya haɗa duka hannayen ya riƙe tare da juyata akan gadon ya koma kanta. “Wana kama to yanzun?”. Ya faɗa yana busa mata iskar bakinsa a kan idonta dake hawayen ƙarya. Baki ta sake kumburawa tana matso hawaye. “To bakai ka fara tsokanata ba. Ni dai dana fita ai banma kulaka ba amma ka takaleni”. Ƙanƙance idanunsa yay da ɗage gira sama. Yace, “Yarinyar nan kin iya sharri. A yaushe na tsokanekin?”. “Na rantse da ALLAH kai ne ka fara tsokanata, kuma bazan ƙyaleka ba sai na rama”. “Da gaske?”. Ya faɗa a hankali yana sake matsar da fuskarsa dab da tata har hancinsa na gogar nata. Cikin sarƙe idanunsa cikin nata ya sake faɗin, “Yaushe zaki daina rashin ji ne?”. Duk yanda taso bashi amsa ta kasa. Saboda goga mata lips ɗinsa da ya farayi akan nata. Tai ƙoƙarin kauda kanta gefe, yay saurin tarewa da nashi yana faɗin, “Uhmyim?. Faɗamin yaushe zaki san kin girma?”. Ba ƙaramin harbawa zuciyar Aymah tayiba saboda jin a yanda yay maganar, kafin tai wani yunƙuri ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Tabbas yau kam tamafi ranar shan chocolate, dan Yoohan ya tabbatarma Aymah a matuƙar zalame yake dason kasancewa da ita. Duk yanda yaso sassauta mata ya gagara, sai da ya ɗora mata sabon salon karatunsa mai wahalar haddacewa. Gaba ɗaya kukan da taso masama sai ta nemesa ta rasa, sai wani irin tsoro da matsananciyar kunyace da bata taɓa karo da itaba a rayuwarta ta lulluɓe ta. Tunda ta samu ya barta ta tura kanta cikin filos bata sake yarda sun haɗa idanu ba. Sun kwashe mintuna talatin a kwance kafin taji ya sake matsota. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba jin ya kwanto a bayanta. Amma sai ta daure tana ambaton sunan ALLAH. “Akwai matsala fa”. Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa a rigarta. Saurin riƙe masa hannu tayi ta zabura zata matsa yaƙi bata space. Dole ta haƙura sai daifa mutuniyar taku tsorone fal cikinta. “Kin jamin sai nayi wanka, kuma ni ban iya ba”. “Hu'um. wankan ne baka iyaba? Babu dai ƙyau manya na ƙarya”. Tai maganar da son jan jikinta. Saurin sake ruƙota yayi ya matse. A kunnen nata Yace, “Bafa normal wanka bane, Uncle ya sanarmin a addinin musilinci wanka ya kasu kashi da yawa. *_Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji. 2. Ɓoyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahiɗi ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda. 5. Jinin al’ada. 6. Jinin biki (wato jinin haihuwa). 7. Wankan jumu’ah. 8. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 9. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka, Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah). 10. Idan mutum ya farfado daga hauka ko farfadiya. 11. Wankan shiga Makkah. 12. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rokon ruwa. 13. Wanka na mai istiha a kowacce sallah. 14. Ga kowanne jima’i an so a yi wanka._* �kinga kenan yanzunma sai nayi fa tunda kin sakani na fitar da......” Wani irin wuntsilowa Aymah tayi ta dafe masa baki tana faɗin, “Na shiga uku ni Zainab, ni dai wlhy babu ruwana”. Ta fashe masa da kukan taɓara. Wani mugun dariya ne yaji yana taso masa. Amma sai ya danne da ƙyar dan karya ƙara tunzurata a samu matsala. Hannu yasa ya janye nata dake akan bakinsa. Fuskarta kuma har yanzu tana a ɓoye. “Okay yi haƙuri bake bace nine. Yanzu dai kisan yanda zakiyi dani lokacin salla yayi”. “To ni ya kakeso in maka?”. “Ki koyamin”. Tamkar zata fasa masa sabon kuka tace, “ALLAH ya sani nama fasa zaman hutawar ka maidani Nigeria kawai tunda na warke”. Shi dai dauriya yaketa yi dan kar yay dariya matsalar tafi haka. yace, “To naji, yanzu dai tashi muje ki koyamin yanda zanyi wankan”. “Ni dai babu inda zanje, idan kanaso na koya maka a haka kaje kayi abunka”. “A'a gaskiya, sai dai fa kiyimin practical zanfi fahimtarki. Haka ake malami yayta ragema ɗalibi mudun koyarwa”. Shiru tayi taƙi motsawa, taki kuma tanka masa. ya tashi zaune yana faɗin, “Okay shikenan, bara kawai na kira Uncle saina sanar masa abinda ya faru daga nan ya koyamin yanda zanyi wank.......”. Zaune ta tashi dingangan ta ɗare masa jiki da danne bakinsa da hannunta tana waro idanun dake cike da ƙwalla. “Yanzu dan baka da kunya sai ka kira Abbana ka sanar masa wannan abun?”. Hannunta ya ture yana marairaice fuska shima. “To yaya kikeso nayi ne Sweet girl? Kinga dai babu damar nayi salla babu wankan nan? Kema kanki nasan fa sai kinyi”. Ya kai ƙarshen zancensa da kashe mata ido ɗaya. Filo ta jawo ta maka masa a hannu sannan ta sauka masa a jiki tana ƙunƙuni. Duk yanda yaso danne dariyarsa ta gagara sai da yayi abinsa. Itako data sauka a gadon sai masifa takeyi a ranta tana sharar ƙwallan da babu tantama najin kunya ne. Shi dai Yoohan ganin ya samu yanda ya keso tasowa
Chapter 149 · 0% Book details